Kusan za a iya cewa, shekaru 65 na samun ‘yancin kan Nijeriya, sun kai munzalin a ce yaro ya girma ya kuma waye.
Sai dai, Nijeriya wadda ta yi bikin cika sheka 65 da samun’yancin kan a makon da ya gabata, wannan batun bai kasance hakan ba, musamman saboda da gadawar cika alkawura daga bangaren mahukunta tun a baya, har kumar zuwa yau.
- Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus
- ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote
A nan za a iya cewa, wannan batun, ya faro ne tun daga lokacin Jamhuriya ta farko wato lokacin tsohon mulkin marigayi Nnamdi Azikiwe, inda kuma lamarun juyin mulkin soji suka kutso ciki wanda kuma matsalar yakin basasa da ya barke a kasar, ya kara dagula al’amura.
Kazalika, tarihin Dimokiradiyyar kasar ya sha cin karo da kwam gaba kwam baya kusan za a iya cewa, tun bayan dawowar mulkin Demokaradiyya a 1979 da kuma sake dora kasar a wata turbar ta Demokiradiyyar a 1999.
Alal misali, jamhuriyya ta hudu ta kasance ta jima sosai, amma kusan babu wasu ayyukan na inganta rayuwar ‘yan kasar da za a bigi Kirji a ce gasu an gani a kasar a zahiri.
Idan aka dubi bangaren samar da hasken wutar lantarki kusan za a iya cewa, karni da dama da suka bace, har zuwa yau Nijeriya ta gaza samar da karfin wutar da kuma rabar da ita da ta kai karfin Megawatts 5,000 musamman duba da cewa, wannan adadin bai wuce na wani can karamin birini ne, za a samar ba, idan aka yi la’kari da kasar, wadda ake mata kirari da uwa ga daukacin kasahen da ke a nahiyar Afirka.
Bugu da kari, an jibga dimbin biliyoyin Naira domin farfado da fannin, amma har zuwa yau, haka ba ta comma ruwa ba.
Wani karin abin takaicin shi ne, na kalubalen rashin tsaro da ya ke ci gaba da wata zama babbar barazana ga kasar, domin sama da rayukan ‘yan kasar 169,000 da ba su ji ba su kuma gani ba aka hallaka daga tsakanin 2006 zuwa 2021.
Sun rasa rayukansu ne, ko dai, sanadiyyar wasu tashe-tashen hankula ko na hare-haren Boko Haram ko na ‘yan bindiga daji ko a rikice-rikicen manoma da Fulani Makiyaya ko kuma a rikice-rikicen kabilanci.
A takaice, za a iya cewa, dubban mutane ne, suka rasa rayukansu kusan a karni biyu da suka bace, inda adadin ya rubanya na wadanda aka hallaka, a lokacin yakin basasa a kasar.
Hakazalika, a bangaren batun gudanar da sauye-sauye tare da yin amfani da fasahar zamani a harkar gudanar da zabe a kasar, musamman domin a gudanar da sahihin zabe da kuma dakile matsalar sayen kuri’u, amma har zuwa yau, babu abinda ya sauya wanda daga karshe, ‘yan takardar da aka yiwa wa kaci ka tashi a lokacin da aka tabka magudi a zabubbukan, ke garzaywa zuwa kotu, domin bin hakwinsu.
Kazalika, batun cin hanci da rashawa na daya daga cikin matsalar da ta daidaita kasar, an yi kiyasin cewa, a 2012, Nijeriya ta tabka asarar da ta kai ta sama da dala biliyan 400.
Wannan adadin sun isa ace, an yi amfani da su, wajen gina hanyotin Layin Dogo da makarantu da gina Asibiti da kuma masana’antu, amma abin bakin ciki, wasu sun yi kwaciyar Magirbi kan wadannan kudaden.
Amma duk da wadannan matsalolin, an gudanar da bikin na samun ‘ yancin kan kasar, musamman a yayin da, ake ci gaba da nuna damuwa a kasar .
A bangaren masana’antar kirkire-kirkiren fasaha, fannin ya samu daukaka har a idon duniya, inda misali, fitattun mawaka da kuma a bangaren masu shiyar Fina-Finai, a masana’antar Nollywood suka kai wani mataki a duniya, musamman wajrn birge masu bibiyarsu.
Alal misali, daga mawaki irinsu Dabido, Wizkid, Burna Boy, har ta kai ga, sun shahara a Nahiyar Turai.
Haka batun dai yake a fannin kimiyyar zamani na kasar, duba da cewa, Nijeriya ta kai matakin mamaye kasashen da ke Afirka a bangaren zuba kudade, a fannin.
Suma matasan ‘yan kasuwa, musamman a jihar Legas da kuma Abuja, inda suke kirirar manhajar zamani, ta hada-hadar kudade da da kuma samar da kayan fasahar zamani.
Karin wata matsalar da ke ci gaba da zamowa ruwan dare a kasar shi ne, na yawan samun karuwar kwararrun Likitoci, da ke ficewa zuwa kasashen duniya, domin neman aikin, ganin cewa, a kasashen ana tsoka, inda a Birtaniya suke ci gaba baza hajarsu, su kuma kwararrun Injinoyi na kasar nan nan da suka noma zuwa Amurka, ke ci gaba da zan akalar tsari na fannin na kasar.
Duk hakan na akuwa ne, saboda gazawar tsarin kasar wanda hakan ya sanya, aka gaza ci gaba rike irin wadannan zakakuran da ake da su a kasar.
Nigeriya ta kasance, ta na alumma sama da kaso 60, wanda kuma masu shekaru 25, suka kasance masu hazakar da za a iya amfani da ita wajen ciyar da kasar gaba.
Bugu da kari, kasar na kuma da dimbin marasa aikin yi wanda hakan ya kara haifar da samun aikata nau’ukan laifuka da dama.
Hakazalika, akwai da dama da suka haura har zuwa iyakokin kasar, misali ta hanyar amfani da kungiyar ECOWAS da kuma yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci ta Afirka wato AfCFTA wanda hakan ya bai wa kasar damar wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikinta.
Amma saboda rashin tafiyar da shugabanci yadda ya kamata da rashin ingantattun kayan aiki da rashin samar da kyakyawan yanayi a bangaren harkar tsaro, wadannan matsalolin, suna kasar cin gajiyar wannan damar.
Kasar ta cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, amma tana ci gaba da fuskantar kalubale iri-iri da suka hada da cin hanci da rashawa, matsalar rashin tsaro da ta hana yara ci gaba da zuba makaranta.
A nan, zamu iya cewa shekaru 65, sun isa ace an koyi darasi a kasar.
Kazalika, ra’ayinmu a nan shi ne, abinda ake bukata a bangaren masu rike da madafun iko, su mayar da hankali wajen wandar da tsare-tsaren da za su inganta rayuwar ‘yan kasar da kuma ciyar da kasar gaba.