An Ceto Ginin Hukumar SUBEB Bauchi Daga Barazanar Macizai

An bayyana samun nasarar ceto lalacewar da ginin hukumar lura da ilimi daga tushe ta jihar Bauchi ke yi ta hanyar barazana wa rayuwar ma’aikata ta  zubar ruwan sama da barazana da macizai ke yi wa ma’aikatan tsawon lokaci, ba tare da samun wani gyara na zo a gani ba, har sai zuwan wannan gwamnati inda aka lura da halin lalacewar da ginin ya yi tsawo lokaci aka yi gyara na musamman tare da samar da kujerun zama don samun ingancin aiki da ciyar da ilmin yaran Jihar Bauchi gaba tun daga tushe.

Farfesa yahaya Ibrahim Yero shugaban hukumar ta SUBEB shine ya bayyana haka cikin jawabinsa mai shafi takwas da ya karanta lokacin da aka yi bikin bude sabbin ofisoshin da aka gyara a harabar hukumar yammacin wannan alhamis da ta gabata. Inda ya kara da cewa tun zamanin mulkin soja lokacin  gwamnatin Kanal Abu Ali aka bude wannan ma’aikata shekaru 27 aka ci gaba da aiki da ginin ba tare da yin kwaskwarima da za ta sa ma’aikatan wajen su ji dadin aiki ba. Sai bayan da gwamnatin Bauchi ta nada shi a zaman shugaba ya lura da halin da ginin ke ciki yadda ko ruwan sama ake yi sai ko ma’aikata su rika komawa gefe guda da kayan aiki a jira idan wajen ya gama yoyon ruwa a share a ci gaba da aiki.

Yayin da a waje guda kuma macizai ke barazana a cikin gine ginen saboda yadda wasu wuraren suka zama tamkar kufayi, don haka ya dauki hotunan da irin yanayin da ginin ke ciki ya tura wa gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar don kawo dauki wa hukumar, inda gwamnan ya amince aka yi amafani da sauran wani kudi naira milyan 11,097,690.59 bayan sun rubuta wa hukumar ilmi daga tushe ta kasa UBEC kuma aka amince suka yi amfani da kudin don gyaran ofisoshin harma da yin wasu sabbin gine gine don inganta yanayin aiki da ciyar da ilmi gaba.

Farfesa Yahaya Ibrahim Yero, har wa yau ya gode wa kokarin da injiniyoyin hukumar suka yi wajen gudanar da wannan aiki cikin sauki da aminci ba tare da kashe kudi mai yawa ba, inda ya ce injiniyoyin da suke ma’aikatar za su ci gaba da gudanar da aiki mai kyau kamar wanda aka yi domin dawo da dukkan makarantun Jihar bauchi cikin yanayi mai kyau don yaran talakawa su yi karatu cikin kwanciyar hankali. Inda ya bayyana cewa tuni hukumar ta dukufa wajen kai dauki ga dukkan makarantu da ake dasu don gyara su da samar musu kayan aiki tare kuma

da inganta jin dadin malamai da basu horo don sauke nauyin da aka dora musu na ilmantar da yaran Jihar Bauchi.

Shi ma gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abdullahi Abubakar ya yaba game da wannan aiki inda ya bayyana cewa yana daga cikin kudirin gwamnatinsa na ganin an mayar da makarantun gwamnati sun kasance masu kyau fiye da makarantu masu zaman kansu saboda mutane su ji dadin sanya yaransu yin karatu a ciki. Musamman ganin yadda shi kansa tun daga firamare har zuwa sakandare da jami’a duk ya yi karatu ne a makarantun gwamnati, don haka bai ga dalilin da a halin yanzu za a bar irin wadannan makarantu a baya ba. Ya ce gwamnatinsa a shirye take wajen ganin ta samar da yanayin karatu mai kyau a makarantu da kuma inganta biyan albashi akan lokaci da biyan hakkokin ma’aikata, kamar yadda ya aiwatar lokacin da ya kama ragamar mulkin jihar Bauchi, inda ya biya dukkan  wasu basussuka da ya gada na ma’aikatan sassan ilmi da sauran sassan gwamnati.

Don haka ya bayyana cewa kofar gwamnatinsa a bude take wajen tallafawa duk wata hidima ta ci gaban ilmi saboda kuwa yaran da ke tasowa su ne manyan gobe, don haka ya zamo wajibi a basu kulawar da ta kamata. A saboda haka ne ya dauki nauyin karatun wata daliba Elizabez B. Rabson wacce ta zo ta daya a wata gasar zaben sarauniyar ilmin yara mata ta kasa wacce ta gudana a kwanakin baya. Inda ya bata kyautar nan dubu dari kuma ya ce gwamnati za ta dauki nauyin karatun yarinyar wacce ta fito daga Gemzo firamare a karamar hukumar Toro, inda za a biya mata kudin makaranta tun daga firamare zuwa sakandare har zuwa karatun jami’a.

Shi ma shugaban kwamitin ilmi na majalisar dokokin Jihar Bauchi Mohammed Inuwa Dadiye cikin jawabinsa ya yaba game da rawar da gwamnatin jihar Bauchi ta taka wajen inganta ilmi tare da samun nasarar jarrabawar makarantun sakandare, wacce a baya yara sun yi ta faduwa amma zuwa wannan gwamnati ta dauki mataki inda a halin yanzu yara da dama suke samun nasara a jarrabawar su ta kammala karatun sakandare inda suke samun tafiya manyan makarantu da sakamakon da ake nema.

Exit mobile version