Mutane goma da suka shiga gasar hackathon da Bankin Zenith ke shiryawa a kan fasahar zamani ta karo na hudu, sun samu tallafin Naira miliyan 77.5, bayan sun zamo Zakaru a gasar.
Sun zamo zakarun ne, bikin baje koli na fasahar zamani mai taken ‘Samar Da Alkibla 4.0: hadadar kudi, yaki da kutse a na’urar zamani’.
- Nijeriya Na Buƙatar Naira Tiriliyan 1 Don Kawo Ƙarshen Cin Zarafin Mata –Bankin Duniya
- Karancin Takardar Kudi: Masu POS Da Bankuna Na Wasa Da Hankulan Jama’a
An rabarwa wadanda suka samu nasarar wannan adadin kudin ne, wadanda suka samu nasara a kan sauran wadanda suka gasar su sama da 1,700.
Kamfanin JumpnPass, ne ya zamo na daya inda ya samu kyautar Naira miliyan 25, tare da kuma koyar da shi da za a yi, na mako shida a kan shirin kera na’urar yin kyankyasa.
Za a gudanar da aikin ne dgaa watan Disambar 2024 zuwa watan Fabirairun 2025.
CreditChek, da ya zamu na biyu ya samu kyautar Naira miliyan 20, inda Salad Africa, ya samu kyautar Naira miliyan 15.
Sauran da suka samu kyautar su ne, Regdta, CashAfrica, Middleman, Messenger, Pocketfood, Famasi Africa da kuma Kitobu, inda kowannen su, ya samu kyautar Naira miliyan 2.5.
A jawabinta a wajen taron, babbar shugabar bankin na Zenith Bank Plc, Adaora Umeoji, ta bayyana jin dadinta ga Dakta Jim Obia wanda ya kirkiro da wannan gasar shekaru biyar da suka gabata.
Ta gode masa kan yin zurfin tunani ta ci gaba da wanzar da wannan fasahar ta zamani, musamman domin kara bunkasa fannin kasuwanci da ayyukan gudanar da banki.
A kan gasar ta Hackathon, ta ce, gasar ta shekara-shekara za ta kara karffawa matasan da ke a fannin fasaha guiwa.
Ta kuma, yi fatan samar da fitattun mutane a duniya, kamar su Bill Gates, Mark Zuckerberg, Stebe Jobs, da kuma Elon Musk a nan gaba ta hanyar gasar ta Hackathons ta bankin Zenith.
A sakonsa na fatan alheri a taron Gwamna jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bukaci da a rinka yin amfani da fasahar zamani, a fannin gudanar da kasuwanci.