Abba Ibrahim Wada" />

Batun Tafiyar Messi PSG Na Sake Fitowa Fili

Messi PSG

Batun yiwuwar sauyin shekar kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Lionel Messi zuwa kungiyar Paris Saint German  na ci gaba da yin karfi a ‘yan makwannin nan, bayan da fitacciyar mujallar wasanni ta France Football ta wallafa kanun wani sharhi dake cewa ‘Wasikar kungiyar PSG ta sirri’ tare da wallafa hoton gwarzon dan wasan sanyen da rigar kungiyar ta Paris Saint Germain.

Sai dai za a iya cewa a nata bangaren PSG na yin taka tsantsan wajen fitowa fili kan aniyar kulla yarjejeniya da Messi, har sai koma ya tabbata saboda gargadin da kungiyar Barcelona tayi mata akan yawan maganar Messi da takeyi.

A watan Disambar bara tauraron PSG Neymar ya sha alwashin ya zama dole a wannan karon ya koma buga wasa tare da Messi, ya yin da a watan Janairu, daraktan wasannin PSG Leonardo ya ce kulla yarjejeniya da manyan ‘yan wasa irinsu Messi shi ne burinsu.

A dai watan na Janairu ne kuma, dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafar ta PSG, Leandro Paredes, dan kasar Argentina, ya ce tuni suka soma tuntubar kaftin din na Barcelona domin haka a yanzu wuka da nama na hannunsa.

A farkon wannan makon ne tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, John Laporta, ya bayyana cewa dan wasa kuma kaftin din kungiyar, Leonel Messi ya karbi tayin albashi daga wasu daga cikin kungiyoyin dake bibiyarsa.

A farkon wannan watan ne Laporta, wanda shi ne ake ganin zai lashe zaben, Joan Laporta,  ya zargi kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German da haddasawa kungiyar Barcelona rudani, sakamakon soma tuntubar kaftin dinsu Lionel Messi.

A watan daya gabata daraktan wasannin PSG, Leonardo ya ce kulla yarjejeniya da manyan ‘yan wasa irinsu Messi shi ne burinsu, yayin da shima dan wasan tsakiya na kungiyar ta PSG Leandro Paredes ya ce tuni suka soma tuntubar kaftin din na Barcelona don haka a yanzu wuka da nama na hannunsa.

A karshen kakar wasa ta bana yarjejeniyar Messi da Barcelona za ta kare, bayan kokarin katse ta da dan wasan yayi a shekarar bara, abinda ya janyo kai ruwa rana tsakaninsa da kungiyar wanda har yayi sanadiyar tafiya da kujerar shugaban kungiyar Jose Maria Bartemeu.

A wata hira da yayi da wani gidan Radio a kasar Sipaniya, Laporta ya tabbatar da cewa wasu kungiyoyi sunyiwa Messi tayin kudi mai yawa kuma tuni ya fara Magana dasu hakan yasa nake ganin abune mai wahala su iya rike shi

Tun a kakar wasa ta bara ne kuma ake alakanta Messi da komawa kungiyar PSG ko kuma Manchester City, kungiyar da a waccan lokacin har ta tattauna da maihafin tauraron na dan wasan.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta tattauna da mahaifin dan wasan wanda daga baya ya bayyana cewa dan nasa zai ci gaba da zaman kungiyar har zuwa karshen kakar wasa ta bana wadda zata kare a watan Mayun bana.

 

Exit mobile version