Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban, wadanda suka shafi al’umma. Ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da korafe-korafen da wasu mutanen ke yi dangane da warin jiki, wanda dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu;
“Akwai mutanen da idan suka shiga cikin jama’a kamar ta bangaren; abun hawa, wajen zaman majalisa, shiga kasuwa ko wajen aiki, da dai sauransu. Za a ji suna bugawa (Warin rana na tashi) sosai da zarar sun isa wajen, har ya zama sun takurawa na kusa da su, ba za a daina ji ba har sai idan sun bar wajen. Kuma hakan yana faruwa daga kowane bangare tsakanin mata da maza.
- Ana Fatan Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
- A Karo Na Hudu ’Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Sun Yi Nasarar Kammala Ayyukansu A Wajen Kumbon
Shin me yake haifar da hakan?, Ta wacce hanya za a bi domin magance irin wannan matsalar, Wacce shawara ya kamata a bawa sauran al’umma bakidaya game da wannan batu?.
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta, Ƙaura-Namoda Jihar Zamfara:
Sau da yawa wasu mutane suna raina wanka da gyara jikinsu, Inda suka fi gane wanke jiki ko rashin amfani da turare, bayan kuma tsafta tana daga cikin imani. Abubuwan da ke kawo wari mai tashi ya addabi wadanda ke kusa; sun hada da rashin wanke jiki da lungu da sako a yayin wanka. Sannan rashin saka turare a jiki yana haifar da wari ko da ana wanka. Bugu da kari wasu suna yin kwana hudu, biyar, har zuwa sati daya ba tare da sun yi wanka ba. Kayan jiki ma wasu suna maimaita saka su fiye da sau biyu ko uku a cikin sati daya. Hanyoyin da za a bi domin magance matsalar wari mai tashi su ne; yawan yin wanka ko da sau biyu a rana, kada a maimaita kaya sau ba adadi ba tare da an wanke ba. A dinga amfani da turare ko na awo ne a murza wa jiki da tufafi kafin a fita. Shawarata a nan ita ce, duk wanda ya san yana cudanya da jama’a, ya yi kokarin gyara kansa da jikinsa saboda gudun a dinga kyamar sa idan ya shiga mutane. Sannan a yawaita wanke baki saboda shi ma yana haddasa gagarumin wari mai tashi a cikin al’umma.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya wannan matsala tana faruwa a kowane bangaren, kuma wasu suna samun wannan matsala ne daga Allah wasu kuma dabi’a ce ta kazanta. To, da farko dai idan daga Allah ne sai dai mutum ya dage da addu’a Allah ya raba su da shi. Wadanda kuma kazanta ce ta jawo suke yi kamata yayi su yi kokari suna zaftacce jikin su domin kaucewa cutar da mutane. To, shawara anan ita ce, ya kamata mutane suna tsaftacce jikin su domin kaucewa cutar da mutane abokan zaman su domin hakan zai taimaka wajen a samu zaman lafiya.Su kuma wadanda Allah ne ya jarabce su da wannan matsala sai su dage da addu’a Allah ya raba su da ita.
Sunana Khadija Auwal Koki, A Jihar Kano:
Gaskiya rashin tsaftacce jiki ne yake kawo haka, kuma yana da kyau ace ana tsaftacce jiki domin kuwa ita tsafta ma cikon addini ce. Ta hanyar gyara jiki da kuma tsaftacce shi akai-akai, sannan kuma ayi amfani da kayan gyara domin a kasance a tsaftacce. Ya kamata mu kasance masu tsaftacce jikin mu a kodayaushe, ka da mu kasance masu zama da dauda a jikinmu ko kazanta.
Sunana Abba Abubakar Yakubu daga Jos, a Jihar Filato:
Abin da zan ce game da wannan muhawara shi ne, akwai rashin tsafta, akwai kuma halitta. Na farko dai akwai wasu mutane da wanka yake zama musu matsala, kuma ba su damu da tsaftace jikinsu ba. Ko dai a dalilin kazanta ko wani ra’ayi na ganin dama, kamar wasu da ke ganin yawan wanka yana daga cikin son duniya da rashin tuna lahira. A wajen su yawan wanka ba abu ne mai kyau da mumini zai rika yi ba a kodayaushe, wannan ra’ayin su ne. Amma kuma akwai wadanda halinsu ne ba sa son zuba ruwa a jikinsu, saboda ba su dauki hakan kazanta ba, sai lokacin da suka yi ra’ayi. Akwai kuma masu tsafi ko wani asiri da za a hana su sa ruwa a jikinsu tsawon wani lokaci, saboda kada asirin ya karye. Ga wadanda a baya na ce halitta ce, su kuma akasari ana haihuwar su ne da lalurar warin kashi ko warin baki, inda duk turaren da suka sa ko tsaftar da suka yi, sai ka ji hamamin jikin su na tashi. Ana kuma samun wasu da ke fama da wata lalura ta rashin lafiya, wanda ke fitar da diwa ko wani wari, saboda gyambon da ke jikinsu, ko wani abu makamancin haka.
