ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Guje Wa Siyasantar Da Matsalar Tsaro

by Leadership Hausa
4 weeks ago
Tsaro

Barkewar cacar bakin da ta kaure a kafar yada labarai wato sukar da babban ministan tsaro Christopher Musa mai murabus ya yi kan tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ta sake haifar tarnaki, ga lamarin rashin kasar a cikin bangaren siyasa. 

Christopher, a wata hira da aka yi da shi, a kafar talabijin, ya yi kakkausar suka ga El-Rufai, musamman kan yadda a lokacin da ya mulki jihar Kaduna, gwamnatinsa, ta kirkiro da tsauraran matakai, wanda hakan, ya haifarwa da lamarin tsaron Kaduna, cikas, musamman biyo bayan samun aukwar hare-haren, da suka yi sanadiyyar daukar rayukan wasu da ke a yankin kudancin Kaduna. 

Sai dai, El-rufai a martanin gaggawa da ya yi kan wannan sukar ta ministan ta hanyar lauyoyinsa, ya bai wa ministan wa’adin kwanuka bakwai da ya janye kalamansa, kan wannan sukar, tare da kuma neman yafiya, daga gun El-rufai. 

ADVERTISEMENT

Kazalika, El-rufai ya kuma barazanar daukar matakin Shari’a tare da neman a biya shi diyyar Naira biliyan 10, kan bata masa suna da ministan ya yi, kan wannan sukar. 

Wannan batun, ya sanya masu yin rubuce-rubuce a kafafen yada labarai, yin amfani da wannan damar ta tataburzar a tsakanin jiga-jigan kasar biyu, inda hakan ke nuna cewa, wata sabuwar jan daga ce, a tsakainsu, musamman a bangaren siyasar kasar. 

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Nijeriya Sun Gaji Da Uzurin Gwamnati Na Ƙarin Farashin Mai A Ƙasa

Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki

A namu ra’ayin, wannan fafatarwa ta fatar baki kan batun, a kafar yada labara, sabawa ka’idar bangaren shari’a ne da kuma haifar da wawagegen gibi, kan kokarin da ake yi, na samar da bayanan sirri, kan lamarin kalubalen rashin tsaron kasar, da yaki ci ya kuma ki cinyewa. 

Idan aka baje kan wannan batun a Faifai, musamman domin a fahimci yadda lamarin yake dole ne, a yi waiwaye kan tarihin tafiyar da bangaren tsaro na Kaduna, musammana daga 2015 zuwa 2023. 

A lokacin tsohuwar gwamnatin El-Rufai, yankunan da ke a Kudancin Kaduna, musamman Kasuwan Magani, Kajuru, Zangon Kataf da kuma Kauru, an fuskanci yawan samun aukuwar daukar rayukan wasu mazauna wadanan yankunan, musammman, ta hanyar hare-haren ‘yan bindiga tare da kuma tarwatsa rayukan wasu da wa’kir, ta rutsa da su. 

Ga duk wanda ya ke a Kaduna a lokacin tsohuwar gwamnatin ta El-rufai, an ruwaito ya furta kalaman da ke kara haddasa kiyayaya da gaba, a tsakanin ‘yan jihar, musamman cika har da ikirarinsa na cewa, tsowar gwamnatinsa, ta bakado ana daukar nauyin Fulami Makiyaya na ketare, domin kisan daukar fansa, a jihar. 

Bugu da kari, an samu korafe-korafen yin watsi da wasu yankunan jihar, kawai domin sun soki gwamnatinsa, kan nuna rashin tausayi tare da kuma kakaba masu dokar hada fita da kuma gazawar gwamnatinsa, na cafko maharani da ke hallaka alumma a wasu yankunan na kudancin jihar. 

Haka zalika, an soki gwamnatinsa, kan kakabawa wasu shugabannin alumma, sarakunan gargajiya da ke a yankin, laifiin da ba su ji, ba su kuma gani ba, wanda hakan ya sanya, aka kama wasunsu tare da kuma garkame su, inda su kuma maharani, suka ci gaba da cin Karensu, babu babbaka. 

Tarin irin wannan, ta’asar ta tsohuwar gwamnatin Malam, ta shiga tarihi, wanda idan har an tabbatar da hakan, akwai bukatar abi wa alummar wadannan yankunan adalaci. 

A nan, sai dai, ba mu ji dadin yadda ministan ya soki El-rufai, a kafar gidan talabijin ba, domin duba da cewa, shi ne, babban ministan tsaron kasar, yafi dacewa, a hukuamce, ya umarci hukumomin tsaron kasar, su gudanar da cikakken bincike, maimakon yin sukar, a kafar yada labarai. 

Yin wannan sukar a kafar ta talabijin, ta haifar da tambayar da ke da sarkakiyar, amsawa, domin idan har gwamnatin tarayya, na da cikakkun hujojin da ke alakanta cewa, El-rufai da su, shin, me ya sa gwamnatin ba za ta bi matakan shari’a ba ko kuma ta gudanar da bincike? 

