Ana gudanar da makon shayar da Jarirai Nonon uwa ne, a duk shekara, inda a makon na satin zagayowar ranar, ya jaddda mahimancin ƙara ci gaba da ɗorewa da kuma kula da lafiyar Jarirai.
Taken taron na wannan shekarar shi ne,“ Cigaba da Shayar da Jarirai Nonon uwa na ƙara masu yin doguwar rayuwa a cikin lafiya,”.A duk lokacin zagayowar makon, hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya wato WHO da kuma Asusun tallawa ƙananan yara wato UNICEFm su kan gabatar da yin kirakirayen ci gaba da kula da lafiyar Jarirai da kuma bayar da goyon baya, ga shayar da Jarirai Nonon uwa, musamma domin a ɗora Jariran kan rayuwa mai ɗorewa.
Akasari dai, ƙungiyar haɗakar ƙasashe ta WABA tare da haɗaka da UNICEF da WHO, suka faro bikin makon ne a 1992. Inda a duk ranar 1 zuwa ranar 7, na kowanne watan Agustan shekara, ake gudanar da bikin makon.An kuma jaddda matuƙar buƙatar, ,atakan gwamnati uku da guraren yin aiki na su samar da kyakyawan yanayi ga iyaye masu shayarwa, domin su zamu zarafin shayar da Jariransu, Nono.
A ɗaukacin faɗin duniya, an yi ittifaƙin cewa, shayar da Jarirai Nonon uwa, na rage yawan samun mutuwarsu da kuma ƙara inganta kiwon lafiyarsu.Bugu da ƙari, baya ga shayarwar, hakan na ƙara bunƙasa shaƙuwa a tsakanin uwa da Jaririnta.
Haka zalika, bincike ya nuna cewa, shayar da Jarirai Nonon uwa na kare uwar daga hatsarin kamuwa da cutar Siga ta mataki biyu, tare da kuma ƙarawa uwa lafiya.Ga Nijeriya, za a iya cewa, wannan saƙon bai zo akan lokaci ba, amma dai, ƙasar sannu a hankali, na ci gaba da samun raguwar mutuwar mata masu juna biyu da kuma Jariransu.
A gafe ɗaya kuma, wasu yaran ƙasar, musamman masu shekaru ƙasa da biyar, na ci gaba da fuskantar barazanar ƙarancin abinci mai gina masu jiki.Hatta ma’aikatar kula da kiwon lafiyar ƴan ƙasar ta tarayya, ta sha yin gargaɗi kan ƙalubalen da ake da shi a ƙasar, na ƙarancin abinci mai jiki, a tsakanin yara masu shekaru ƙasa da biyar.
Wannan matsalar, na ci gaba da shafar rayuwar sama da gidajen miliyon talakawa ƙasar, wanda hakan kuma ke ci gaba haifar da koma baya, ga ƙoƙarin da ake yi, a matakin ƙasa, na ƙara haɓaka ƙasar.A ɗaukacin faɗin ƙasar, an ƙiyasata cewa, ya zuwa yanzu, aƙalla yara miliyan biyu, na ci gaba da fuskantar matuƙar barazanar ƙarancin abinci mai gina jiki.
A gafe ɗaya kuma sama da ƴan Nijeriya miliyan 36 a ɗaukacin faɗin ƙasar, ke ci gaba da fuskantar ƙarancin abinci.Misali, wannan ƙalubalen, ya fi yin ƙamari a jihohin da ke Arewacin Nijeriya, musamman inda ake ci gaba da fusknatar rikice-rikice, inda a ƙalla mutane miliyan 17, ke ci gaba da zama a cikin matsalar yunwa.
Kazalika, hatta mata masu juna biyu da kuma mata masu shayarwa, da ke a cikin irin wannan jihohin, na ci gaba da kai gwauro da mari, domin neman abinda da za su kai a bakin salati, ballantana wata maganar samun abinci mai gina jiki.Rashin samar da abinci mai gina jiki, na shafar lafiyar uwa da Jaririnta, musamman duba da cewa, ana buƙatar, uwa ta shayar da Jaririnta Nono uwa zalla har zuwa tsawon shekaru biyu, wanda shayarwa, na kare Jariran daga kamuwa da cutuka, kamar irin su, gudawa, ko kuma mutuwarsu.
Duk da irin gangamin wayar da kan da ake yi a Nijeriya kan mahimmancin shayar da Jarirai nonon uwa, amma hakan na ci gaba da raguwa.A cewar UNICEF, kaso ɗaya a cikin uku na Jarirai a ƙasar ake syara da su Nonon uwa, bayan an haife su, inda kuma kaso uku kacal su ake shayar da Jiriransu Nono har zuwa wata shida, na haihuwarsu, wanda hakan ke nuna cewa, shayarwa, ta yi ƙasa da yadda ake buƙata.
A saboda yin dubi da mahimmancin shayar da Jarirai Nono uwa ne, ya sanya gwamnatin ƙasar, a ranar zagoyawar ranar, ta ƙaddamar da shirin sauya tuanin kan shayar da Jarirai Nonon uwa, musaman har zuwa tsawon wata shida.A saboda haka, akwai buƙatar a samar da kyakywan yanayi a guraren yin aiki, na masu zaman kansu da kuma na gwamnati, da zai bai wa masu shayawa, damar shayar da Jariransu.
Kazalika, ya kamata gurane yin aiki masu zaman kansu, su rinƙa bayar da hutu ga iyaye mata masu shayarwa.Suma masu faɗa aji a cikin alumomi, sarakunan gargajiya da malaman addinai, na da gudunmwar da za su bayar, ta faɗakarwa da wayar da kai, kan mahimmancin shayar da Jarirai Nonon uwa.
Kowanne yaro a ƙasa, ana buƙatar fara rayuwarsa, a matakin ƙoashin lafiya, inda ta hanyar shayara da Jarirai Nonon uwa ne, kawai, za su iya samun hakan.Nijeriya dai, na ci gaba da fuskantar ƙalubalen ƙarancin abinci mai gina jiki, inda kuma a gafe ɗaya, ƙasar ke ci gaba da fuskantar barazanar ƙaranncin abinci.
Ƙara ƙarfafa goyon bayan shayar da Jarirai Nonon uwa, abu ne, da ya zama wajbi, ba wai batu kawai, na samar da ɗauki, ga fannin kula da kiwon lafiya ba.Daga yau ne, ya kamata a ƙara sanya ƙaimi, a fannin zuba jari a ɓangaren shayar da Jarirai Nonon uwa, domin a gobe, a samar da yara masu ingantacciyar lafiya.














