Sani Abdullahi Anwar" />

Da Sauran Rina A Kaba: Sulhu Tsakanin Ganduje Da Sarki Sanusi Bai Kammala Ba

Tun a daren ranar Juma’ar da ta gabata ne, Shugaban Kungiyar Gwamnnoni Nijeriya, Kayode Fayemi tare da Alhaji Aliko Dangote da sauran wasu muhimman mutane masu fada a ji suka shiga tattaunawa da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar  Ganduje da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi 11, don sasanta tsakanin a birnin tarayya Abuja.

Kamar yadda rahoton ya nuna,  Shugaban kungiyar gwamnonin, Kayode Fayemi da Alhaji Aliko Dangote da kuma wasu manya daga cikin masu fada a jin, suna ta kokarin ganin Shugabannin biyu sun samu daidaito sakamakon wani sabani da ya shiga tsakanin su da ake kyautata zaton na da alaka da siyasa tun bayan kammala zaben bana.

A yayin fara wannan tattaunawar ne kuma nan take suka taya junansu murnar Sallah tare da fatan alheri bisa kammala azumin watan Ramadanan da ya gabata da kuma sauran bukukuwan Sallah.

Haka zalika, dukkanin Shugabannin sun gabatar da jawabai ga sauran al’ummar Musulmi, inda suka bukaci sauran Musulmi musamman ma al’ummar Jihar Kano da su  ci gaba da koyi da kyawawan abubuwan alherin da suka koya a watan azumin Ramadanan da ya wuce.

Har ila yau, Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II, ya yi amfani da wannan dama wajen taya  Gwamnan Kanon murnar sake lashe zabensa da ya yi a karo na biyu, ya kuma yi masa fatan samun cikakkiyar nasara daga wannan shekara ta 2019 zuwa ta 2023 da zai kammala.

Tun dai bayan kammala zaben wannan shekara ne, Ganduje da Sarkin suka sanya kafar wanda daya da juna, wanda hakan ya yi sanadiyar kekketa Masarautar Kanon har gida biyar a cikin dan kankanin lokaci bayan sanyawa dokar da Majalisar Jihar Kanon ta yi na karin Masarautu hudun da gwamnan ya amince da ita.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da aka taba shiga tsakanin gwamnan da Sarkin ba, duk dai da cewa a wannan karon rashin jituwar tasu ta fi yin tsamari. Har izuwa yanzu dai, ba a cimma matsaya a kan batun yin sulhun ba kamar yadda mai Magana da yawun Gwamnan Kano, Malam Abba Anwar ya bayyanawa Jaridar Leaderhip A Yau Lahadi.

Haka zalika, a jiya ne Fadar Sarkin Kano Sanusi 11, ta aika da takardar amsar tuhumar da Fadar Jihar Kano ta aike masa ta karkashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji a ranar  Alhamis din da ta gabata, ta kuma umarce shi da ya gaggauta amsa tuhumar kafin awanni 48.

Har ila yau, sakamakon amsa wannan tuhuma da Fadar Sarkin ta yi a jiyan, wasu na ganin cewa, ba karamin ruwa ta ballo ba, don kuwa ba lallai ba ne gwamnan ya yarda a ci gaba da zaman tattaunawar tare da shi da Sarkin da kuma masu kokarin ganin duk yadda za a yi an sasantar.

Exit mobile version