Duba da cewa, wannan sukar ta ministan kan El-rafi, na zuwa ne, daidai lokacin da kasar ke fuskantar zaben 2027, musamman ganin cewa, ya kasance daga bangaren adawa, sukar ta ministan, na iya haifarwa da fannin tsaron kasar matsala. 

Bugu da kari, sukar ta ministan na iya shafar kimar da ta yi saura ta hukumomin tsaron kasar, musamman duba da yadda darajar hukomomin tsaron kasar, ke ci gaba da zubewa a fuskar ‘yan kasar. 

Ra’ayin wannan Jaridar shi ne, idan har gwamnatin tarayya na da cikakkun hujoji kan zargin da take yiwa tsowar gwamnatin ta El-rufai, ba wai yin amfani da kafar yada labarai domin yanke masa hukunci ne, ya dace ba. 

Abinda ya yafi dacewa gwamnatin ta yi shi ne, bin matakin shari’a, idan har tana son ta hukunta El-rufai, kan wadanna zargin da take yiwa tsowar gwamnatinsa, da aikatawa. 

Ba girama da kimar ministan ba ne, ya siyasantar da fannin tsaron kasar ba, domin ya zamar masa wajibi, ya banbance batun siyasa da kuma lamarin da ya shafi fannin tsaro. 

Alummar kudancin Kaduna da kuma sauran wadanda kalubalen rashin tsaro ta yi silar rasa rayukansu da kuma tarwatsa rayuwarsu, musamman a Arewacin Nijeriya, sun cancanci, a abi matakan shari’a. domin abi masu hakkinsu, amma bai wai, a rinka siyasantar da halin da suka tsinci kansu a ciki ba. 

Abinda ya wajaba a yi la’akari akai shi ne, ba ta hanyar yin suka a kafar yada labarai ne, za a iya samar da tsaro mai dorewa ga kasar ba. 

Kazalika, duk wani zargin da ake yi akai, zuwa gaban kuliya domin gano ba’asi, shi ne kawai mafita, amma ba wai yin suka, ba gara, ba sabat ba. 

Bukatar Guje Wa Siyasantar Da Matsalar Tsarobarkewar cacar bakin da ta kaure a kafar yada labarai wato sukar da babban ministan tsaro Christopher Musa mai murabus ya yi kan tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ta sake haifar tarnaki, ga lamarin rashin kasar a cikin bangaren siyasa.Christopher, a wata hira da aka yi da shi, a kafar talabijin, ya yi kakkausar suka ga El-Rufai, musamman kan yadda a lokacin da ya mulki jihar Kaduna, gwamnatinsa, ta kirkiro da tsauraran matakai, wanda hakan, ya haifarwa da lamarin tsaron Kaduna, cikas, musamman biyo bayan samun aukwar hare-haren, da suka yi sanadiyyar daukar rayukan wasu da ke a yankin kudancin Kaduna.Sai dai, El-rufai a martanin gaggawa da ya yi kan wannan sukar ta ministan ta hanyar lauyoyinsa, ya bai wa ministan wa’adin kwanuka bakwai da ya janye kalamansa, kan wannan sukar, tare da kuma neman yafiya, daga gun El-rufai.Kazalika, El-rufai ya kuma barazanar daukar matakin Shari’a tare da neman a biya shi diyyar Naira biliyan 10, kan bata masa suna da ministan ya yi, kan wannan sukar.Wannan batun, ya sanya masu yin rubuce-rubuce a kafafen yada labarai, yin amfani da wannan damar ta tataburzar a tsakanin jiga-jigan kasar biyu, inda hakan ke nuna cewa, wata sabuwar jan daga ce, a tsakainsu, musamman a bangaren siyasar kasar.A namu ra’ayin, wannan fafatarwa ta fatar baki kan batun, a kafar yada labara, sabawa ka’idar bangaren shari’a ne da kuma haifar da wawagegen gibi, kan kokarin da ake yi, na samar da bayanan sirri, kan lamarin kalubalen rashin tsaron kasar, da yaki ci ya kuma ki cinyewa.Idan aka baje kan wannan batun a Faifai, musamman domin a fahimci yadda lamarin yake dole ne, a yi waiwaye kan tarihin tafiyar da bangaren tsaro na Kaduna, musammana daga 2015 zuwa 2023.A lokacin tsohuwar gwamnatin El-Rufai, yankunan da ke a Kudancin Kaduna, musamman Kasuwan Magani, Kajuru, Zangon Kataf da kuma Kauru, an fuskanci yawan samun aukuwar daukar rayukan wasu mazauna wadanan yankunan, musammman, ta hanyar hare-haren ‘yan bindiga tare da kuma tarwatsa rayukan wasu da wa’kir, ta rutsa da su.Ga duk wanda ya ke a Kaduna a lokacin tsohuwar gwamnatin ta El-rufai, an ruwaito ya furta kalaman da ke kara haddasa kiyayaya da gaba, a tsakanin ‘yan jihar, musamman cika har da ikirarinsa na cewa, tsowar gwamnatinsa, ta bakado ana daukar nauyin Fulami Makiyaya na ketare, domin kisan daukar fansa, a jihar.Bugu da kari, an samu korafe-korafen yin watsi da wasu yankunan jihar, kawai domin sun soki gwamnatinsa, kan nuna rashin tausayi tare da kuma kakaba masu dokar hada fita da kuma gazawar gwamnatinsa, na cafko maharani da ke hallaka alumma a wasu yankunan na kudancin jihar.Haka zalika, an soki gwamnatinsa, kan kakabawa wasu shugabannin alumma, sarakunan gargajiya da ke a yankin, laifiin da ba su ji, ba su kuma gani ba, wanda hakan ya sanya, aka kama wasunsu tare da kuma garkame su, inda su kuma maharani, suka ci gaba da cin Karensu, babu babbaka.Tarin irin wannan, ta’asar ta tsohuwar gwamnatin Malam, ta shiga tarihi, wanda idan har an tabbatar da hakan, akwai bukatar abi wa alummar wadannan yankunan adalaci.A nan, sai dai, ba mu ji dadin yadda ministan ya soki El-rufai, a kafar gidan talabijin ba, domin duba da cewa, shi ne, babban ministan tsaron kasar, yafi dacewa, a hukuamce, ya umarci hukumomin tsaron kasar, su gudanar da cikakken bincike, maimakon yin sukar, a kafar yada labarai.Yin wannan sukar a kafar ta talabijin, ta haifar da tambayar da ke da sarkakiyar, amsawa, domin idan har gwamnatin tarayya, na da cikakkun hujojin da ke alakanta cewa, El-rufai da su, shin, me ya sa gwamnatin ba za ta bi matakan shari’a ba ko kuma ta gudanar da bincike?Duba da cewa, wannan sukar ta ministan kan El-rafi, na zuwa ne, daidai lokacin da kasar ke fuskantar zaben 2027, musamman ganin cewa, ya kasance daga bangaren adawa, sukar ta ministan, na iya haifarwa da fannin tsaron kasar matsala.Bugu da kari, sukar ta ministan na iya shafar kimar da ta yi saura ta hukumomin tsaron kasar, musamman duba da yadda darajar hukomomin tsaron kasar, ke ci gaba da zubewa a fuskar ‘yan kasar.Ra’ayin wannan Jaridar shi ne, idan har gwamnatin tarayya na da cikakkun hujoji kan zargin da take yiwa tsowar gwamnatin ta El-rufai, ba wai yin amfani da kafar yada labarai domin yanke masa hukunci ne, ya dace ba.Abinda ya yafi dacewa gwamnatin ta yi shi ne, bin matakin shari’a, idan har tana son ta hukunta El-rufai, kan wadanna zargin da take yiwa tsowar gwamnatinsa, da aikatawa.Ba girama da kimar ministan ba ne, ya siyasantar da fannin tsaron kasar ba, domin ya zamar masa wajibi, ya banbance batun siyasa da kuma lamarin da ya shafi fannin tsaro.Alummar kudancin Kaduna da kuma sauran wadanda kalubalen rashin tsaro ta yi silar rasa rayukansu da kuma tarwatsa rayuwarsu, musamman a Arewacin Nijeriya, sun cancanci, a abi matakan shari’a. domin abi masu hakkinsu, amma bai wai, a rinka siyasantar da halin da suka tsinci kansu a ciki ba.Abinda ya wajaba a yi la’akari akai shi ne, ba ta hanyar yin suka a kafar yada labarai ne, za a iya samar da tsaro mai dorewa ga kasar ba.Kazalika, duk wani zargin da ake yi akai, zuwa gaban kuliya domin gano ba’asi, shi ne kawai mafita, amma ba wai yin suka, ba gara, ba sabat ba.

Tsaro
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    PalmPay Na Ƙara Wayar Da Kan Jama’a Game Da Hanyoyin Tuntuɓar Tallafi Na Hukuma Yayin Da Haɗarin Zamba Ke Ƙaruwa
  • Leadership Hausa
    ‘Yan Nijeriya Sun Gaji Da Uzurin Gwamnati Na Ƙarin Farashin Mai A Ƙasa
  • Leadership Hausa
    Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar
  • Leadership Hausa
    Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

MASU ALAKA

NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN
Ra'ayinmu

‘Yan Nijeriya Sun Gaji Da Uzurin Gwamnati Na Ƙarin Farashin Mai A Ƙasa

October 11, 2026
Tsaro
Ra'ayinmu

Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki

August 14, 2026
Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG
Ra'ayinmu

Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG

July 31, 2026
Next Post
Tawagar Super Eagles Ta Shilla Zuwa Guinea-Bissau

Tawagar Super Eagles Ta Shilla Zuwa Guinea-Bissau

LABARAI MASU NASABA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.