Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kashe kusan Naira biliyan 100 a shekarar 2025 wajen tabbatar da tsaro, lamarin da ya ce ya yi wa ci gaban jihar babban cikas. Ya bayyana haka ne yayin ziyarar sa ga Sarkin Uba, Ali Ibn Mamza, a garin Uba na ƙaramar hukumar Askira/Uba, domin duba halin tsaro a yankin. Gwamnan ya ce matsalolin tsaro sun hana gwamnati aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa, musamman gine-ginen hanyoyi da ake shirin ƙaddamarwa.
Zulum ya nuna damuwa kan yadda hare-hare ke sa ma’aikata da ƴan kwangiloli barin wuraren aiki, abin da ya daƙile manufofin cigaban jihar. Ya ce wannan ne ya sanya gwamnati ke kafa wurin hakar duwatsu a Gwoza tare da sayen manyan motocin aiki 100 domin hukumar gyaran hanyoyi ta iya bin diddigin shirye-shiryen samar da hanyoyi ba tare da dogaro ga kwangiloli na waje ba. Ya jaddada cewa idan an samu zaman lafiya, adadin kuɗin da ake kashewa kan tsaro za a mayar da su kan harkokin ilimi, da lafiya da sauran muhimman ayyuka.
- ISWAP Ta Kashe Jami’ai 8 A Wani Sabon Hari A Borno
- Ƴansanda Sun Fara Tabbatar Da Dokar Hana Zirga-zigar Babura A Kano
Duk da ƙalubalen tsaro, gwamnan ya tabbatar wa jama’ar yankin cewa nan ba da jimawa ba za a fara gudanar da sabbin aiyuka, ciki har da gina hanyoyi, da kafa cibiyoyin kimiyya da kwamfuta da kuma wasu muhimman makarantu a yankin. Ya ce gwamnatin jihar na da shirin tabbatar da cewa al’ummar Borno ba za su rasa sauyin da suke muradi ba duk da matsalolin da ake fuskanta. Ya ƙara da cewa gwamnati tana fito da tsare-tsare na dogon lokaci domin tabbatar da ɗorewar cigaba bayan samun kwanciyar hankali.
A nasa ɓangaren, Sarkin Uba, Ali Ibn Mamza, ya yaba wa gwamna Zulum bisa jajircewarsa wajen gudanar da aiyukan raya ƙasa duk da matsalolin tsaro da jihar ke fama da su. Ya ce abubuwan da gwamnati ta yi suna nan a bayyane, yana mai gode wa gwamnan kan kulawa da tallafin da ake bai wa al’ummar Uba. Sarkin ya tabbatar da cewa za su ci gaba da yin addu’o’i domin samun zaman lafiya mai ɗorewa a Borno da ƙasa baki ɗaya.














