Connect with us

RAHOTANNI

Babbar Sallah: Sayen Ragunan Layya Sai A Hankali – Danjuma Rabiu

Published

on

Shugaban kungiyar cigaban Arewa Kwaminiti na Jihar Legas, Alhaji Danjuma Rabiu Kurna ta cikin Birnin Kano, wanda ya ke zaune a unguwar Agbomalu ta karamar hukumar Apapa da ke cikin Birnin Ikko, ya bayyana cewar, a halin yanzu Babbar Sallar Idin Bana maganar sayen ragunan layya a wajen al’ummar Nijeriya sai a hankali a wajen sauke sunnar da Allah ubangiji ya dora mu su, idan a ka yi la’akari da irin matsalolin kudi da al’ummar kasar su ke ciki a halin yanzu.

Ya ce, ba karamin abu ba, idan a ka auna da irin wannan jarrabawa da Allah ya dora wa ’yan kasuwa da sauran al’ummar kasar na zaman gida, domin kaucewa daga kamuwa da cutar Korona. A cewarsa, al’amarin ya yi sanadiyar karyewar wadansu ’yan kasuwar kasar da na kasashen duniya a wajan kasuwancinsu na yau da kullum.
Ya cigaba da cewa, da yawan wadansu ma sai sun fita a kowacce rana sannan su ke samun abincinsu na ranar, bayan al’amuran da za su biyo baya irin rashin lafiya da sauran abubuwan da su ka shafi rayuwarsu da iyalansu bakidaya.
A kan haka ya ke isar da sakonsa na jeje ga ’yan kasuwa da sauran al’ummar kasar a game da wannan jarrabawa da Allah ya doro wa al’umma na wannan annoba ta cutar Korona, kuma a cewarsa, jama’a su dauki wannan al’amari kaddara ce kawai daga Allah kuma da fatan Allah ya kawar da ita a bisa doran kasa bakidaya.
Ya ce, a kan haka ya ke shawartar al’ummar kasar da su cigaba da gudanar da addu’o’i na musamman, domin samun gudunmawa a wajen ubangiji na kashe wannan cuta da sauran cututtuka bakidaya.
Advertisement

labarai