Da yammacin ranar Talata 25 ga watan Maris na shekarar 2025, Allah ya yi wa shahararren jarumi kuma dattijo a masana’antar fina-finan Hausa Abdullahi Shuaibu (Karkuzu) rasuwa, ya rasu bayan shafe tsawon lokaci ya na jinya a asibitin koyarwa ta Jami’ar Jos, Karkuzu ya rasu ya na da shekara 94 a duniya inda ya bar ‘ya’ya shida da mata daya.
An yi jana’izar sa da safiyar ranar Laraba 26 ga watan Maris na shekarar 2025 a gidansa da ke Haruna Hadeja Street, cikin garin Jos, Jihar Filato, ‘yan fim da dama sun yi alhinin rashin sa, sun kuma yi addu’ar Allah ya jikan sa, ya ba iyalin sa hakurin jure wannan babban rashin.
- Kasafin Kudi Na 2025: Kowanne ÆŠan Ƙasa ÆŠaya Zai Kashe Ƙasa Da $2.15 – Rahoto
- Me Ya Sa Fina-finai Masu dogon Zango A Masana’antar kannywood ke Zama Cin kwan Makauniya?
Karkuzu dai dan wasan kwaikwayo ne wanda ya yi tashe a wajen masu kallon wasan talabijin na ‘Karkuzu’ a shekarun 1980, a wasan yakan yi wa kan sa kirari da, “Ni ne Karkuzu, dan Kurmuzuzu, jikan Kuzu na Bodara, abar ni sai ta Allah ya yi”, dattijon kafin rasuwarsa ya shafe shekara 43 a masana’antar wasan kwaikwayo, kafin rashin lafiya ya sa ya daina.
A cikin watan Agustan shekarar 2023 ya bayyana a shafukan sada zumunta inda aka gan shi ya na neman taimako a wajen al’umma da abokan sana’arsu ta fim, saboda abin da ya kira kuncin rayuwa da yake ciki a wancan lokacin, saboda yanayin rayuwa inda har ya yi kira ga jama’a da su kai masa dauki.
A wancan lokacin Karkuzu ya samu matsalar gani inda har ta kai ga ya rasa idanunsa duka biyun, bugu da kari ya bayyana cewar bayan rashin abincin da zai ci ga kuma rashin muhallin zama saboda a wancan lokacin ya ce baya da gidan kanshi da zai zauna, Karkuzu ya yi bayanin ne a wata hira da yayi da TRT Hausa a shekarar 2023.
A yayin hirar Abdullahi Shuaibu ya ce “Ni dai suna na Abdullahi Shuaibu, amma al’uma na kirana da Karkuzu, ko kuma Abdullahi Kano, yanzu shekaru 43 kenan ina wannan harka ta fina finan Hausa, amma yanzu wasu lokutan sai in kwana ba ni da abin da za a ci a gida na, kuma wani abin tausayi, ni Karkuzu a yanzu zancen da na ke, wannan gida da nake ciki an sa shi a kasuwa, ba gida na ba ne, haya nake yi.
Ya ci gaba da cewa, yanzu a cikin wannan al’amari da na ke yi, in an ce na mallaki gida mai dimbin yawa, wadansu da za su ke kallo na sai su ce gaskiya ne, amma wallahi tallahi, daki daya bani da wani gida da za a kalla ace wannan mallakina ne, na rasa ido yanzu zancen da na ke mai kallo na ba na gani.
A kan batun ‘yan fim da za su iya taimaka masa, Karkuzu ya ce ba wai al’ummar Kano kawai ko al’ummar Jos, Kaduna ko na Legas ba, duk al’ummar duniyar nan ina bukatar a taimaka min, wannan gida yanzu da aka sa shi a kasuwa za a sayar, ba ni da kudi, bayan ba ni da kudi ba na gani, ba na zuwa ko’ina, ina da ‘ya’ya, maganar abinci kam ma babu, wannan shi ne zahirin gaskiya inji Karkuzu a hirar su da TRT Hausa na ranar 10 ga watan Agusta 2023.
A wancan lokacin sakamakon wannan neman taimako da ya yi, kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Nijeriya Ahmed Musa ya gwangwaje Karkuzu da kyautar makudan kudade har Naira 5,000,000, sannan kuma ya ba da umarnin a nemo gida ya saya masa, wanda bai wuce naira miliyan hudu zuwa biyar ba, kuma haka aka yi, domin kuwa Ahmed Musa ya saya masa gida na N5,500,000 kafin rasuwarsa.
Karkuzu ya yi manyan fina-finai madu dimbin yawa da tasiri a masana’antar Kannywood, daga cikinsu akwai Gida Da Waje, Ga Duhu Ga Haske wanda su ka shirya da Jaruma Zainab Muhammad (Indomie), a tsawon shekaru fiye da 40 da ya shafe a masana’antar Kannywood ya yiwa da dama a cikin jarumai hanyar samun daukaka a masana’antar.
Tasirin marigayi Abdullahi Shuaibu Karkuzu ba boyayye ba ne a jahar Kano, Arewacin Nijeriya da ma kasar bakidaya, wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na gwamnan jahar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar 28 ga watan Maris wadda LEADERSHIP Hausa ta fassara ya nuna yadda gwamnan jahar Abba Kabir Yusuf ya yi ta’aziyar mutuwar Abdullahi Shuaibu Karkuzu.
Sanarwar ta ce: “Gwamna Yusuf Ya Yi Ta’aziya Ga Masana’antar Kannywood Da Iyalan Shahararren Jarumin Kannywood Karkuzu Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi alhinin rasuwar shahararren jarumin Kannywood, Abdullahi Shuaibu wanda aka fi sani da Karkuzu wanda ya rasu a kwanakin baya bayan doguwar jinya, Karkuzu ya rasu ya na da shekaru 94 a duniya.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a Kano ranar Juma’a, Gwamnan ya ce mutuwar babban rashi ne ga masana’antar Kannywood na wani wanda ya kira kwararren jarumi mai fikira, da ya jajirce wajen yin sana’ar tare da taimako wajen tasowar yan wasa da dama a masana’antar.
Ya ci gaba da cewa marigayin ya bar wani gibi da zai yi wuyar cikewa cikin sauki, a shekarun da ya kwashe a masana’antar, ya nuna kwarewa iri-iri da kuma kokarin kawo sauyi ta hanyar nishadantarwa da kuma fadakarwa.
A madadin gwamnati da jama’ar Jihar Kano, gwamnan ya na mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin, ‘yan Kannywood da masana’antar fim.
Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya kyautata makwancinsa ya kuma baiwa ruhinsa dawwamammen aminci a cikin kabari, ya kuma roki Allah ya sa Aljanna Firdausi ce makomarshi.”
Wannan ya sa muka rubuta makalar “BA RABO DA GWANI BA” domin tunawa da wannan dattijo da ya shafe kusan rabin shekarun rayuwarshi domin ya nishadantar ya kuma fadakar da al’umma ta hanyar fina-finan Hausa, Karkuzu zai shafe tsawon lokaci ana tunawa da irin gudunmawar da bayar wajen kawo masana’antar Kannywood matsayin da ta ke a yanzu.
Hakazalika masu sha’awar kallon fina finan Hausa zasu dade su na kallon marigayin a matsayin wani mutum da ya nishadantar da kuruciyarsu ya kuma fadakar da tsufansu ta hanyar fina finanshi, sannan kuma matasa a masana’antar Kannywood za su tuna Karkuzu a matsayin wani jigo da su ka kwaikwayi ayyukanshi kuma sukayi amfanin da shawarwarinshi wajen samun daukaka a masana’antar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp