• English
  • Business News
Friday, May 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Kafa Dokar-ta-baci Kan Yaduwar Jabun Magunguna

by Leadership Hausa
2 months ago
in Manyan Labarai
0
Bukatar Kafa Dokar-ta-baci Kan Yaduwar Jabun Magunguna
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A kwanan baya ne Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, ta rinka kai samame ba kakkautawa, a manyan kasuwannin da ke a daukacin fadin kasar nan, wanda hakan a zahirance, ya tona asirin irin hatsarin da Nijeriya ke ciki na masu hada-hadar jabun magunguna.

Hukumar a yayin samamen nata, ta bankado yadda ake hada-hadar sayar da jabun magunguna wadanda kuma suka lalace a kasuwar Aba a Onitsha da kuma ta Idumota da ke a jihar Legas, wadanda kudinsu ya kai na biliyoyin Naira.

  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 92, Sun Kubutar Da Mutane 75 A Cikin Mako Guda – DHQ
  • Yadda Fadada Bude Kofar Kasar Sin Ke Haifar Da Damammaki Ga Duniya

Baya ga irin wannan bakar hada-hadar ta jabun magungunan = da irin wadannan mugayen mutanen keyi a wadannan kasuwannin, bankado wadannan gurbatattun magungunan na bliyoyin Naira a wadannan kasuwannin ya nuna karara yadda tsarin kiwon lafiyar na kasar nan yake tafiya a kan tarkon mutuwa.

A nan ya zama wajbi, mu jinjinawa kokarin na Hukumar NAFDAC ke yi, na jajircewar bankado wadannan kasuwanin, amma duk da haka za a iya cewa, Hukumar ta dan gaza duba da cewa, tana gudanar da irin wannan samamen ne, kawai daga wani lokaci zuwa wani lokaci.

A ra’ayin wannan jaridar, wannan binciken na Hukumar a kasuwannin ba komai bane, tamkar na tayar da hankalin ‘yan Nijeriya, duba da irin tulin jabun magungunan da hukumar ta bakado a kasuwannin.

Labarai Masu Nasaba

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

A kasuwar Ariaria da ke Aba, NAFDAC, sun gano jabun magunguna da kudinsu ya kai na miliyoyin Naira.

Bugu da kari, a kasuwar Idumota da ke a jihar Legas, NAFDAC sun garkame Shanguna sama da 3,000 bayan sun gano Shagunan shake da jabun magunguna.

A kasuwar kan Gadar Onitsha, nan ma Hukumar ta sun kama manyan motoci goma shake da jabun magungana, inda a bayan kamen dilolin magungunan suka yi yunkurin bai wa jami’an na NAFDAC cin hancin Naira miliyan 135.

Har ila yau, a kasurgumar kasuwar Cemetery da ke Aba, nan ma NAFDAC ta kama tare da kwace jabun magunguna da kudinsu ya kai na sama da Naira miliyan biyar.

Bisa batun gaskiya, irin wannan bakar hada-hadar jabun magunguna, ya wuce maganar alkaluma, domin kuwa, abinda yafi dacewa, shi ne, yankewa irin masu wannan bakar harkalar hukuncin ta hanyar rataye su, duba da yaddda suka kara jefa rayuwar marasa lafiya a cikin wata ukuba ta hanyar sayar da jabun magunguna.

Abinda ya kara jefa fargaba a zukakan jama’a ne, shi ne, kan irin hanyoyin da irin wadannan bata garin ke bi wajen sarrafa jabun magungunan, musamman ganin yadda suke da kayan aikin da suke sake sarrafa magungunan da suka riga suka lalace.

Kazalika, a wani gwaji da NAFDAC kan mangunan yara, da wadannan bata garin ke sarrafawa suke kuma sayar da shi, kan farashi mai sauki, NAFDAC bata iya gano wani abu da ba daidai ba.

Wannan rashin iya ganowar na NAFDAC ya nuna yadda sarrafa magungunan na jabu, sun jima suna yin sanadiyar mutuwar yara, ba tare da yin amfani da bakin Bindiga ba.

Wannan matsalar dai, ba wai kawai ta tsaya kan daidaikun ‘yan kasuwa masu sarrafa jabun magungunan bane, domin abu ne, da ya karade daukacin miyagun masana’tun da ke da ke sarrafa jabun, inda suka fakewa a matsayin Shaguna suna cikin Karensu babu babbaka ciki har da sarrafa jabun magunguna na yakar cuta mai karya garkuwar jiki.

A yayin samamane na NAFDAC, sama da haramtattun masana’antu 240 da ake sarrafa jabun magunguna aka bankado a kasuwar Cemetery.

A ra’ayin mu wadannan matakan da aka dauka na kai samame a kasuwannin bai isa ba, duba da cewa, hukuncin shigo da kwayar maganin Tramadol zuwa cikin kasar nan ta haramtacciyar hanya, shi ne, kodai yin shekaru biyar a gidan gyran hali ko kuma biyan tararar Naira 250,000, domin kuwa dole mu mayar da hankali wajen kare kiwon lafiyar yan kasar nan.

