• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Tsoro Ne Yasa Muka Amince Da Sulhu Da Ƴan Bindiga Ba – Gwamnatin Sokoto

by Abubakar Sulaiman
4 months ago
Sokoto

Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayyana cewa matakin da ta ɗauka na tattaunawa da ƴan bindiga da suka yanke shawarar ajiye makamansu ba yana nufin rauni ba ne, sai dai wata hanya ta dindindin wajen kawo zaman lafiya a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan wani mai sharhi a kafafen sada zumunta, Basharu Altine Guyawa, ya soki matakin gwamnatin. Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan tsaro, Kanal Ahmed Usman (Rtd), ya fitar da sanarwa inda ya kare matakin gwamnatin.

  • Sojoji Sun Kashe Na Hannun Daman Bello Turji A Sokoto
  • Ya Kuɓuta A Hannun ‘Yan Bindiga Bayan Shafe Kwanaki 8 Yana Gudu A Dajin Sokoto Da Neja

Kanal Usman ya ce Guyawa a baya ya nuna shirin shiga tsakanin gwamnati da masu tada ƙayar baya, don haka ba daidai ba ne ya soki irin wannan yunƙurin. Ya ƙara da cewa gwamnatin Ahmed Aliyu ta rungumi tsari na “a bugu jaki a daki taiki” wato amfani da ƙarfi da kuma tattaunawa — bisa tsarin Soja na “kinetic da non-kinetic” — domin magance matsalar tsaro.

Gwamnati ta ce lardunan da abin ya shafa kamar Rabah, Goronyo, Isa da Sabon Birni na fuskantar mummunan tasiri, inda manoma suka bar gonaki, da kasuwanci ya tsaya, kuma mutane da dama na gudun hijira. Wannan yana jefa jihar cikin matsin tattalin arziƙi da barazanar rashin abinci.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnati na da niyyar dawo da zaman lafiya ta hanyar haɗa shiri na musamman domin karɓar masu tuba tare da tsauraran matakan kulawa da gyaran hali. Gwamnati ta ce hakan ba sassaucin hukunci bane, sai dai dabarar gina zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

A ƙarshe, gwamnatin ta bukaci masu sukar matakin da su yi hakan cikin hikima da niyyar gyara, tana mai cewa haɗin kai da fahimta ne kadai za su kai jihar Sokoto ga warware matsalolin tsaro da ta ke fuskanta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum
Manyan Labarai

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”
Labarai

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Next Post
An Kafa Fiye Da Kamfanonin Waje 24,000 A Sin Cikin Watanni 5 Na Farkon Bana

An Kafa Fiye Da Kamfanonin Waje 24,000 A Sin Cikin Watanni 5 Na Farkon Bana

LABARAI MASU NASABA

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

October 27, 2025
Sokoto

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.