A daidai lokacin da ‘yan Nijeriya suke tunanin ba za su sake gani ko jin labarin wani jami’in dansanda ya kashe mai mukamin (ASP) mai suna Drambi Bandi, wanda yake aiki a ofishinsu na yankin Ajah a Jihar Legas ya dirka wa wata matar aure kuma Lauya wanda kuma aka tabbatar tana dauke da cikin ‘yan biyu, mai suna Misis. Bolanle Raheem bindiga, inda ta nan take ta ce ga garinku nan a ranar Kirsitimeti.
Wannan kisan ya jefa iyalai, ‘yanuwa da al’ummar Nijeriya gaba daya cikin alhini da tausayi.
- Tabarbarewar Aikin Gwamnati A Matakin Jihohi
- Kuskuren Shugabannin Baya Ne Ya Jefa Nijeriya Cikin Tsaka Mai Wuya – Kwankwaso
Binciken da na yi ya nuna cewa, Marigayyar ta fito daga wani gidan sayar da abinci ne tare da iyalanta don shakatawar ranar Kirsimeti, a lokacin da take kokarin bi ta karkashin gadar Ajah sai kawai dansandan ya dankara wa motarta harsashi.
Bayani ya nuna cewa, nan take aka garzaya da ita asibiti amma koda aka isa asbitin Likitocin sun tabbatar da cewa, ta riga mu gidan gaskiya. Misis Bolanle ’yar shekara 41 a duniya, ta rasu ta bar yara hudu tana kuma dauke da ciki wata 7 na ‘yan biyu.
Jami’in watsa labarai na rundunar ‘yansanda Jihar Legas, (SP) Benjamin Hundeyin, ya tabatar da aukuwar kisan ya kuma sanar da kama dukkan ayarin ‘yansandan da ke aiki a wurin da abin ya faru don gudanar da cikakken bincike a kan yadda lamarin ya faru tare da daukar matakin hukunci a kan su, tuni kuma Shugaban Rundunar ‘Yansandan Nijeriya IG Usman Baba ya bayar da umarnin dakatar da wanda ake zargin don a samu cikakkaken yanayin gudanar da bincike.
Haka kuma kamar yadda ake samu in irin haka ya faru, manyan kasa da manyan, siyasa kan kai sa baki tare da kira da ayi adalci ga wanda aka kashe, haka ma a wannan lokacin, Gwaman Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi tir da kisan ya kuma bayar da tabbacin bayar da goyon bayan ganin an gudanar da bincike yadda yakamata don a gaggauta tabbatar da adalci ga wadda aka kashe. Haka kuma kungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) reshen Jihar Legas ta shigar da kara inda take neman diyyar naira Biliyan 10 a kan kisan.
Ba nufi na in ba baku labarin abubuwan da suka biyo bayan kisan, amma babbar tambayar da ya kamata a na nemi amsa a nan shi ne wai shin har zuwa yaushe ne ‘yansandan da aka dorawa alhakin kare rayuwar al’umma za kuma su zama sanadiyyar kisansu? a farkon watan jiya ne wani dan shekara 31 a duniya mai suna Gafaru Buraimoh ya gamu da ajalinsa yayin da wani jami’in ‘yansanda da ke aiki a ofishin rundunar da ke Ajah a Jihar Legas ya dankara masa bindiga sakamakon wata takaddama wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Rahoton da Cibiyar Bunkasa Harkar Dimokradiyya (CDD) ta bayar ya nuna cewa, a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2021, jaim’an tsaron Nijeriya sun yi sanadiyyar mutuwar ‘yan Nijeriya fiye da 13,000, wannan na daga cikin wadanda aka iya samun rahotonsu ke nan, don bincike ya nuna cewa, akwai ire-iren kisan da ‘yansanda ke yi da ba a iya samun rahotonsu, saboda wasu dalilai.
