Rukunin Kamfanin Dangote ya sake jaddada muhimmiyar rawar da samar da kayayyaki a cikin gida ke takawa wajen karfafa juriyar tattalin arzikin Nijeriya.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a karshen mako ta bakin Babban Manajan Kamfanin, Mista Abdullahi Bello Danmusa, wanda ya wakilci Daraktan Yanki/Mai Ba Shugaban Kamfanin Dangote, Fatima Wali-Abdurrahman, shawara a Ranar Musamman ta Dangote a bikin Baje Kolin Kasuwanci na Abuja da ake gudanarwa.
Da yake magana a yayin bikin baje kolin na bana mai taken, “Juriyar Tattalin Arziki: Ciniki, Haraji da Tattalin Arziki,” Mista Danmusa ya ce haraji na daga cikin muhimman ginshikan ci gaban kasa, yana mai cewa Kamfanin Dangote na daukar nauyin biyan harajinta da muhimmanci, kuma yana samar da makudan kudaden shiga ga gwamnati duk shekara, tare da tallafa wa samar da ayyukan yi, bunkasa sana’o’i da kirkirar darajar tattalin arziki a dukkan ayyukansa.
Ya ce ciniki zai iya haifar da babbar fa’ida ga tattalin arziki idan aka tallafa masa da karfin samar da kayayyaki a cikin gida.
Ya ce: “Ciniki ya fi ma’ana idan aka tallafa masa da samar da kayayyaki. Babu wata kasa da za ta iya ginuwa kan juriyar tattalin arziki mai dorewa ta hanyar dogaro fiye da kima da kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje, wadanda za ta iya samarwa cikin gasa a cikin gida.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa Kmfanin Dangote ke ci gaba da zuba jari a masana’antu da karfin samar da kayayyaki a fannonin siminti, sukari, gishiri da kayan kara dandano, masarufi, takin zamani, sinadaran petrochemical da tace albarkatun man fetur.
“Taken bikin Baje Kolin Kasuwanci na bana shi ne, ‘Juriyar Tattalin Arziki: Ciniki, Haraji da Tattalin Arziki,’ ya yi daidai da hakikanin yanayin da muke ciki a wannan lokaci.”
Ya ce: “Juriyar tattalin arzikin Nijeriya a karshe za ta dogara ne da wani muhimmin zabi: ko mu ci gaba da shigo da kayayyakin da za mu iya samarwa a cikin gida, ko kuma mu gina karfin da zai ba mu damar samarwa, yin gogayya da sauran kasashe da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.”
Danmusa ya lura cewa karfafa karfin masana’antun cikin gida zai taimaka wajen fadada harkokin tattalin arziki, samar da ayyukan yi, tallafa wa ’yan kasuwa na cikin gida da kuma rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje fiye da kima.
Ya kara da cewa jarin da Kamfanin ya zuba a fannoni daban-daban ya nuna jajircewarta wajen tallafa wa bunkasar masana’antun Nijeriya da kuma bayar da gudummawa wajen gina tattalin arziki mai inganci da juriyar fuskantar kalubale.
Shi ma da yake magana a Ranar Musamman ta Dangote, Mataimakin Shugaban Farko na kungiyar ’Yan Kasuwa ta Abuja (ACCI), Farfesa Adebisi Adesugba, ya yaba wa Kamfanonin Dangote bisa gudummawar da suke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.
Adesugba, wanda ya wakilci Shugaban ACCI, Emeka Obegolu, SAN, ya ce hadin gwiwar da ke tsakanin Dangote da kungiyar ya nuna muhimmanci matuka.
Ya lura cewa jarin da Dangote ya zuba a fannoni masu muhimmanci, ciki har da siminti, takin zamani, noma, tace man fetur da sinadaran petrochemical, ya taimaka wajen karfafa karfin samar da kayayyaki a cikin gida, samar da guraben ayyukan yi, rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje da kuma taimakawa wajen samar da kudaden waje.
Ya ce: “ACCI na kallon Dangote ba kawai a matsayin mai baje koli da mai daukar nauyin taron ba, har ma a matsayin abokin hulda na dabarun kasuwanci.”
Ya ce hadin gwiwar da ke tsakanin ACCI da Dangote ya taimaka wajen samar da damammaki ga ’yan kasuwa da ’yan kwazo, tare da tallafa wa harkokin ciniki, zuba jari da ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
Adesugba ya kara bayyana godiyar kungiyar ga Dangote bisa dogon lokaci na hulda da hadin gwiwa da ACCI, yana mai bayyana wannan hadin gwiwa a matsayin muhimmin dandali wajen karfafa al’ummar ’yan kasuwa da bunkasa damammakin tattalin arziki.
Ranar Musamman ta Dangote ta hada shugabannin ’yan kasuwa, wakilan gwamnati, masu zuba jari, masu baje koli, ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, a matsayin wani bangare na shirye-shiryen da ake gudanarwa a Baje Kolin Kasuwanci na kasa da kasa na Abuja.
Shi ma da yake magana a Ranar Musamman ta Dangote, Mataimakin Shugaban Farko na kungiyar ’Yan Kasuwa ta Abuja (ACCI), Farfesa Adebisi Adesugba, ya yaba wa Kamfanonin Dangote bisa gudummawar da suke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.
Adesugba, wanda ya wakilci Shugaban ACCI, Emeka Obegolu, SAN, ya ce dogon hadin gwiwar da ke tsakanin Dangote da kungiyar ya nuna muhimmiyar rawar da kamfanoni masu daukar nauyi ke takawa wajen habaka kasuwanci, zuba jari da harkokin kasuwanci a Nijeriya da ma yankin Afirka baki daya.
Ya lura cewa jarin da Dangote ya zuba a fannoni masu muhimmanci, ciki har da siminti, takin zamani, noma, tace man fetur da sinadaran petrochemical, ya taimaka wajen karfafa karfin samar da kayayyaki a cikin gida, samar da guraben ayyukan yi, rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje da kuma taimakawa wajen samar da kudaden waje.
Ya ce hadin gwiwar da ke tsakanin ACCI da Dangote ya taimaka wajen samar da damammaki ga ’yan kasuwa da ’yan kwazo, tare da tallafa wa harkokin ciniki, zuba jari da ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
Adesugba ya kara bayyana godiyar kungiyar ga Dangote bisa dogon lokaci na hulda da hadin gwiwa da ACCI, yana mai bayyana wannan hadin gwiwa a matsayin muhimmin dandali wajen karfafa al’ummar ’yan kasuwa da bunkasa damammakin tattalin arziki.
Ranar Musamman ta Dangote ta hada shugabannin ’yan kasuwa, wakilan gwamnati, masu zuba jari, masu baje koli, ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, a matsayin wani bangare na shirye-shiryen da ake gudanarwa a Baje Kolin Kasuwanci na kasa da kasa na Abuja.
Taron ya ba masu ruwa da tsaki damar tattaunawa kan batutuwan da suka shafi haraji, ciniki, bunkasa masana’antu, zuba jari, samar da kayayyaki a cikin gida da kuma fadadden damar da ke akwai ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.













