Connect with us

WASANNI

Babu Banbanci Tsakanin Salah Da Ronaldo Da Messi

Published

on

Mai koyar da tawagar ‘yan wasan kasar Masar Maguire ya bayyana cewa, kawo yanzu babu banbanci tsakanin dan wasan kasar, Muhammad Salah da Leonel Messi da kuma Cristiano Ronaldo idan ana maganar iya buga kwallo.

Muhammad Salah dai ya shiga cikin jerin ‘yan wasa uku da hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai ta fitar domin zama zakara a ‘yan wasan da suke buga kwallo a nahiyar sai dai daga baya dan wasa Luka Modric na Crotia ne ya lashe kyautar.

A halin yanzu ma Salah yana daya daga cikin ‘yan wasa uku da hukumar kwallon kafa ta duniya ta ware inda a cikinsu za ta zabi gwarzon dan kwallon duniya na wannan shekarar kuma Ronaldo da Modric da Salah din dai aka sake warewa.

Muhammad Salah dai ya yi kokari a kakar wasan data gabata a kungiyarsa ta Liberpool inda ya zura kwallaye 32 a gasar firimiya sanann kwallaye 43 ya zura a kakar wasan gaba daya hakan yasa ya zama gwarzon dan wasan gasar firimiya.

“Ina ganin a halin yanzu acikin Ronaldo da Messi da Salah babu wanda yafi wani a cikinsu duba da yadda ‘yan wasan suke buga wasa yadda ya kamata kuma suke zura kwallaye a raga a kowanne lokaci hakan yasa kungiyoyinsu suke kokari” in ji kociyan kasar ta Masar

A karshe ya ce, duk da cewa mutum daya ake son ya samu nasara a wajen lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya amma yana fatan Salah ya samu nasara saboda gogewarsa kuma hakan zai karawa kwallon kafa daraja a Afrika.

 
Advertisement

labarai