A makon jiya ne, bayan cika shekara 44 da kafuwa aka sauya fasalin kamfanin albarkatun mai na NNPC zuwa cikakken kamfani mai zaman kansa. Ana fatan wannan tsarin zai kai ga gwamnatin tarayya ta tsame hannunta daga zuba kudi wajen tafiyar da harkokin kamfanin kamar yadda dokar kafa kamfanin ta samar a shekarar 1977.
Sabon kamfanin NNPC Ltd zai gudanar da ayyukansa ne a halin yanzu kamar yadda dokokin kafa kamfanonin Nijeriya ta samar a karkashin dokar ‘Company and Allied Matters Act (CAMA)’.
- Sabon Yunkurin Murkushe Barazanar Tsaro A Nijeriya
- Hukumar Kwastom Ta Cafke Miyagun Kwayoyi Na Kimanin Biliyan N1.4 A Legas
A wannan tsarin, Ma’aikatar Albarkatun Mai da Ma’aikatar Kudi suke da mallakin jarin kamfanin gaba daya ana kuma sa ran a nan gaba za a bude hannun jarin kamfanin ga al’ummar kasar ta hanyar sayar da hannayen jarin.
Idan za a iya tunawa a ranar 16 ga watan Agusta 2021 ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannun a kan dokar alkinta albarkatun man fetur wanda ya samar da tabbatar da cefanar da kamfanin NNPC don ya zama kamfani mai zaman kanshi, ana sa ran kamfanin zai gudanar da ayyukansa ta hanyar neman riba ba tare da dogara da kudaden gwamnati ba, ana kuma bukatar ganin ribar da kamfanin ke samarwa ta amfanar da masu hannun jari, wanda daga nan ne kuma za a shirya ganin hannun jarin gwamnati ya zama kashi 20 a cikin dari sauran kuma ga al’umm.
Da wannan shirin da aka samar, za a cigaba da gudanar da NNPC ne kamar yadda ake tafiyar da takwarorionta a sassan duniya, kamar Aramco a kasar Saudi Arabia, Petronas a Malaysia da Petrobras na kasar Brazil.
A shekarar 2020, Aramco ta zama daya daga cikin manyan kamfanoni a duniya inda a ranar 11 ga watan Mayu kudin ribar da ta samu ya zarce na kamfanoni irin su Apple Inc. a na kuma fatan cewa, a ‘yan shekaru masu zuwa kamfanin NNPC zai zama kamar Aramco a wajen samar da kudaden shiga ga kasar nan.
Ra’ayin wannan jaridar shi ne, tabbas wannan mataki ne da ya dace, muna kuma fatan za a samu nasara irin yadda muka gani tattare da kamfanin samar da iskar gas ta NLNG inda ta samar da ribar Dala Biliyan 100 a matsayin kudin shiga a shekara, muna da tabbacin cewa, in har aka sake wa sabon NNPC mara zai iya samun irin wannan nasarar.
Yana da matukar muhimmanci a bar sabon kamfanin NNPC ya gudanar da harkokinsa ba tare da katsalandan ba don samun cikakiyar nasarar da ake bukata.
Ana sa ran kamfanin NNPC ya zamab abban kamfani nan da shekaru masu zuwa, mun yi imanin za ta iya zama cikin manyan kamfanonin da za a yi alfahari da su a duniya.
Yana kuma da matukarm uhimmnanci a ra’ayinmu, sabbin mahukuntan NNPC su gudanar da cikakken bincike tare da garanbawul ga ma’aikatan kamfanin.
Wannan na da muhimanci don toshe duk wata hanyar da ake barnar kudaden kasa wannan abin da aka yi ta zargin kamfanin ke nan a baya. Ya kamata sabin masu tafiyar da kamfanin su tabbatar da babu almundahana da cin hanci da rashawa tattare da tafiyar.
Ya kuma kamata a dauki kwararrun ‘yan Nijeriya daga kamfanonin mai na duniya don samar da canjin da ake bukata.
Babbar tambaya anan ita ce ya za a yi da tallafin mai wanda yake tatse dan tattalin arzikin kasar nan da yake a kan gargara. Gwamnatin tarayya ta kiyasta kashe Naira Tiriliyan 6.72 a kan tallafin man fetur a shekara mai zuwa wannan kudin da aka kiyasata ya zarce kudin da aka kashe a wannan shekarar na Naira Tiriliyan 2.53.
A ra’ayinmu wannan ba abin da za a amince da shi ba ne.
Masana sun yi imanin cewa, da wannan cefanar da NNPC da aka yi ba za ta rika zuba kudade a asusun gwamnatin tarayya ba, wanda hakan na nufin cewa, a yanzu babu kudaden da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi za su rinkarabawa a tsakaninsu, amma tabbas za ta rika biyan dukkan hakoki na haraji da sauransu ga gwamnati.
A ra’ayinmu, wannan labari ne, mai kyau don zai tilastawa yawancin gwamnonin jihohi neman wasu hanyoyin samar da kudaden gudanar da harkokinsu ba tare da jiran kudi daga gwamnatin tarayya ba.
Mun dade muna kira a wannan shafin cewa, ya kamata gwamnoni su zama kamar shugabanin manyan kamfanoni ta hanyar nema wa jihohinsu kudaden shiga. Amma yanzu da a aka samu janyewar wadannan kudaden ya zama dole su nema kansu wasu hanyoyi na daban na neman kudaden shiga.
Abin takaici kuma shi ne a halin yanzu da ya kamata Nijeriya ta ribaci yadda farashin man fetur ke hauhawa a kasuwannin duniya sakamakon yakin Rasha da Yukiren amma abin ba haka yake ba, a kan haka muke kira ga sabbin mahukuntan NNPC su duba yadda Nijeriya za ta ci gajiyar irin wannan lamarin don amfanin al’umma.
Muna kara jinjina ga gwamnatin tarayya a kan wannan mataki da ta dauka.