Asusun Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ya ce zuwa yanzu cutar mashako ta kashe rayukan yara kanana 122 a Nijeriya.Â
A wata sanarwa da wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Dokta Cristian Munduate, ta fitar a ranar Juma’a, ta ce cutar ta shafi jihohi 27 a Nijeriya.
- Majalisa Ta Ki Amincewa Da Shirin Tinubu Na Daukar Matakin Soji A Kan Nijar
- Manchester United Ta Dauki Hujland Daga Atalanta
Kana ta ce, zuwa watan Yulin 2023, an samu wadanda suka kamu da cutar 3,850 yayin da aka tabbatar da mutum 1,387 sun kamu da cutar.
Sanarwar, ta ce cutar ta shafi jihohin Kano, Yobe, Katsina, Lagos, Birnin tarayya Abuja, Sakkwato da Zamfara, wanda cutar ta kama a tsakanin yara ‘yan shekara 2 zuwa 14.
A cewarta, abin damuwa ne matuka da aka gano kaso 22 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar ba su karbar rigakafin cututtuka da ake yi wa yara.
“Mafi rinjaye na yaran da suka kamu da cutar, musamman wadanda suka mutu ba su taba karbar rigakafin kariya ko sau daya ba.”
Cristian, ta kara da cewa domin yaki da cutar, UNICEF ta na hadin guiwa da cibiyar binciken cututtuka ta Nijeriya (NCDC), jihohin da lamarin ya shafa, hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA), domin samar da tallafin kwararru da yadda za a dakile cutar.
Tallafin na UNICEF ya kunshi kudade, saukaka jigila wajen kai rigakafi, tuntubar masu ruwa da tsaki, kayan aiki da taimakawa a bangaren rigakafin a jihohin da lamarin ya shafa.
A cewarta sauran sun hada horas da ma’aiktan kiwon lafiya, masu bada gudunmawa, samar da takunkumin fuska, man tsaftace hannu da sauran kayan aiki.
UNICEF, ta shawarci iyaye da suke tabbatar da ‘ya’yansu suna amsar rigakafin cututtuka domin kare su daga cututtuka.
Ta kuma bukaci gwamnatoci da su tashi tsaye wajen kawo karshen cutar, inda ta ba da tabbacin ba su cikakken goyon baya domin kare yaran Nijeriya daga cutar.