Aikin Hajjin 2024, ya ajiye tarihin da ba za a manta da shi ba a tarihin aikin hajjin da Nijeriya ta halarta a kasar Saudiyya ta fuskoki da dama sakamakon tsare-tsaren da Hukumar jin dadin alhazai ta kasa, NAHCON ta aiwatar.
NAHCON, a karkashin jagorancin Malam Jalal Ahmad Arabi ta samu nasarori da yabo daga mahajjata da masu sanya ido a harkokin aikin hajji bisa aiwatar da tsare-tsaren kwarewa da hukumar ke da shi a tarihinta. Sai dai ana cewa, Ubangiji ne kadai ya cika 100 bisa 100.
- Sojoji Sun Lalata Matatun Mai 20 A Yankin Niger Delta
- Yadda Mai Haihuwar Fari Za Ta Kula Da Kanta (2)
Kwararren masanin aikin Hajji, Ustaz Abubakar Siddeq Muhammad, a cikin sharhinsa mai suna “Mal. Jalal Ahmad Arabi a aikin Hajjin 2024 (2)” wanda Kamfanin jaridar LEADERSHIP ya buga, ya yaba da tsare-tsaren shirye-shiryen Arafah da ba a taba yin irinsa ba inda ya ce. “A karon farko cikin fiye da shekaru 20, an shirya tantunan Nijeriya tsaf, an baje shimfidar kafet da na’urorin sanyi,” in ji shi.
Bugu da kari, wani masanin ayyukan aikin hajji, ya yi sharhi da tsokaci game da nasarorin da Arabi ya samu a lokacin jagorancinsa a matsayin shugaban hukumar NAHCON, kamar yadda aka buga a: “https://www.hajjnews.com.ng/2024/12/nahcon-in-2024-year-of-achievements-challenges-and-renewal.html”
Duk da cewa, rayuwa ba matabbata ba ce, haka ma, mulki ko jagoranci, suna da lokaci da iyaka. An yanke wa’adinsa jagorancinsa saboda wasu dalilai na siyasa da zarge-zarge amma shugabancin Jalal Arabi a matsayin Shugaban Hukumar NAHCON ya ba da sakamako wanda ya kawo sauyi, wanda a halin yanzu ke tabbace cikin cikakken bayanin rahoton Hukumar na 2024, mai taken “2024: Shekarar Nasarori, Kalubale, da Sabuntawa”.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ne ya amince da nadin Arabi a matsayin Shugaban Hukumar NAHCON a ranar 17 ga watan Oktoban 2023.
Daga cikin muhimman abubuwan da tarihi ba zai manta da ambaton sunan Arabi ba, sun haɗa da:
1. Samun Biza cikin sauki: Duk wani mahajjaci ya samu bizarsa ne kafin fara jigilar alhazai.
2. Ayyukan jigilar mahajjata zuwa Saudiyya: Sama da Alhazai 52,000 ne aka kwashe kafin ranar 9 ga watan Yunin 2024, kafin cikar wa’adin da Saudiyya ke bai wa kasashe na kammala jigilar alhazai. Kuma an kammala jigilar dawo da alhazai gida Nijeriya da kwanaki biyar saura.
3. Jin dadin Alhazai a Mina: An raba kayayyakin jin dadi kamar kayan zuwa bayan gida da karamar fankar hannu don maganin zafi.
4. Kula da kiwon Lafiya: An bayar da magunguna kyauta na cututtukan da ake saurin kamuwa kamar zazzabin cizon sauro da hawan jini, tare da tabbatar da kulawa da mahajjata cikin gaggawa akan lokaci.
Wadannan nasarori, da aka cimma duk da kalubalen tattalin arziki, sun nuna jajircewa da sadaukarwar NAHCON. Ƙoƙarin Jalal Arabi ya sami karɓuwa a duniya a lokacin da aka keɓe shi aka ba shi damar shiga wani ɓangare a Ka’aba mai tsarki wanda aka keɓe ga fitattun mutane a duniya.
A yayin da NAHCON ke ci gaba da samun nasarori, aikin Hajji na 2025 ya shirya tsaf don samun nasara tare da gudanar da aikin hajji cikin sauki ga mahajjatan Nijeriya. Irin wannan shine amfanin kafa tushe mai ƙarfi.