Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta sake tsawaita yajin aikin da take yi zuwa makonni hudu bayan karewar wa’adin yajin aikin da ta shiga a ranar 31 ga Yuli, 2022.
Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana matakin da kungiyar ta dauka a ranar Litinin a cikin wata sanarwa da ta fitar.
- An Kashe Makiyaya 6, Wasu Sun Bace Bat A Filato
- Matsin Rayuwa: Za A Rage Farashin Man Fetur A Afrika Ta Kudu
Ya ce majalisar zartaswar kungiyar ta dauki matakin ne bayan tattaunawa mai zurfi kan gazawar da gwamnati ta yi wajen magance matsalolin da suka shafi ASUU na shekarar 2020.
Osodeke ya ce kungiyar ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin zuwa makonni hudu domin bai wa gwamnati isasshen lokaci domin shawo kan matsalolin da ake fama da su.
Yajin aikin a cewarsa, zai fara aiki ne daga karfe 12.01 a ranar Litinin, 14 ga Agusta, 2022.
Idan ba a manta ba ASUU ta jima tana yajin aikin kan gaza cimma matsaya game da bukatunta da ta dade tana nema a wajen gwamnatin tarayya.
Lamarin da ya janyo a satin da ya wuce kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) da sauran kungiyoyi suka shiga zanga-zangar mara baya ga ASUU don jan hankalin gwamnatin tarayya na kawo karshen takaddamar.