Cutar Cizon Sauro Na Salwantar Da Rayuka A Kano

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Annobar zazzaɓin cizon sauro na cigaba da jawo salwantar rayuka a sassan jahar Kano, sakamakon rashin ɗaukar wani ƙwaƙƙwaran mataki daga ɓangaren Gwamnatin jahar, kamar yadda yawancin jama’a ke kokawa. Manyan Asibitoci suna cikar ƙwari da marasa lafiya,dan har ta kai ana shinfiɗe wasu a ƙasa. A ziyarar da wakilinmu ya kai asibitin Murtala a ranar Alhamis ya tarar da ɗinbin marasa lafiya wasu a shimfiɗe a ƙasa,wasu kuwa da aka kwantar sun ce da katifunsu suka zo saboda ba gado da za a kwantar da marasa lafiyar musamman waɗanda jikinsu ya yi tsanani suke buƙatar gaggawa.

Wani da ya kawo wata matashiyar ƙanwarsa da ta kamu da cutar ya ce, sun zo Asibitin ne ɓangaren taimakon gaggawa amma ba gado, sai dai wani Ma’aikacin lafiya ya rubuta masa wasu magunguna da allurai masu tsada da ya ce, idan aka yi mata su za ta sami sauƙi, hakan kuwa aka yi ya sayo aka yi mata sannan ta dawo hayyacinta suka  koma gida.

Wata majiya ta tabbatar mana da cewa, ba wani tanadin kawo ɗaukin gaggawa da gwamnatin Kano ta yi kan annobar cutar zazzaɓin cizon sauron a asibitoci, sai dai kawai kowa tasa ta fisshe shi, dan kuwa ko inda ake sai da magunguna a asibitoci na gwamnmati ba a faye samun maganin zazzaɓin ba da ake saye da rahusa. Dole ta sa sai dai idan an rubuta wa majinyaci magani ya nemi mafita, in yana da abin saye. Idan kuma babu, haka ake dangana sai abin da Allah ya yi. Hakan ta sa ana samun rashe-rashen rayuka da ake danganta su da sanadin zazzaɓin sauron.

Wani magidanci ya shaida mana ’ya’yansa kusan biyar sun kamu da cutar wanda sai da ta kai shi ga rance sannan aka shawo kan lamarin, dan kuwa Asibitin in an je ba kuɗi ma sai dai ka dawo da mara lafiya ka aje.

Wasu na ganin cewa rashin wani yunƙurin gaggawa daga Gwamnatin Kanon ya jawo cigababan  cutar. Jama’a da dama na ganin ɓangaren Gwamnati ta yi wa matsalar zazzaɓin da ke addabar al’uma ko in kula hakan na daɗa ta’azzara lamarin a wajen waɗanda ba su da yadda za su yi.

Ƙoƙarin jin ɓangaren gwamnati ta bakinn Kwamishinan lafiya Dokta Kabir Ibrahim Getso har zuwa lokacin rubuta wannan labarin ya ci tura.

Exit mobile version