Sunana Princess Fatimah Mazadu, Jihar Gomben Nijeriya:
Wasu gaskiya rashin wanka ne, wasu kuma warin kashi da daudar jiki. Yawan wanka da amfani da kamshi ko ka tsaftace gabobin jiki sosai, kula da sutura da tsaftarsu, sannan sanya wankakakkun suturu. Shawarar kam ai kawai ana rage dauda, saboda zubar mutunci da kima. Dan tsabta ma karin daraja ce a idon al’umma, sannan “Annazafatu minal imaan” cewar, Manzon Allah SAW. Ko baka saka turare b,a ka tsaftatace kayanka da jikinka ya wadatar. Mata ana amfani da ‘body spray’ ko turare dai mara karfi sosai, dan wallahi yadda a mazan ake da masu wari haka a matan ma. Wallahi in ka zauna kusa da wani ko wata, sai ka amayar da hanjinka. Allah ya tsaremu da masu cutar da mutane, sannan da cutar da kahunansu, saboda kai kanka in ka ji kamshi ko ka je wuri mai kamshi hanci kake budewa kai ta muzurai. Amma naka jikin kamar masai ko kwata tsabar wari, akwai cutarwa sosai a kula.
Sunana Abubakar Usman, Malam Madori A Jihar Jigawa:
Sau tari za ka ga mutane sun fito daga gida ko mota, yayin da ake rana sun hada zufa, jikin su ya na tashi, wanda hakan ya na takurawa mutane sosai, usamman idan suka shiga cikin jama’a. Hakan yakan sa mutane su ji rashin dadi yayin da suke tare da su har sai sun bar wajen. Warin jiki ko warin rana yana faruwa ne sakamakon abubuwa kamar haka; Rashin tsafta (rashin wanka akai-akai), yawan zufa da rashin amfani da turare, amfani da kaya marasa tsabta, cin abinci mai kamshi mai tsanani kamar albasa, tafarnuwa, da sauransu. Abubuwan da ya kamata a yi; Wanke jiki kullum, musamman idan za a fita ko bayan an yi gumi, Amfani da sabulun da ya ke kamshi, Sanya kaya masu tsabta, a wanke su da kyau, a shanya su, Yin amfani da turare na jiki, Cin abinci mai tsafta da guje wa mai haifar da warin jiki. A rika kula da tsaftar jiki da kaya,
Sunana Hassana Yahaya Iyayi, daga Kano:
Sosai yana faruwa ba ga mazan ba, ba ga matan ba. Wasu halittar su ce haka ciwo ne, wasu kuma kazanta ce da rashin sanin yadda za a gyara wajen dake fitar da wari wasu har da karni ma za ki ji, ko ba shi- ba shi duk suke yi. Wasu gaskiya yadda nace miki ciwo ne inji iyayenmu, tun daga wankan jariri ne ba a fitar masa da daudar haihuwa ba da yake yaro warin kashi ya kama shi. wasu kuma an ce zafi ne dasu a jikinsu shi ya sa, wasu kuma kazanta ce da barin gashin hammata babu gyara shi ke jawo wa. Shi dai na warin kashi sun ce; durasar gero da sabulun salo da madarar turare ake hadawa ko hadda kanwa ne na manta ake hada wa ana wanka da shi. Masu wari hammatan nan kuma dan Allah in babu kudin siyan ‘roll on’ akwai Allumin shi kadai ya isa in ki/kana fitowa daga wanka ki/ka goga a hammata sai a dan shafa turare a jiki, za a ji tsaf. A kiyaye dai tsafta cikon addini ce, ba za ka so kana dosowa ana gudu ba, Allah ya kyauta.
Sunana Ibrahim Garba Bizi, Damaturu Jihar Yobe:
Rashin tsafta na jiki, musamman rashin wanka da canza kaya akai-akai. Ciwon fata ko rashin lafiya da ke haddasa wari. Yin wanka kullum, amfani da sabulu da turare masu kyau. Neman shawarar likita idan wari ya wuce kima. A rika kula da tsafta ta jiki da tufafi, Kada a raina tsafta saboda kowa na iya cutuwa da wari, A fadakar da juna cikin ladabi da tausayi ba da cin mutunci ba.
