Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce babu wanda zai alakanta shi da satar dukiyar jama’a a lokacin da yake kan mulki.
Buhari ya nuna cewa bai tara wata dukiya a boye ba, “Ba ni da ko taku daya na fili a kasar waje.”
Da yake magana a Damaturu, a Jihar Yobe a wajen liyafar da aka shirya domin karrama shi a daren ranar Litinin kamar yadda kakakinsa, Femi Adesina, ya sanar cikin wata sanarwar da ya fitar, ya nanata rantsuwar da ya yi na cewa zai yi gaskiya har ranar da zai kammala wa’adinsa na mulki.
Ya shawarci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da kasancewa masu kishin kasa, “Sama da shekara 30 ina fada, ba mu da wata kasa da ta wuce mana Nijeriya, ya kamata mu tsaya mu hada karfi da karfe mu ceto ta.’’
Shugaban ya nuna farin cikinsa kan yadda lamura ke kara dawowa daidai a jihohin Arewa Maso Gabas da suka sha fama da matsalar tsaro.
Ya ayyana cewar ya cika alkawarin da ya yi a lokacin da ya karbi mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2015 kan yaki da ‘yan Boko Haram da daidaita lamura a kasar nan.
‘‘A Arewa Maso Gabas, Allah ya taimake mu mun kawar da Boko Haram, tattalin arziki ya farfado.
“Wasu mutane na tambaya ta kan nasarorin da na cimma a bangaren alkawarin da na yi kan yaki da cin hanci da rashawa.
‘‘To, a karkashin wannan tsarin yaki da rashawa da cin hanci ba karamin abu ba ne. A lokacin da nake soja, shugaba a zamanin soja, na kulle wasu mutane saboda kundin tsarin mulki ya ce dole ka ayyana kadarorinka, mutanen da ba su bayyana na kulle su.
“A karshe dai ni ma an kulle ni. Don haka, idan kana son ka hidimta wa kasar nan dole ka shirya wa shan wahala. Amma akwai abu guda da nake gode wa Allah a kai, babu wani mutum da zai iya bakanta ni. Ba ni da ko takudin fili a wajen Nijeriya kuma ina da niyyar zama a Nijeriya ko da na yi ritaya daga hidimta wa al’umma.”
Buhari ya yi godiya ga ‘yan Nijeriya da suka fahimce shi domin a cewarsa ya yi rantsuwa zai yi aiki tsakanin da Allah da kishin kasa.
Buhari ya gode wa gwamna Mai Mala Buni bisa kokarin da ya yi kan matsalar tsaro da daidaita zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar tare da shimfida ayyukan raya kasa.
Shi ma a jawabinsa, gwamna Buni, ya gode wa Buhari bisa kaddamar da ayyuka a jihar da suka kunshi Yobe katafaren sashen filin jirgin sama, babbar kasuwar zamani ta Damaturu, sashen kula da mata masu juna biyu da yara a Asibitin Koyarwa na Jihar Yobe, rukunin gidaje 2600 a Potiskum da kuma babbar makarantan Damaturu a Bra-Bra.