Mojisola Adeyeye, Darakta Janar ta kasa ta Hukumar NAFDAC, ta bukaci da a rinka yanke hukuncin kisa ga masu sarrafa jabun magunguna, duba da yadda suke jefa rayuwar alumma a cikin matsala da kuma jefa tsarin kiwon lafiya a cikin barazana.

Yawan samun irin wadannan kasuwannin na sarrafa jabun magungunnan duk da kokarin da NAFDAC ke kan yin a rage sarrafa jabun magungunan akalla zuwa kaso biyar a cikin dari a 2025, hakan na ci gaba da zama wani babban kalubale ga hukumar, musamman duba da yadda ake ci gaba da samun karuwar a kasar.

Wani abin bakin ciki shi ne, yadda halastatun kungiyoyin dilolin sarrafa magunguna kamar irin su, EKUMI Plaza Patent Medicine, suma suka bi sahu wajen shiga kazamar hanyar ta hada-hadar kasuwancin jabun magunguna da suka kai na Naira miliyan 50.

Karafafa yakar wannan lamarin bai wadatar ba, domin kuwa kamata ya yi a yiwa fannin rabar da magunna na kasar nan garanbawul baki daya.

Ci gaba da samun wanzuwar irin wadannan kasuwannin na sayar da jabun magunguna na kara haifar da gibi a bangaren tsarin kiwon lafiyar kasar.

Ya zama wajbi Gwamnatin Tarayya ta sake yin nazari kan bayar da takardun fito na shigo da magunguna cikin kasar, musamman domin a tallafawa halastattun masana’atun cikin gida da ke sarrafa magungunan.

Ya kuma kamata a kara karfafa shirin Inshorar kiwon lafiya na kasa NHIS, wanda hakan zai taimaka a rinka samar da ingantatun magunguna kuma a cikin farashi mai sauki, wanda hakan kuma zai sanya, durkushewar bakar kasuwar ta sayar da jabun magunnan a kasar.

Kazalika, akwai bukatar a rinka ilimantar da alummar gari kan illar irin wadannan jabun magungunan.

Bai kamata bangaren Shari’a ya rinka yin hukunci mai sauki ga masu wannan dabi’ar ba, musamman duba da yadda kawai irin masu wannan dabi’ar da suka shiga hannun hukuma ake cin su tara ‘yar kadan.

Dole kutuna sun tilatsa tsauraran hukunci, ciki har da yanke hukunci zaman gidan Yari da kuma yanke hukuncin haramtawa wadanda aka kama suna sarrafa jabun magunguna kara yin duk wata sana’a da ta shafi sarrafa magunguna.

Yawon da irin wadannna jabun magungunan a cikin alumma, tamkar yankewa iyalai hukuncin kisa ne.

Bugu da kari, ya zama wajbi daukacin ‘yan Nijeriya su tashi tsaye mu yi aiki tukuro domin kawo karshen wannan bakar dabi’ar, mu kuma jajirce har sai mun ga an a sayar da ingantatun magunguna a kasar.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: DokaJabun MagungunaNAFDAC
ShareTweetSendShare
Previous Post

Nijeriya Za Ta Fara Aiwatar Da Yarjejeniyoyin Haɗin Gwiwa Da Kafofin Watsa Labarai Na Sin – Ministan Yaɗa Labarai

Next Post

Karin Kudin Lantarki Da Na Kira: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shirya Zanga-zanga A Fadin Nijeriya

Related

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje
Manyan Labarai

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

7 hours ago
Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai
Manyan Labarai

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

8 hours ago
Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa
Manyan Labarai

Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

16 hours ago
Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma
Da ɗumi-ɗuminsa

Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma

21 hours ago
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

21 hours ago
Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron Sauyin Yanayi A Dubai
Manyan Labarai

Tinubu Ya Kai Ziyarar Aiki Jihar Anambra

24 hours ago
Next Post
Karin Kudin Lantarki Da Na Kira: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shirya Zanga-zanga A Fadin Nijeriya

Karin Kudin Lantarki Da Na Kira: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shirya Zanga-zanga A Fadin Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

May 9, 2025
Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

May 9, 2025
Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

May 9, 2025
Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

May 9, 2025
GORON JUMA’A 09/05/2025

GORON JUMA’A 09/05/2025

May 9, 2025
Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

May 9, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

May 9, 2025
AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 

AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 

May 9, 2025
Rabe-Raben Aikin Hajji Da Abubuwan Da Aka Halasta Ga Mahajjaci

Rabe-Raben Aikin Hajji Da Abubuwan Da Aka Halasta Ga Mahajjaci

May 9, 2025
Matatar Mai: Har Yanzu ‘Kabal’ A Ɓangaren Mai Na Yaƙar Nasararmu – Dangote

Matatar Mai: Har Yanzu ‘Kabal’ A Ɓangaren Mai Na Yaƙar Nasararmu – Dangote

May 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.