Wani barawon mota mai karfin hali wanda ya sami yarinya a bayan kujerar motar da ya sata a garin Oregon, ya koma ya tsawata wa uwar game da barin yarinyar ba tare da kulawa ba.
A cewar ‘yan sanda na garin Oregon, lokacin da wanda ake zargin ya ga yarinyar sai ya koma wurin mahaifiyar ya tsawata ma ta ya kuma yi barazanar kiran ‘yan sanda a kanta, sannan ya ja motarta ya yi gaba.
A yayin da ya shiga cikin motar ne kafin ya tuka ya fahimci cewa akwai yarinya ‘yar shekaru 4 a ciki, sai ya koma ya umarce uwar ta da fitar da yarinyar daga motar, sannan ya sake tuka motar ya yi gaba, “jami’in mai magana da yawun ‘yan sanda na Beaberton, Matt Henderson ya shaida wa manema labarai.”
Lamarin ya faru ne a kasuwar nama da ke garin Beaberton, inda Crystal Leary ta bar injin motarta a kunne da kuma kokofi a bude ta shiga cikin kasuwa don siyan nama da galan din madara.
Wani ma’aikacin shagon ya fadawa hukumomi cewa, matar ta shiga shagon cikin ‘yan mintoci kadan wani mutumi ya zo ya tafi da motar ta.
Henderson ya ce, “barawon ya yi wa mahaifiyar lakca sosai saboda barin yarinyar a cikin motar, kuma ya yi barazanar kiran ‘yan sanda a kanta. Mun ma yi sa’a bai tafi da karamar yarinyar ba.”
‘Yan sanda sun ce, an dawo da karamar yarinyar ba tare da ko kwarzane ba.
Henderson ya ce, matar ba ta yi wani laifi ba kuma tana jin sautin yarinyar ta. Lamarin ya zama darasi akan iyaye da su rinka daukar ‘ya’yansu zuwa ko ina.
An gano motar mai kirar Honda Pilot da launin Silba ta shekarar 2013, ‘yan awanni kadan bayan faruwar lamarin a Portland, mai tazarar mil 8 daga garin Beaberton, amma ‘yan sanda na ci gaba da neman barawon, a cewar Henderson.