Janye tallafin man fetur da sabuwar gwamnatin dimokuradiyya ta yi a Nijeriya ya haifar da cece-kuce a bangarori daban-daban. Gwamnati ta yi ikirarin cewa cire tallafin ya zama dole don ta samu kudin da za ta habaka ababen more rayuwa, jin dadin rayuwar jama’a, da habakar tattalin arziki. Sai dai da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya ba su gamsu da wannan hujja ba, domin suna ganin cire tallafin tamkar cin amanar alkawuran zabe ne da kuma nauyi ga talakawan da ke fama da wahala.
Cire tallafin man fetur ya haifar da hauhawar farashin man fetur zuwa sama da Naira 630 kan lita daya, hawan da ba a taba gani ba! Hakan ya yi tasiri matuka kan farashin kayayyaki da ayyuka, kamar sufuri, abinci, kudin makaranta, da kula da lafiya da dai sauransu. Yawan hauhawar farashin kayayyaki ya haura sama da kashi 27, mafi girman da aka taba samu.
- Mutane 19,000 Sun Amfana Da Tallafin Fadama III A Zamfara
- Cire Tallafin Fetur: Kano Za Ta Biya Ma’aikata Karin Albashin N20,000, ‘Yan Fansho N15,000.
Naira kuma ta fadi idan aka kwatanta da Dala, yayin da ake musayar kusan Naira 800 a hukumance tana ciniki sama da Naira 1,200 a kasuwar bayan fage, bambacin fiye da Naira 500. Wadannan abubuwa sun samar da karyewan karfin tattalin arzikin da tabarbarewan rayuwar ‘yan Nijeriya, musamman ma wadanda suka fi kowa rauni, masu dogaro da kai, da marasa aikin yi.
Har ila yau, cire tallafin man fetur ya haifar da tarzoma da zanga-zangar nuna rashin amincewa da yajin aiki wanda bai yi tasiri ba, yayin da ‘yan Nijeriya da dama ke nuna rashin gamsuwa da fushinsu da matakin da gwamnati ta dauka yayin da wasu kuma suka dauki hanyar ‘Sidon- look’. Kungiyoyin kwadago, kungiyoyin farar hula, da jam’iyyun adawa sun yi kira da a sauya manufar ko kuma a rage farashin mai, sun kuma bukaci a kara mafi karancin albashi, da sake duba kudin wutar lantarki, da kuma kawo karshen cin hanci da rashawa da rashin iya gudanar da ayyuka a bangaren man fetur da sauran su.
A daya hannun kuma, gwamnatin ta yi kira da a yi hakuri da fahimtar juna, inda ta ce manufar ita ce mafi alheri ga al’umma, kuma nan ba da dadewa ba za a ga amfanin ga kowa.
Amma abin lura a nan shi ne ne, a bangaren kungiyoyin kwadago sun kasa kare hakkin ‘yan Nijeriya masu karamin karfi, masu dogaro da kai, marasa aikin yi, da ma’aikatan gwamnati na jihohi sai dai kawai sun tattauna da gwanati ne kan ma’aikatan gwamnatin tarayya da ke aiki, wadanda ‘yan tsiraru ne, wannan ya nuna yadda kungiyoyin kwadago ke da karancin hangen nesa.
Wani abin takaicin kuma shi ne a halin da ake ciki da wannan wahalhalun da al’ummar Nijeriya ke fuskanta, ‘yan majalisar kasa sun “tsinci dami a kala” idan kowannensu ya yi gaba da sabuwar mota kirar Toyota Landcruiser jeeps ta Naira miliyan 160, wanda wannan ba karamar wauta bace da dolonci na dan Nijeriya.
Cire tallafin man fetur dai batu ne mai sarkakiya da ya raba kan al’ummar kasar. A gefe guda, wasu manazarta da masana sun goyi bayan manufar, suna masu cewa tallafin ba shi da amfani, ba shi da inganci, kuma mai azurta wasu tsirarun ‘yan Nijeriya ne. Sun yi nuni da cewa tallafin yana jawo wa gwamnati asarar kusan Naira tiriliyan 1 a duk shekara, wanda za a iya kashewa a wasu sassa. Sun kuma yi ikrarin cewa tallafin ya fi amfanar masu hannu da shuni, domin masu hannu da shuni sun fi amfani da mai. Sun kuma tabbatar da cewa tallafin na karfafa fasakwauri, tarawa da karkatar da man fetur zuwa kasashen makwabta, inda farashin ya yi tsada.
Don haka suka bukaci gwamnati da ta yi tsayiwar daka kan matakin da ta dauka tare da aiwatar da wasu gyare-gyare domin dakile tasirin manufofin ga al’umma.
A daya gefen kuma, wasu masana da kungiyoyi da masu fafutuka ‘yancin kai sun yi adawa da manufar, suna masu cewa tallafin yarjejeniya ce ta zamantakewa da kuma hakki na mutane.
Sun yi hasashen cewa tallafin yana bayar da taimako da tallafi ga jama’a, wadanda tuni suke fuskantan kalubale da wahalhalu. Sun kuma nuna shakku kan lokaci da kuma yadda tsarin zai kasance, inda suka ce kamata ya yi gwamnati ta tuntubi jama’a tare da tafiyar da al’umma kafin ta dauki wannan tsattsauran mataki.
Sun kuma kalubalanci gwamnati da ta yi lissafin kudaden da aka tara daga tallafin da aka cire da kuma tabbatar da gaskiya da rikon amana a bangaren man fetur.
Cire tallafin man fetur wani abu ne mai daci ga kashi 99 cikin 100 na ‘yan Nijeriya, wadanda tuni suke fafutukar shawo kan tabarbarewar tattalin arziki da kalubalen tsaro. Manufar cire tallafin ta fallasa matsalolin da ke tatare da tattalin arzikin Nijeriya da kuma nuna rashin daidaiton tsarin tattalin arzikin Nijeriya, wanda ya dogara kacokan kan kudaden shiga da man fetur ke shigo da su daga waje.
Manufar kuma ta nuna cin amana da rashin amincewar da jama’a ke da ita akan gwamnati, wadda ta hau kan madafun iko ta silar kawo sauyi da fatan alheri.
Duk da hujjojin da magoya baya da masu suka suka gabatar suna da inganci.
A karshe, idan aka takaita dukkanin muhawarar, daga ina za’a samo kudaden da aka ce za su yi rara tun da shi kasafin kudin bara tashin farko rabinsa bashi ne aka ciwo, kuma shi ma kasafin kudin wannan shekaran wanda aka gabatar kwanan baya fiye da rabi bashi ne za’a ciwo. Shin raba kayan tallafi da motocin CNG (motocin safa safa masu amfani da iskar gas) shi ne za su zama mafita?
Wanna al’amari ya fi kama da wauta da shirme!