Jam’iyyar PDP ta kara fadawa cikin wani sabon rikici bayan kwanciyar hankali da aka samu, a daidai lokacin da jam’iyyar take shirin gudanar da babban taronta na kasa a ranar 15 ga Nuwamba.
PDP ta kara fadawa rikicin cikin gida ne a daidai lokacin da shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Umar Damagum da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, suka samu rashin jituwa kan yadda aka gudanar da zabe a jihohi uku da suka hada da Kuros Ribas da Kebbi da Filato.
- Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin
- Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara
An dai shirya za a gudanar da zaben shugabannin PDP na jihohi a ranar Asabar, 27 ga Satumba. Sai dai kuma kasa da awanni 48 kafin fara babban taron, kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar karkashin jagorancin Damagum ya rubuta wa hukumar zabe ta kasa (INEC) sanarwar dage zaben, bisa abin da suka kira lamuran da ba a za ta ba.
A wani bangare na wasikar da Damagum ya aika wa INEC ya ce, “Kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyarmu yana dakatar da babban taron jihohi a Korus Ribas da Filato da Kebbi. Za a sanar wa hukumar zabe sabon ranar da za a gudanar da taron.”
A wani mataki da ke nuna rashin jituwa a cikin kwamitin gudanarwar, Sanata Anyanwu ya rubuta wasika ta mayarwa ga INEC, yana ba da shawarar ga shugaban INEC da ya yi watsi da dage zaben da shugaban jam’iyyar ya bukata.
Anyanwu a cikin wasikarsa ya bayyana cewa an kammala dukkan shirye-shirye wasu tsare-tsare don gudanar da taron, kuma za a gudana da shi kamar yadda aka tsara.
“Muna tabbatar wa hukumar zabe cewa za mu gudanar da taron kamar yadda aka tsara tun farko ba tare da dagawa ba.
“Ya kamata hukumar zabe ta yi watsi da wasikar da shugaban jam’iyyar ya tura mata tun da farko na dage toron,” ya aika wa INEC wasikar ne a ranar 26 ga Satumba ba tare da sa hannunna ba.
A cewar sakataren, bai kamata INEC ta yi aiki kan wata wasikar da ba sanya hannunsa hade da na Damagum ba.
Wata majiyar ta bayyana cewa abin da ke faruwa yanzu ya nuna yadda kowani bangare ke kokarin mallakan iko a jam’iyyar PDP.
A ranar Alhamis da ta gabata, sakataren yada labarai na jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya bayyana matakin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na dage tarukan jam’iyyar, musamman na jihohin Filato da Kuros Ribas zuwa sabbin ranaku, wadanda za a sanar da su a nan gaba kadan.
“Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya bukaci dukkan shugabanni da masu ruwa da tsaki da daukacin mambobin PDP da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da kafofin watsa labarai da hukumomin tsaro da jama’a gaba daya tana sanar da su dage lokacin zabe kuma su bi ka’idojinta da suka dace,” in ji Ologunagba.
Bincike ya nuna cewa kwamitin zabe na PDP da aka kafa don gudanar da taron a Jihar Kuros Ribas sun gudanar da zaben a ranar Asabar.
Kwamitin, wanda Honourable Jones Chukwudi Onyereri ya shugabanta, ya yi watsi da umarnin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na dage zaben.
Jam’iyyar ta yi zazzafar muhawara kan wannan lamari, wanda hakan ya kara ruruta wutar rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp