Daga Ranar 9 Zuwa 12 Ga Watan Zulhaj 1442

Zulhaj

LITININ

Litinin jajibarin babbar Sallah,  tara ga watan Zulhaj,  shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitrta,  Annabi Muhammad S. A. W. daidai da goma sha tara ga watan Yuli,  shekarar 2021.

Gobe take Sallah,  kuma yau ake hawan Arfa,  inda akan bukaci al’umar Musulmi a tashi da azumi yau.  Ana ci gaba da sayen ragunan layya,  da kayayyaki na Sallah,  kama daga na girke-girke zuwa na sawa don adon Sallah. Sai dai kuma kayayyaki na ci gaba da yin tsada.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari,  ya bukaci gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi na kasar nan,  a hada karfi wuri guda domin samar da kayayyaki na kyautata rayuwar jama’ar Nijeriya.

Fadar Shugaban Kasa ta mayar wa da Hassan Mathew Kukah martani, a game da furucin da ya yi cewa makarantun kiristoci kidinafas da ‘yan bindiga ke kai wa hari.  Fadar Shugaban Kasa ta ce kalamai ne da ba su dace a ji su daga mutum irinsa ba.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawal,  ya ce da sauran Nijeriya,  a amfani da laturonik wajen sha’anin zaɓuɓɓuka a kasar nan.

Kwamitin Shugaban Kasa na yaki da kwaronabairos,  ya ayyana jihohi Legas,  da Ribas,  da Oyo,  da Kaduna,  da Kano,  da Filato da Babban Birnin Tarayya Abuja.  A matsayin jihohin da za a fi sanya wa ido,  a yanzun da guguwa ta uku ta kwaronabairios ta tashi.

Ministan aikin gona/noma,  Nanono,  ya ce tsadar da sufuri ya yi, da faduwa kasa warwas da Naira ta yi,  da fitar da kayayyakin abinci kasashen waje,  da ɓoye kayan abinci, da kuma damuna,  su suka sa abinci ya yi tsada.

Gwamnatin jihar Yobe za ta dawo da karɓar harajin dabbobi a hannun masu su,  don bunkasa kudaden shiga na jihar.  Ta ce tana sa ran karbar kudin harajin dabbobi guda miliyan 8 da rabi da ‘yan kai.

A yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna,  kidinafas na mutum da dabba,  sun kashe mutum guda,  suka yi kidinafin mutum bakwai,  da shanu guda a kalla 60.

A yankin karamar hukumar Rafi ta jihar Neja,  ‘yan bindiga sun kai hari,  ‘yan sintiri da jami’an tsaro suka yi nasarar dakile harin nasu,  sun kuma kashe ‘yan bindigan su a kalla goma,  su kuma suka kashe ‘yan sanda biyu.

A yankin Gusau da ke jihar Zamfara,  ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda goma sha uku, da wasu mutanen uku.

Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Usman Alkali Baba,  ya bai wa ‘yan sandansa umarnin su tabbatar da an yi Sallah hankali kwance.

TALATA

Talata,  goma ga watan Zulhaj,  shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta,  Annabi Muhammad S. A. W.  Daidai da ashirin ga watan Yuli,  shekarar 2021.

Yau take Babbar Sallah wato Idil Kabir.  Sallah ta layya.  Ana kame baki har sai an sauko Sallar Idi. Ana bukatar a ci ado in son samu ne fararen kaya,  hanyar sa aka bi in za a dawo a canza.  Ana tafiya ana karbari in son samu ne a taka sayyada zuwa masallaci da dawowa.  In an idar da Sallah za a jira liman ya yi huduba da yanka nasa ragon layyan,  sannan sauran jama’a da Allah Ya huwacewa abin layyan ya koma gida ya yanka nasa. Sai dai mu a nan jihar Kaduna,  da aka ce tana cikin jihohin da suka fi hadarin harbuwa da kwaronabairos nau’i ta uku,  gwamnatin jihar ta sa a takaita shagulgulan Sallah,  da kaucewa yin Sallar Idin a filin Idi guda daya,  don rage cunkoson jama’a.

Masarautar Zazzau ta fitar da sanarwar cewa a ba hawan Sallah da aka saba yi,  saboda matsalar tsaro da ta kwaronabairos.

A Kano ma gwamnatin jihar ta ce ba hawa da sauran shagulgulan Sallah da aka saba taruwa ana yi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa ‘yan Nijeriya saboda sadaukar da kan da suke ci gaba da yi,  da tabbacin gwamnati ta mike tsaye,  wajen tabbatar da ta kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar kasar nan.

Hukumomin sojan Nijeriya sun ce tabbas ‘yan bindinga sun hari wani jirgin yaki da ya dinga yakarsu tsakanin Kaduna da Zamfara,  sai dai matukin jirgin yakin Filayit Liyutenan Abayomi Dairo da dama shi kadai ne a cikin jirgin ya yi kundinbala da lema ta saukar ungulu ya fice daga jirgin.  Da ‘yan bindiga suka lura ya fice daga jirgin kafin jirgin ya fado kasa,  sai suka bazama nemansa.  Ya samu waje ya ɓoye ya kira agaji,  sojoji na sama da kasa suka kai masa dauki suka killace inda yake, suka hana ko kuda gittawa wajen,   da har zuwa wayewar garin Allah suka gano inda ya fake,  suka dauke shi (Ga masu iya ganin hoton da ke tare da wannan rubutu na yau,  shi ne a tsakiyar manyan hafsoshin soja suna masa barka).

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi a matsayin shugaban Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa NECO.

Kotu ta dakatar da wani yunkuri na tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara.

Sojojin sun kashe wasu ‘yan Boko Haram a jihar Barno,  sannan wasu dakarun kungiyar da matansu da ‘ya’yansu sun yi saranda sun mika kai ga sojoji.

Mata su fiye da 70 ‘yan bindiga suka sako su a jihar Zamfara.

Kotu ta nemi Nyako ya hallara a gabanta don kare kansa a kan wata Naira Biliyan 29.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS,  ta bukaci Nijeriya ta kara yawan harajin tamanin kaya BAT da take karɓa daga otel-otel da sauransu.

Nijeriya ta yi wa Amurka fintinkau  a matsayinta ta hudu da ke sayarwa da Indiya man fetur.

Wasu malaman makaranta da ma’aikatan kananan hukumomi na jihar Kaduna,  sun yi korafin albashin watan jiya,  da na watan shekaranjiya har yau shiru.

Ma’aikatan kwalejojin foliteknik na gwamnatin tarayya,  na shirin cika shekara uku suna dakon ariyas na sabon albashi

Daliban jami’ar jihar Kaduna da na sauran manyan makarantu da gwamnatin jiha ta kara wa kudin makaranta,  na nan suna ci gaba da addu’ar Allah Ya kawo musu mafita cikin hanzari.

LARABA

Laraba,  goma sha daya ga watan Zulhijja,  shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta,  Annabi Muhammad S. A. W.  Daidai da ashirin da daya ga watan Yuli,  shekarar 2021

Jiya al’umar musulmi da ke ko’ina a fadin duniya suka yi hawan Idi,  aka kuma sauko lafiya.  A Nijeriya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi tasa sallar idin a garinsu Daura tare da Sarkin Daura.  Ya yanka nasa ragunan layyyan guda biyu,  ya bukaci jama’a a dinga tona asirin miyagun mutane da ke tare da su,  don su suka fi kowa saninsu.  Buhari ya yi addu’ar zaman lafiya,  da jaddada tsayin dakan da ya yi na magance matsalar tsaro,  da bai wa manoma damar komawa gona hankali kwance,  ya kuma gana da ‘yan bautar kasa da aka tura Daura.

Sarkin Musulmi da ya yi tasa sallar a Sakkwato Birnin Shehu,  ya yi kira ga shugabannin su ji tsoron Allah.

Tsohon Shugaban Mulkin Soja Abdulsalam Abubakar,  da ya yi tasa sallar a Minna da ke jihar Neja,  ya bai wa kidinafas da ‘yan bindiga da sauransu,  shawarar su tuba su rungumi rayuwa mai tsafta,  domin wannan hanya da suke kai ba mai billewa ba ce.

A nan jihar Kaduna ma an yi Sallah a filayen idi daban-daban,  har da Dandalin Murtala Mohammed inda Sanusi Lamido Sanu Na Biyu ya limancin sallar.

Yau al’umar musulmi ke ci gaba da shagulgulan Sallah,  da rabon abinci,  da rabon naman layya,  da yawon Sallah,  da kure adaka.

Raguna na nan tunjun kuma birjik a kasuwannin dabbobi daban-daban musamman Zangon Shanu da ke Tudun Wadar Kaduna,  saboda babu masu saye sosai saboda tsada.

Jami’an tsaro sun damke shugaban aware na Yarbawa wato mai gwagwarmayar ɓallewa don kafa kasar Yarbawa daga Nijeriya Igboho,  a Cotonou/Kwatano da ke kasar Binin,  a tashar jiragen sama yana kokarin sulalewa zuwa Jamus. Yanzun haka kungiyoyin yarbawa sun mike tsaye,  wajen ganin sun hana a taso keyarwa zuwa gida Nijeriya don yi masa shari’a,  kamar yadda aka yi nasarar cafko Kanu mai gwagwarmayar kafa kasar Biyafara ta Inyamurai,  aka taso keyarsa zuwa gida Nijeriya.

Hukumar sanya ido ɓangaren lantarki NERC,  ta zaɓi kamfanoni 99 da za su sanya wa jama’a mita ta iya-kudinka-iya-shagalinka.

Wasu sabbin masu zuba jari sun saye kamfanin raba wutar lantarki DISCO na Yola.

Daliban jami’ar jihar Kaduna da na sauran manyan makarantu na gwamnatin jihar da aka kara wa kudin makaranta,  sun ce suna barar addu’ar Allah Ya kawo musu mafita.

Exit mobile version