Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar kokarin inganta ilimi da walwalar ‘yan Nijeriya na hana shi bacci.
Shugaban ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da ya yi wa ‘yan kasar a talabijin a daren ranar Litinin.
- Sojoji Sun Yi Luguden Wuta A Sansanonin ‘Yan Bindiga A Katsina Da ZamfaraÂ
- Da Dumi-dumi: Abdullahi Gwarzo Zai Maye Gurbin Ganduje A Matsayin Minista Daga Kano
“Kokarin inganta ilimi, lafiya da walwalar ‘yan Nijeriya ce ke hana ni barcin dare da rana.”
A cikin jawabin da shugaban ya yi a talabijin ya bayyana wasu shirye-shirye da zai yi don saukaka halin matsi da ‘yan Nijeriya ke ciki sakamakon cire tallafin man fetur.
Sai dai kungiyar kwadago ta kasa (NLC), ta shirya shiga yajin aiki a ranar Laraba don kin amincewa da cire tallafin man fetur.
Sai dai shugaba Tinubu ya roki kungiyar da ta ba shi lokaci don saita abubuwa tare da rage radadin cire tallafin man.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp