Wasu daga cikin manoman dankalin Turawa a jihar Filato sun bayyana farbagarsu ta cewa, bana za su samu gibi mai yawa, saboda bullar wata sabuwar cuta da ke yi wa dankalin illa.
Jihar Fitalto na daya daga cikin jihohin da ke kan gaba a kasar nan wajen noman dankalin Turawa tare da fitar da shi zuwa yankunan kasar nan domin sayarawa.
- Ko Makiyan Buhari Sun San Aikin Da Ya Yi Yafi Na Gwamnatocin Baya -Minista
- Hisbah Ta Jadadda Muhimmancin Gwajin Lafiya Kafin AureÂ
Sun kuma koka kan yadda irin na dankalin ke yin matukar tsada daga watan Afirilu zuwa watan Mayu na kowace shekara, inda suka kara da cewa, hakan na shafar fara da dashensu na dankalin.
Sai dai, Sun danganta tashin farashin na irin kan yadda kayan masarufi ke kara yin tashin gwaron zabo a kasar nan.
Sun sanar da cewa, buhu daya na irin dankalin an sayar da shi a bara,a kan naira 15,000, amma a yanzu, ana sayar da shi kan naira 20,000 zuwa naira 22,000, inda wannan tsadar ta janyo wa wasu manomansa da dama, ba za su iya yin noman dankalin a bana ba.
Amma duk da wannan kalubalen, wasu manoman ba su fitar da ran samun amfaninsa mai yawa ba.
Wasu daga cikin manoman da cutar ta lalata musu amfaninsu sun bayyana cewa, hakan ya janwo musu yin asarar kudinsu da suka zuba wajen yin nomansa.
Daya daga cikin manoman, Uwargida Atong James ta ce, ta dasa irin dankalin buhu biyu a gonarta a bana.
Matar wadda gonarta take a yankin Lamingo a garin Jos, ta ce, ta haki kimanin kashi 70 daga cikin dari na dankalin, amma ko cikakken buhu daya ba ta iya samu ba.
Uwargida Atong ta ci gaba da cewa, idan ta dasa buhu biyu zuwa uku na irin dankalin Turawam tana samun daga buhu 12 zuwa 15, amma saboda bullar cutar, ta yi asara sosai. Idan ta dasa buhu biyu zuwa uku na irin dankalin Turawam tana samun daga buhu 12 zuwa 15, amma saboda bullar cutar, ta yi asara sosai a bana.
Ta kara da cewa, ta daina noman dankalin Turawan, inda a yanzu ta koma noman albasa da masara da rogo da kuma Kabeji.
Saboda irin wannan yanayin na yanzu kan noman dankalin na Turawa a yankin, za a ci gaba da samun karancin irin na dankalin Turawan.
Tabbas bisa ga irin wannan yanayin da manonsa ke fusknta na karancin irin zai yi wa karamin manominsa wahala matuka, musamman a yankin.
Ta bayyana cewa, domin a magance matsalar, akwai matukara bukatar mahukunta su kawo wa fannin dauki, musamman wajen samar da wadataccen irin na dankalin Turawa da kuma dakile yaduwar cutar.
Shi ma wani manomin na dankalin Turawa mai suna Bitrus Mador ya bayyana cewa, bullar cutar ba karamar barazana ba ce ga manoman na dankalin da ke yin noma a yankin.
Bitrus ya kara da cewa, an bayyana cewa, cutra ta bulla ne saboda samun canjin yanayi wanda hakan ya fi aukuwa a lokacin damina.
A cewarsa, wadanda suka dasa dankalin a watan Afirilu sun sa a cutar ba ta harbi dankalin da suka dasa sosai ba, inda ya kara da cewa, ya dasa buhu shida na irin na dankalin a cikin kimainin wata shida.
Shi ma wani manomin dankalin mai suna Mador ya sanar da cewa, tuni dankalin da ya dasa ya fara nuna alamar harbuwa da cutar.