Babban rukunin gidajen rediyo da telabijin na kasar Sin (CMG), ya kaddamar da sabon aikin yayata tamburan kasuwanci na kasar Sin, jiya Asabar, a birnin Beijing na kasar.
Shugaban CMG, Shen Haixiong, da mataimakin ministan kula da albarkatun ruwa na kasar Sin, Liu Dongshun, da dimbin manyan kusoshi sun halarci bikin kaddamarwar, inda suka shaida kafuwar wani dandalin samar da bayanan gaske masu alaka da tamburan kasuwanci na kafar CMG.
Da yake jawabi a wajen bikin, Mista Qi Zhuquan, mataimakin shugaban CMG, ya ce CMG din zai yi kokarin samar da karin gudunmowa ga yunkurin yayata tamburan kasuwanci na kasar Sin, ta hanyoyin gudanar da bincike, da mu’amala da bangarori daban daban, da raya harkoki masu alaka da fasahohin zamani, da dai sauransu.
Kana duk a jiya Asabar, an shirya taron kulla hadin gwiwa bisa wasu manyan ayyukan da kafar CMG za ta gudanar da su a shekarar 2027 mai zuwa, a birnin na Beijing, inda aka gabatar da wasu manyan ayyuka fiye da 110 da kafar CMG za ta aiwatar, masu nasaba da aikin watsa labarai, da tsara wasan kwaikwayo na telabijin, da daukar fim din labarin gaskiya, da shirye-shiryen nishadantarwa, da dai makamantansu. (Bello Wang)














