Jakadan Nijeriya a Kasar Turkiyya Ismail Yusuf, ya ce babu wani dan Nijeriya da girgizar kasar ta shafa.
Yusuf ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a ranar Talata.
- ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum Daya, Sun Sace 10 A Jihar Neja
- Mun Tara Wa Dan Takarar Gwamnanmu Miliyan 511 A Kano – NNPP
A cewarsa, ofishin Jakadancin yana cikin shirin ko ta kwana domin sanin halin da duk wani dan Nijeriya ke ciki a kasar.
NAN ta ruwaito cewa a safiyar ranar 6 ga watan Fabrairu, girgizar kasa mai karfin mita 7.8 ta afku a wasu garuruwa a Kudu Maso Gabashin kasar Turkiyya.
Shugaba Recep Erdogan, ya ce girgizar kasar ita ce Iftila’i mafi muni da kasar ta fuskanta cikin shekaru 84.
Yusuf, ya ce ana ci gaba da aikin ceto kuma babu wani rahoto da aka samu na asarar rayukan ‘yan Nijeriya da ke zaune a yankin da lamarin ya shafa har zuwa lokacin da yake zantawa da NAN.
“Da sanyin safiyar ranar Litinin da karfe 4:17 na safe agogon Turkiyya, girgizar kasa mai karfin mita 6.5 zuwa 7.8 ta afku a garuruwan Malatya, Sanliurfa, Osmaniye, Diyarbakir da Gaziantep.
“Ba mu da labarin kowane dan Nijeriya a cikin wadanda abin ya shafa ya zuwa yanzu.
“Wannan aiki ne da ke gudana. Muna yin iyakar abin da za mu iya. Muna kokarin shimfida aikin ceto da matakan kariya.”
Yusuf ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Kasar Turkiyya, inda ya yi alkawarin ‘yan bai wa Nijeriya goyon baya da hadin kai.
Ya zuwa yanzu dai sama da mutane 3,400 ne suka mutu a girgizar kasar a Turkiyya, inda dubbai suka jikkata, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Yayin da sama da mutane 2,000 kuma aka bayar da rahoton sun mutu a Siriya a sanadin girgizar kasar ta afku.