Idan za a iya tunawa a watan Oktoba na shekarar 2020, matasa a sassan Nijeriya suka gudanar da wani gaggarumin zanga-zanga don yin Allah wadai da cin zarafi da kisan da ‘yansanda ke yi wa ‘yan Nijertiya a sassan kasa, zanga-zangar da aka yi wa lakabi da Endsars wadda daga baya ta brikide ta zama tarzoma, babban burinta shi ne yekuwar neman a kawo karshen kisan da shi a bisa ka’ida da jamji’an ‘yansanda na rundunar da aka yi wa lakabi ba SARS suka tafka a kan ‘yan Nijeriya. Duk kuwa da an rusa rundunar amma daga dukkan alamu al’amurra bas u canza ba daga bangarern rundunar ‘yansandan.
Irin wannan kisan da ‘yansanda ke yi wani abu ne da bashi a bisa ka’ida wanda babu wata al’umma da za ta amince da shi kuma dole a kawo karshensa, take hakkin dan adam ne kuma babban abin kunya ce ga duk kasar da ta bari irin wannan abin ya cigaba da aukuwa.
Amma abin takaicin shi ne, kisan da ‘yansandan ke yi wa al’umma ya zama ruwan dare a Nijeriya, inda zaka samu ‘yansanda na amfani da mukamin su suna kisan mutane ba tare da wani ka’ida na shari’a ba, kuma ba tare da an hukunta su ba.
Dole gwamnatin tarayya ta dauki kwakkwarar mataki na kawo karshen wannan babban lamarin da ke gudana. Dole ta tabbatar da gudanar da cikakken bincike tare da hukunta dukkan jami’in da aka samu da laifin kashe wani dan Nijeriya ba tare da ka’idar doka ba, a kuma tabbatar da bayar da tallafi da biyan diyya ga iyalan wadanda aka kashe.
Haka mkuma dole a rungumi tsarin sake fasalin ayyukan ‘yansanda a cikin gaggawa kuma dauki hanyar zamanantar da aikin don ya yi daidai da yadda al’amarin yake a sassan duniya. Sake fasalin kuma ya hada da cikakken horaswa ga jami’an don su yi daidai da yadda sauran jami’an ‘yansanda ke tafiyar da harkokinsu a tsakaninsu da al’umma a sassan duniya, a kuma karfafa bukatar mutunta hakkin al’umma a dukkan harkokin aikinsu.
Haka kuma ina mai ra’ayin cewa, yakamata a sa ido a kan yadda ake daukar jami’an ‘yansanda, dole a samar da hanyar da za ta tabbatar da hana ‘ya daba da ‘yan ta’adda tare da mastafa shiga aikin, don a lokutta da dama irinsu ne ke aikata irin wannan ta’asasar na kisan jama’a.
A bayyana yake cewa, hakar daukan jami’an ‘yan sanda ya zama wani fage na cinhanci, kabilanci da son kai wanda hakan yana haifar da rashin samun isasun horo ga ‘yansanda, irin haka kuma yake haifar da rashin aminci a tsakanin al’umma da ‘yansandan, har ma a halin yanzu maganar nan na cewa, ‘yansanda abokin kowa ne ya zama abin dariya, in ba haka ba ta yaya aboki na zai zama kuma mai kashe ni?.
Babbar mastsalar rundunar ‘yansanda na tattare ne da yadda ake gudanar da shirin daukar matasa aikin, dole lamarin ya zama babu sanya hannun ‘yan siyasa, ya zama wadanda suka cancantan ne kawai ake dauka ba tare da lura da daga inda suka fito ba. Ta haka za a tabbatar da samar da ‘yansanda masu kishin kasa da al’umma, wadanda za su sadaukar da rayuwarsu don kare kasa da al’ummarta.
Ta hanyar yin maganin wanna matsalolin, gwamnatin Nijeriya ta hau hanyar samar da rundunar ‘yansndan da za su yi aiki tukuru wadanda za su tsayu wajen kare rayuwa da dukiyar al’umma wanda hakan kuma zai kai ga karfafa kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Al’ummar Nijeriya sun cancanci zama a kasar da ake kare rayuwa da dukiyar su, yayin da kuma wani tsaustayi ya auku suna da tabbacin za a dauki matakin hukunci a kan dukkan wanda ya saba wa doka, akwai kuma bukatar gagguta kawo karshe tare da taka wa kisan da ‘yansanda ke yi wa ‘yan Nijeriya BIRKI.