Da Sana’ar Malumta Na Shigo Legas Kafin Na Zama Sarkin Hausawan Shasha – Alhaji Iliyasu

Sarkin a’l’ummar Hausawa mazauna unguwar Shasha da ke karamar hukumar Alimosho a gundumar Agege cikin garin Legas, Alhaji Iliyasu Isa Kira ta karamar hukumar Musawa a jihar Katsina, ya bayyana kadan daga cikin tarihinsa na farkon zuwansa Legas, inda ya ce, da sana’ar malumta  ya farawa shigo wa garin.

Ya cigaba da cewa farkon zuwansa Legas ya zo ne da sana’arsa ta malunta a inda ya fara sauka unguwar Mile 12, ya cigaba da hulda da ’yan kasuwar Gwari domin yi mu su addu’o’i a kan harkokin kasuwancinsu Allah ya biya masu bukata.

Daga nan sai ya koma unguwar Ikotun wajen Sarkin Kausawan Ikotun, Alhaji Nuhu Alasan, shi ma su ka fara harkar almajirci da shi.

Ya ce, wani  lokaci ma idan sarkin zai fita zuwa wadansu unguwannin  garin Legas ya kan rike ma sa jakarsa su tafi tare. A cewarsa, haka su kai ta yi har ya dawo unguwar Shasha, wanda a nan ne a halin yanzu shi ne Sarkin al’ummar Hausa mazuna unguwar ta Shasha.

Sarkin ya cigaba da cewa a kan haka ne ya ke isar da sakon godiyar sa ga al’ummar Hausawa na wadannan unguwanni da ya zauna, musamman al’ummar Hausawan unguwarsa ta Shasha wadanda su ka ga ya cencanta suka sanya hannunsu da bakunan su acewarsa wadansuma da aljihunsu aka nadashi amatsayin sarkin al-ummar hausawa shasha agundumar garin agege da fatan Allah ya saka masu da Alherinsa amin ya kara da cewar kuma zaiyi iyakar kokarisa awajan  kare hakokin al-ummar hausawan na unguwar shasha da kewayenta bakidaya sannan ya nuna bacin ransa na karancin hadin kan sarakunan al-ummar hausawa mazuna jihar ta legas da suka kasa hada kawunan juna nsu awajan zabar mutun daya tilo wanda za’a nada shi amatsayin sarkin al-ummar hausawan legas da kewayenta bakidaya sannan kuma ya ummurci sara kunan al-ummar hausawan mazuna legas dasu fara yin tunanin yin hakan kafin nanda lokaci kadan mai zuwa yakara da cewar yin hakan shine zaifi zama alheri ga sarakunan dama mabiyansu bakidaya.

Sarkin na al-ummar hausawan shasha iliyasu isa kira da ya juya kan bayanin irin cigaban da yakawo ma al-ummar hausawanshi na unguwar shasha kuwa cewa yayi lallai ya kawo ma al-ummarsa  gaggarumin cigaba acewarsa bayan alhaji aminu dogara sarkin al-ummar hausawa jihar legas ya nadashi a matsayin sarkin hausawan unguwar shasha sai ya cigaba da hada kawu nan hausawan domin su rika gudanar da taro daga lokaci zuwa lokaci domin tattau nawa akan matsalolin da suke damunsu tareda kawo hanyoyin war warewa da kuma kawo wadan zasu kara ciyar da al-ummar hausawan unguwar gaba da kewayenta bakidaya.

Sannan kuma ya kara cewa ya nada kwamtin binciken wadanda sukayi shekaru aru aru alegas basu zuwa gida domin ganin iyayensu da iyalansu injishi kuma sun sami mutane da yawa masu irin wannan matsalar sukayi masu shatara ta arziki domin zuwa gida gano yan uwansu dake arewacin Nijeriya sannan kuma ya ummurci alummar hausawan na unguwae ta shi ta shasha dasu cigaba da hada kawunan junan su awajan gudanar da irin wannan hadin kai domin Karin samu cigaba aungwar ta shasha bakidaya sannan kuma yacigab da yabama uwar  kungiyar katsinawa mazuna  garin legas Dakta hajiya asabe matar margayi tsoho shugaban kasar Nijeriya janaral shehu musa yaraduwa akokarinta na tallafama kungiyar ta katsinawa mazauna jihar legas da al-ummar katsina bakidaya injshi da fatan Allah yasaka mata da Alheri bakidaya .

Exit mobile version