Bayan tattaunawa sosai tare da shiga tsakani ta kai ga sako karin fasinjoji 11 na jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da aka yi garkuwa da su a ranar 28 ga Maris, 2022.
Hadimin Sheikh Dakta Ahmad Abubakar Gumi, Malam Tukur Mamu (Dan-Iyan) Fika) ne ya shiga tsakani har aka ga sake sakin wasu bakwai daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a ranar Asabar.
- NSCDC Ta Bankado Shirin ISWAP Na Kai Hare-Hare A Makarantu Da Cocina A Abuja
- ‘Yan Nijeriya Sun Yi Alhinin Rasuwar Babban Sakataren OPEC Sanusi Barkindo
Wadanda aka saki a ranar Asabar sun hada da Bosede Olurotimi, Abubakar Zubairu, Alhassan Sule da Sadiq Ango Abdullahi.
Sauran fasinjojin da suka yi sa’a sun hada da Muhammad Daiyabu Paki, Aliyu Usman da kuma wani dan kasar waje daya tilo dan asalin kasar Pakistan, Dr. Muhammad Abuzar Afzal.
Da yake magana kan lamarin, Mamu ya ce nasarar da aka samu a ranar Asabar din na sakin wadanda lamarin ya rutsa da su ya tabbatar da muhimmancin sulhu da Sheikh Dr. Ahmad Gumi ke yi a tsakanin ‘yan bindiga.
“Ina so in tabbatar wa al’umma cewa, duk abin da ya faru a yau, ni kadai ne ya kaddamar da shi tare da cikakken goyon baya da addu’a daga shugabana, Sheikh Gumi.
“Don haka ina jaddada cewa gwamnati na da ikon ceto wadanda ba su ji ba ba su gani ba a rana daya. Wannan mutum daya ne kawai da ya sadaukar da rayuwarsa. Babu wata hanyar soja da za ta magance tabarbarewar tsaro a Nijeriya.
“A duk abin da nake yi, ba na bukata ko kuma bukatar wani lada a wurin kowa sai dai daga wurin Allah kuma ina fatan al’ummar da muka sadaukar da rayuwarmu za su fahimci hakan,” in ji Mamu.
Mai sasantawar ya kara da cewa an mika wadanda aka sako su bakwai ga sojoji kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa Kaduna.
“Wurin da su (masu garkuwa) suka bayar yana da nisa da kuma hadari. Akwai shingen binciken sojoji kafin kutsawa cikin dajin,” ya bayyana.