Cutar tarin fuka (TB), na daya daga cikin cututtuka mafi muni da kuma dadewa a duniya, wadda take ci gaba da lakume rayukan dubun nan ‘yan Nijeriya a kowace shekara, duk da cewa; ana iya yin rigakafi, ana kuma warkewa.
A shekarar 2023 kadai, Nijeriya ta samu mutuwar mutum 71,000, wadanda ke dauke da wannan cuta ta tarin fuka, inda ta zama ta daya a Afirka, kuma ta shida a duniya cikin kasashen da ke fama da ita.
- Tinubu Ya Umarci A Yi Bincike Kan Hatsarin Jirgin Kasa Daga Abuja Zuwa Kaduna
- Yadda Aka Gudanar Da Bikin Ranar Hausa Ta Duniya A Kano
An samu sabbin wadanda suka kamu da wannan cuta ta TB, su kimanin 499,000 a 2023, wadanda ke wakiltar kusan kashi 20 cikin 100 na masu dauke da cutar a Afirka, sannan kuma kashi 18 cikin 100 na wadanda cutar ta kashe a nahiyar. Duk kuwa da cewa, ana samun magunguna da gwaje-gwaje na cutar kyauta a dukkanin fadin kasar, sannan akwai dubbai wadanda ba a auna su ba da kuma wadanda suka fara shan magani a makare, wannan na taimakawa wajen ci gaba da yaduwar cutar a tsakanin al’umma.
Duk da yawan wadanda aka gano suna dauke da cutar, jami’an kiwon lafiya sun bayyana irin ci gaban da ake samu. Daraktan kula da lafiyar al’umma a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Dakta Godwin Ntadom, ya bayyana cewa; Nijeriya ta samu sanarwar bullar cutar tarin fuka mafi yawa a 2024, inda ta gano sama da mutum 400,000 da ke dauke da cutar, kwatankwacin kashi 79 cikin 100 na masu jinyar.
Haka nan, akwai yara da dama wadanda ke dauke da cutar ta TB, amma ba a gano ba. Kazalika, yaran da aka gano suna dauke da cutar, yawansu ya karu daga 8,293 a 2018 zuwa 43,000 a 2024, in ji shi.
Duk da haka, Ntadom ya bayyana cewa; tarin fuka wanda ba ya jin magani, shi ne wanda ya fi illa. “Adadin yawan masu dauke da cutar da ba a gano ba, su ne ke ci gaba da yada ta”, in ji shi.
Domin cike gibin da ake samu, gwamnatin tarayya a kwanan nan ta kaddamar da sauye-sauyen ayyukan fasaha. Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya sanar da tura na’urorin gwaji (D-ray) na wayar hannu guda 400 a fadin jihohin Nijeriya 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
“Wadannan rukunin, wadanda kwararru a bangaren ke sarrafa su, suna ba mu damar gano alamun cututtukan tarin fukar da ba a gano ba,” in ji Pate.
Gwamnati ta kuma damar yin gwajin kwayoyin cikin sauri. Tsakanin 2012 zuwa 2024, yawan kwararrun injinan gwaje-gwajen da aka samu sun karu daga 32 zuwa 513. Haka zalika, adadin cibiyoyin kula da tarin fuka ya kusan ninki biyu daga 12,606 a 2019, zuwa kusan 23,000 a 2024, wanda ya mamaye sama da rabin dukkanin cibiyoyin kiwon lafiya a fadin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp