Buhari Da Obasanjo: Darussa Daga Haduwar Habasha

Sulaiman Bala Idris  07036666850

Ya ishi mai hankali yayi tunani dangane da abubuwan dake faruwa a kasarmu ta Nijeriya. ya ishe mun yin nazari da yi wa kawunanmu fada a daidai wannan bigiren, tun kafin bakin alkalami ya bushe.

Sau da yawa, da zaran wani lamari ya faru a tarayyar Nijeriya, sai ka tarad da jama’a sun dau bangare, kowa na kokarin sai an fahimce shi, ko an bi ra’ayinsa da na bangaren da yake kare wa. Daga irin wannan sabanin ne ake samun rikici, ake samun rashin jituwa.

Irin wannan sabanin na ra’ayin siyasa, kan haifar da kashe-kashe a wasu yanayin, ya kan haifar da rikici, a zub da jinni. ya kan haifar da yanayin sabawa a tsakanin aminai wadanda suka dau lokaci mai tsawo suna kiwon abotarsu.

Ita siyasa, a wurin dan Nijeriya ya dauke a matsayin wani lamari na a mutu ko a yi rai. bakin rai bakin fama. a daidai lokacin da talaka ke irin wannan makauniyar siyasa, ko ma in ce bahaguwar siyasa, su kuma ‘yan siyasan da ake yi domin su, suna fatan Allah ya ara musu lokaci, su yi tozali da abokin hamayyarsu domin su cashe, su rungumi juna.

Wasikar da Obasanjo ya aike a makon da ya gabata, ta tayar da kura, ta yamutsa hazo. An samu mabambantan ra’ayoyi dangane da wasikar, da yawa wasu sun daina yi wa juna magana. Wasu kuma a kafafen sadarwa musamman ma na ‘FACEBOOK’ sun dode juna (Blocking), wasu kuma sun koma yiwa juna habaice-habaice da kallon hadarin kaji.

Lamarin, kai ka ce dama ana zaman jiran juna ne. Domin yadda yanayi ya dumama, lamurra suka yi zafi, sai ka dauka dama ana zaman jiran kiris ne.

Obasanjo ya yi wasikarsa, washegari gwamnatin tarayya ta hannun Ministan Yada Labarai da Al’adu, Mista Lai Mohammed ta fid da sanarwar cewa, wannan wasika ta Obasanjo za su amshe ta da kyakkyawan niyya. Wannan zance daga bangaren gwamnatin tarayya kawai ya ishi mai hankali ya fahimci cewa ba lamari bane na tashin hankali. Amma fa duk da haka, wasu daga cikinmu basu mayar da wukar kube ba. Haka nan aka ci gaba da musayar zafafan kalamai, wadanda ka iya sa a dibi makamai a yi kan juna.

Kwatsam! a jiya, sai ga hotuna sun fara cika kafafen sadarwa, inda aka dauko hoton Buhari da Obasanjo a Birnin Habasha, suna raha, cike da annashuwa da farin ciki. Kana ganin hotunan, suna kumshe ne da wani sako, wanda a cikinsa tamkar ana cewa; “Kun kari hayaniyarku, aboki ya ga abokinsa’.

Su manya da shugabannin Nijeriya sun tabbatar da cewa sabanin tsakaninsu ba lamari bane na daina mu’amala da juna, ko lamari ne da idan aka kai ga haduwa za a fille takubba a fara zubar da jini ba. lamari ne adawa da hamayar siyasa, irin haka kuma babu wani wuri a duniya, inda ake mulkin Dimokradiyya da babu makamancin wannan.

Yana da muhimmanci mu koyi kai hankali nesa dangane da lamarin siyasa. Domin kuwa, idan ba mu sa hankali ba, a haka za mu yi ta yakar juna, mu yi ta kashe juna, mu yi ta musgunawa juna, mu yi ta kawo karshen abota da zumunci. Su kuwa wadanda mu ke yi dominsu, ko a jikinsu, domin su da iyalansu za su hade a Habasha, ko Ingila da Iyalan abokin hamayyarsu su sha madara, su ci nama tare. Har ma idan dama ta samu su yi hotuna da bidiyo domin tarihi. Kai fa? ka zagi Mudi, ka bata da Samuel. Ka dode Musa a Facebook, ka sari Tanko da barandami. Kuma fa duk a banza, babu lada balle la’ada.

Mu dau darasi daga haduwar Habasha!

Exit mobile version