Bai Wa Ishak Hussaini Ragamar Elkanemi Warriours Ne Mafita

Matukar dai ana bukatar kungiyar kwallon kafa ta jihar Borno, wato Elkanemi warriors ta dawo sahun farko na kungiyoyin dake buga gasar cin kofin kwallon kafa ta Najeriya (Nigerian premier league), to sai an baiwa Ishak Hussaini ragamar horas da kungiyar.

Ishak Hussaini (coach) hazikin matashi ne dan asalin birnin Maiduguri wanda ya karanci ilimin horas da kungiyar kwallon kafa a Najeriya. A ‘yan cikin shekaru 5 zuwa 6 da ya yi a matsayin mai horas da kungiyar Aminu Babes, Ishak ya lashe manyan kofa-kofai sama da 14 a birnin Maiduguri. Abin da wani mai horas da wata kungiyar kwallon kafa a Najeriya bai taba yi ba ke nan, a lokacin yana matashi.

Koci Ishak Hussaini:

An kafa kungiyar kwallon kafa ta jihar Borno (Elkanemi warriours) a shekarar 1986. A shekarun 1991 da 2000 kungiyar tayi nasarar lashe gasar zango na biyu na cin kofin kwallo kafa na Najeriya, wato (National second dibision). Bayan haka, a shekarun 1991 da 1992 kungiyar ta lashe gasar FA na Najeriya (Nigeria FA cup). Sai kuma a shekarar 1991 kungiyar tayi kokarin zuwa zagayen farko na gasar cin kofin nahiyar Afirica (Confideration African Football). Sannan kuma shekarar 1993 ta sake zuwa wasan zangon kusa da karshe (semifinal) na gasar nahiyar Afirica. Tun daga nan kuma kungiyar bata sake yin wani abun azo a gani ba.

Matsalar hare-haren Boko Haram cikin shekarun 2015 zuwa 2016 yasa aka maida kungiyar busa wasaninta na gida a filin wasan Sani Abatcha dake birnin Kano da kuma filin wasan Mohammed Dikko dake jihar Katsina kafin kungiyar ta dawo birnin Maiduguri da ciga da buga wasaninta a shekarar 2017.

A ranar 17 ga watan Oktoban shekarar 2017 kungiyar ta gabatar da tsohon mai horas da kungiyar Ranger, wato Imama Amapakabo a matsayin sabon mai horas da kungiyar na tsawon shekara guda. Sannan a shekarar 2018 kungiyar ta sake gabatar da tsohon mai horas da kungiyar Kano Pillars, wato Baba Ganaru a matsayin sabon mai horas da kungiyar, wanda kuma a shekarar kungiyar ta fadi daga jerin kungiyoyin masu buga gasar farko na kofin Najeriya (Nigerian premier league).

Da wannan nake kiran ga gwamnatin jihar Borno, tun da dai wadanda ake ganin zasu iya horas da kungiyar sun kasa tabuka komai wanda har hakan takai ga baduwar kungiyar (Relegation) daga jerin kungiyoyin masu buga gasar farko na kofin Najeriya (Nigerian premier league), to a baiwan wannan jajirtaccen matashin (Ishak Hussaini) ragamar horas da kungiyar, domin a tabbatar da kwarewarsa da nasararsa.

Da fatan gwamnatin jihar Barno zata dube wannan shewarar namu tare da amfani dashi. Allah yasa mu dace, Amin.

Exit mobile version