Sunana Hafsat Sa’eed Jihar Neja:
Ni dai ina ganin abin da yake haifar da hakan ba komai bane kazanta ne, hanyar da ya kamata abi domin magance irin wannan matsala shi ne tsafta. Mutum ya kasance me tsafta duk da dai akwai wadanda za a ga jininsu ne haka, amma a rika kulawa wajen fesa turaruka, ba zai yu ace ka yi irin wannan warin Magancewarsa shi ne ka kasance me tsafta ko da yausje kana cikin tsafta, ko ranayadake ka muddin za ka yi wanka kafeshewa jikinka turare ba yadda za a yi wannan warin ya shiga jikinka. Shawara ta a wurin al’umma bakidaya shi ne mutum ya kasance me tsafta, jiki ba a yi masa tsafta ba ta ya za a yi ba za a ji irin wannan warin ba, so yana da kyau mutum ya rika tsaftace jikinsa da muhallinsa gaskiya wannan abun yana samo asali daga rashin tsafta ne.
Sunana Labaran Jibrin, Zareku Miga, A Jihar Jigawa:
A ganina wannan matsala ce wanda ba kowa ya fahimce ta ba domin yawancin mutane a ido za ka ga cikakkun mutane ne in ba zama bane ya hada ka da su ba, misali; za ka ga mutum yana ji, yana gani, ga kafa, ga hannu, ga hankali, amma yana da tawaya ta jin kamshi ko wari, to ka ga in mutumin da bai fahimci wannan matsalar ba to, dole ya kasa yi musu uzuri akan haka, ba tare da su sun san matsalar su ba. Dan haka dole al’umma su koyi rayuwa da kowa duk wanda Allah ya hada su tafiyar mota, ko kasuwa, ko zaman majalisa, ko wajen aiki. Abin da yake haifar da hakan yawancin mutane basa tsayawa su gane su suwaye ne kafin shiga cikin al’umma, kai da kanka ka tsaya ka nutsu kayi tunani da irin siffar da ya kamata su shiga al’umma da ita ba. Hanyar da za a magance irin wannan matsalar ita ce mu koma cikin addinin mu na musulunci cewar da zarar ka ga wani dan’adam yana fama da irin wannan matsalar to yi amfani cikin hikima ka ganar da shi ta hanyar da ba zai samu damuwa ba. Hanyar ita ce dan’adam ya duba ‘ya’yan yatsunsa zai ga tsayi da kibar su ba daya ba ne, wani ya fi wani tsayi da kauri.
Sunana Hauwa Abubakar Sarki daga Suleja Jihar Neja:
Hakan yana faruwa sosai, musamman ga maza da mata masu kananun shekaru, duk yana faruwa da masu manyan shekarun ma. Amma akasari ya fi faruwa da maza masu kananu shekaru musamman masu tasowa irin yan 16,17. Hakan yana faruwa ne saboda basu san yadda za su kintsa kansu ba ga masu tasowa kenan, wasu kuma halitta ce. wasu kazanta ce wasu kuma halitta ce. Idan ta kazanta ce wanka akai-akai sannan a daina mai-maita kayan da aka cire, sannan a kuma rinka tsaftace sassan jiki. Idan ta halitta ce kuma dole shi ma sai ana wanka akai-akai da daina mai-maita kayan da aka cire da amfani da turaruka kala-kala, hakan zai taimaka wajan rage yawan tashi da mutum zai dunga yi a cikin jama’a.
Sunana Muktari Sabo, Jahun Jihar Jigawa:
Gaskiya ne, akwai mutane masu wannan dabi’a ta shigowa cikin mutane da tufafinsu ko jikinsu yana wari. Hakan na faruwa ne kodai suna da warin jiki ko kuma rashin tsabtacewa, jikin sai ka ji mutum yana wari. Wani kuma aiki zai yi a rana ya hada gumi ga rana sai ka ji yana wari. Za a magance wannan matsalar ne ta hanyar tsaftace jiki da kuma tufafi tare da yin hakan akan lokaci. Shawara a nan ita ce mutane su yi kokari wajen tabbatar da tsaftar jiki da tufafinsu kafin su shiga cikin mutane su yi cudanya da su, don gudun cutar da wani. Domin rashi yin hakan, yana iya cutar da al’umma. Allah ya sa mu dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp