Babban Bankin Nijeriya (CBN) daga karshe dai ya amince da bai wa bankunan kasuwanci umarnin su fitar da tsoffin takardun kudade kuma su karbi tsoffin muddin kwastomomi suka kawo musu, kamar yadda gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Charles Soludo wanda tsohon gwamna CBN ne ya shaida.
Akwai wasu majiyoyi da suka nakalto cewa tun makon jiya dai wasu bakunan suka yi ta bai wa mutane takardar kudi tsoffi.
- Gwamnatin Kogi Za Ta Fara Hukunta Duk Wanda Ya Ki Karbar Tsoffin Kudi
- Shin CBN Ya Umurci Bankuna Su Ba Da Tsafaffin Kudi?
Gwamnan ya ce, yanzu mutane na da damar zuwa bankuna su shigar da takardun kudadensu tsoffi a kashin kai ko kamfanonin kuma ba a kiyasce lokaci ba.
Soludo ya ce, gwamnan CBN ya bayar da umarnin ne a lokacin wata ganawa da kwamitin bankuna da ya gudana a ranar Lahadi 13 ga watan Maris.
Soludo ke cewa, “Gwamnan CBN Dakta Godwin Emefiele da kansa ya tabbatar min a zantawarmu ta wayar tarho a daren ranar Lahadi.
“Don haka mazauna jihar Anambra ina basu shawarar kai tsaye su karbi tsoffin takardun kudi na 200, 500, da na naira 1,000 wajen yin kasuwancinsu tare da karɓan tsohon da sabon takardar kudi.”
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su kai rahoton duk wani bankin da ya ki amsar tsoffin kudi a lokacin da suka ke shigar da kudadensu.
“Gwamnatin Anambra ba wai za ta tsaya kai rahoton bankin da ya ki karban tsohon kudi ba ne, a’a rufe bankin za mu yi kai tsaye.”
Duk kokarin da aka yi don jin ta bakin bankin CBN kan wannan ikirarin na Soludo ya citura domin ba a iya samun Isa Abdulmumin, Kakakin babban bankin ba zuwa hada wannan rahoton.
Wasu majiyoyi masu karfi sun tabbatar da cewa eh lallai an Yi ta ganawa da gwamnan CBN da manyan jagororin bankuna a ranar Lahadi kuma tabbas sabon umarni na biyu.