Dabarun Da Masu Maganin Gargajiya Ke Amfani Da Su Wajen Warkarwa

Akwai dabari masu yawa da masu maganin gargajiya ke bi wajen gano cuta da yadda za a magance ta. Daga cikin wadannan hanyoyin gano cutar akwai neman bayani daga mara lafiya, domin jin tarihin yadda ya fara rashin lafiyar ko yaddda ta shige shi, saboda haka sai mai magani ya bukaci ya bayar da bayani a kan bin da ya same shi, wannan na daya daga cikin hanyar gane cuta. Baya ga wannan kuma akwai lura, bisa yanayin kwareawar da masu maganin gargajiya ke da ita, a fannin sanin cututtuka, sukan gano cuta ta hanyar lura da nazari.
Haka kuma akwai cutar da ake iya ganinta a zahiri, wadda ko ba a tambayi mara lafiya ba, ana iya gane ta. Sannan kuma akwai cutar da masu maganin gargajiya ke ganowa bisa baiwa. Saboda haka dukkan wadannan hanyoyin masu maganin gargajiya na binsu domin gano cuta.
Idan aka fahimci cuta, sai kuma maganin da za yi amfani da shi domin samun waraka. A nan akwai hanyoyi daban-daban nan ma da masu magani ke bi wajen samar da magani.
Daga cikin hanyar da masu magani ke wajen warkarwa ta hanyar gwama dabi’a. Masana dabi’a na da fahimtar cewa, dukkan halitta na da dabi’a. Dole halitta ta kasance da dabi’a daya daga cikin wadannan dabi’u hudu wato, ko Nari ko Turabi ko Hawa’i ko kuma Ma’i. Saboda haka masu warkar da cewa, ta irin wannan hanya, sun tabbatar da cewa, kowane ciwo yana da dabi’arsa.
Kamar yadda ake gwama dabi’ar da ta zo daidai domin samun nasara a tsakanin dabi’un guda biyu haka ake gwama wadanda suke da sabani dimin yakar juna ko kawar da wani daga ciki.
Misali, idan ka hada wani abu mai dabi’ar ruwa da mai dabi’ar wuta, ba za su taba zama wuri daya ba, kamar ka dora ruwa a kan wuta, dole ruwan zai kashe wutar, ko kuma wutar ta kone rowan, saboda haka, shi ma haka ciwo yake yana da dabi’a, saboda haka za a lura da irin dabi’ar ciwon sai a samar da maganin da yake da dabi’ar da za ta yake shi, ta haka za kawar da ciwon.
Ga kuma yadda wadannan dabi’u suke da kuma yadda kowane mutum ke siffantuwa da daya daga cikinsu.
Kamar yadda aka bayyana wannan dabi’a ce da kowace halitta ke da ita. Saboda haka irin wadannan halaye na kowace dabi’a haka ciwon da ke da wannan dabi’ar shi ma zai siffatu da halayyar dabi’ar. Misali ciwon da ked a dabi’ar Nari za ka yana bayyana kansa kamar yadda duk inda wuta take ana saurin ganeta, haka za ka samu ciwo ne wanda yake jefa mai shi cikin mawuyacin hali a cikin karamin lokaci, sannan kuma ciwo ne da ked a bukatar naciya wajen neman magani.
Irin wannan ciwo da ked a dabi’ar wuta, dole bisa masu irin wannan hanya ta waraka maganinsa ya zama yana da dabi’a irin ta ruwa. Domin kuwa ruwa shi ne ke magance wuta kuma idan an lura da kyau wuta da ruwa ba sa zama inuwa daya. Saboda haka da zarar ruwa ya hadu da wuta dole ta bar wurin.
Haka ake amfani irin wannan hikimar ta samar da waraka ga cututtukan da ke dabi’a iri daban-daban.
Malaman aufaku,dana ramli.dana ilmul huruff.dana hisabi.da ilmul falaki,sun tabbatar akwai halayya guda 4 wadda kowane halitta yana da daya daga cikinta,nafarko.
1 Nari > wuta.
2 Ma’i > Ruwa.
3 Hawa’i > Iska.
4 Turabi > Kasa.

1 Nari: wadda yake da dabi’ar Nari. Za ka ga yana saurin fadar ra’ayinsa. yana kuma yawan son nishadi, yana yawan son rinjaye a ko’ina. yana yawan jiji da kai, kuma ba shi da rikon sirri, mai tsatsauran ra’ayi ne, mai yawan neman kudi, mai zafin zuciya da fada, mai saurin sakkowa.
2 Turabi: wadda yake da dabi’ar Turabi, za ka ga yana da hakuri mai sanyin jiki, mai yawan da na sani, mai yawan sha’awa, mai yawan tunani mai amfani, mai kaskantar da kai, mai jan hankali wajen Magana, mai rikon sirri.
3 Hawa’i: wadda yake da dabi’ar Hawa’i za ka ga yana da zafin nama, mai yawan tunani a duk abin da aka gaya masa don gano gaskiya, fitinan ne ne kuma mai yawan tafiye-tafiye, mai nuna bambanci a ko’ina, mai kirkire-kirkire da yin nasara.
4 Ma’i: Wanda yake dabi’ar ma’i za ka ga ya shahara a rayuwarsa, mai yin rinjaye duk inda ya sa gaba, mai iya siyasa da yaudarar mutane, abu maigirma da hatsari yakan dauke shi ba wani abin tsoro ba ne, mai yawan yin abin da wani zai amfana.
Saboda haka masu maganin gargajiyar Hausawa na amfani da irin wannan hikima ta gwamin dabi’a wanda kuma cikin ikon Allah ana samun waraka daga dukkan wata larurar rashin lafiya.

Exit mobile version