Connect with us

WASANNI

Bierra Ya Zama Sabon Kociyan Nice Ta Kasar Faransa

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Nice dake kasar Faransa ta dauki tsohon dan wasan Arsenal, Patrick Bierra a matsayin sabon mai koyar da kungiyar a kaka mai zuwa bayan sun kammala tattaunawa dashi.

Tsohon dan wasan wanda ya taba yin wasa a kungiyoyin Manchester City da Inter Milan da Jubentus yana cikin kakarsa ta uku ne a matsayin kocin kungiyar New York City a kasar Amurka, kafin samun wannan sabon mukamin.

Sai dai gabanin nadin nasa, wadansu suna ganin Bieira, mai shekara 41, yana daya daga cikin mutanen da za su iya maye gurbin Arsene Wenger a Arsenal kafin kungiyar ta bawa Unai Emery.

“Yanke shawarar barin kungiyar New York City abu ne mai matukar wahala gare ni da kuma iyalina,” in ji Bieira.

Kungiyar Nice ta kare kakar Gasar kasar Faransa a matsayi na takwas ne, wato maki daya tsakaninta da samun tikitin zuwa Gasar Europa.

Bieira zai maye gurbin kocin kungiyar Lucien Fabre wanda aka nada kocin Borussia Dortmund a watan Mayun daya gabata.

Tsohon dan wasan kasar Faransa, Bieira yana daya daga cikin ‘yan wasan kasar da suka lashe Kofin Duniya a shekarar 1998.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: