‘Yar takarar gwamna a Jihar Adamawa a jam’iyyar APC, Sanata Aisha Binani Dahiru, ta shigar da kara a kotun tarayya da ke Abuja, inda ta nemi kotun ta yi nazari kan ayyanata da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a matsayin wadda ta lashe zaben gwamna da aka karasa a ranar 16 ga watan Afirilu.
Binani ta kuma bukaci kotun da ta dakatar da INEC da wakilanta daga daukar mataki na gaba kan ayyana wanda ya lashe zaben, har sai kotun ta kammala yin nazari kan bukatar da ta shigar a gabanta.
- Gwamnan Filato Ya Bukaci Jami’an Tsaro Su Kamo Wadanda Suka Kai Hari Wasu Yankunan Jihar
- An Sace Ma’aurata Yayin Da Suke Dawowa Daga Coci A Osun
Binani ta ce hakan ya shafi doka ta 34 daya A da doka 31 a cikin baka da doka 3 2 a cikin baka a, b, c, da doka ta 6 ta babbar kotun tarayya ta shekarar 2019 da kuma ta sashe 251 1 a cikin baka q da kuma ta r kundin tsarin mulki na shekarar 1999 da ta sashe 149 da kuma ta sashe 152 ta dokar zabe ta shekarar 2022 da aka sabunta.
Hujjojin karar da Binani ta shigar a gaban kotun ta bayyana cewa, bayan INEC ta tattaro sakamakon zaben, inda ta shigar da karar INEC a matsayin wadda ta ke kara ta farko wadda kuma ta ayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaben, amma PDP da dan takarar ta gwamna Ahmadu Fintiri wanda ta shigar da kara a matsayin wanda ta ke kara na biyu da uku, sun fara tayar da rikici a jihar, inda hakan ya janyo dukan ma’aikatan INEC da cin zarafinsu.
A cewarta, tayar da rikicin ne ya janyo INEC ta soke ainahin sanar da sakamakon wadda alhali, ba ta karfin ikon yin hakan inda kotun sauraron karararkin zabe ce kawai keda wannan ikon.
Ta ce, soke ayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaben, hakan nuna cewa, INEC ta shiga cikin hurumin ikon kotun sauraron koke zabuka.
Ta gabatar da karar ce ta hanyar Lauyoyinta da babban lauya Hussaini Zakariyau ke jagoranta don kotun ta yi nazari kan ayyanata a matsayin wadda ta lashe zaben.
A cikin takardar bukatar ta Sanatan ta ce, kotu ce kadai keda hurumin daukar mataki kan jami’in INEC ba wai ita INEC din da kanta ba.