Alkalin Alkalan Nijeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ya yi sammacin manyan alkalan Babbar Kotun Tarayya da ta Jihar Kano kan ba da dokoki masu karo da juna da suka shafi rikicin masarautar Kano.
Babbar kotun tarayya da ke Kano, karkashin jagorancin mai shari’a S. A. Amobeda, ta bayar da umarnin korar Sarkin Muhammadu Sanusi na II daga fadar Kofar Kudu, tare da dawo da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.
- Majalisar Dattawa Ta Amince Da Dokar Dawo Da Tsohon Taken Kasa
- Tabbatar Da Cikakken ’Yancin Kai, Ita Ce Za Ta Kyautata Dangantakar Sin Da Japan Da Korea Ta Kudu
A gefe guda kuma babbar kotun Jihar Kano, ta bayar da umarnin hana fitar da Sarki Sanusi II daga fadar masarautar Kano.
Umarnin da kotunan biyu suka bayar ya haifar da ruÉ—ani da rashin tabbas kan harkokin shari’a a jihar.