Idan ana maganar ‘yan kishin kasa, Dakta Soky Amechree na da ban ne shi, domin kuwa mutum ne da za a iya suffanta shi a matsayin wani ginshiki ko jakada na gari, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa harkokin kimiyya da fasaha da kuma masana’antu, tun kusan shekaru talatin da suka gabata a tsakanin Nijeriya, Kanada da sauran kasashe daban-daban a duniya.
- An Rufe Kasuwar Saye Da Sayarwar ‘Yan Wasan Kwallon Kafa Ta Bana A Turai
- Har Yanzu Dokar Ababen Hawa Na Aiki A Katsina —Gwamnatin Jihar
Mutum ne wanda ya samu shaida daga wurin akilan mutane masu ilmi, a matsayin shugaba na gari wanda ya samu kwarewa a fannin ayyuka daban-daban. Kazalika, Daktan ya fito ne daga Jihar Ribas ta yankin Neja Delta, wanda ya bayar da gudunmawa a bangaren da ya shafi kasa baki-daya tare da ci gaba a fannin masana’antu masu zaman kansu da gwamnati da kuma harkar koyarwa a manyan makarantu tun shekaru talatin baya da suka wuce.
Kadan daga cikin ci gaban da ya kawo sun hada da samar da kyakkyawar alaka tsakanin Nijeriya da Kanada, wanda hakan ya yi sanadiyyar samar da Hukumar Kula da Jakadancin Kanada a Abuja da Gwamnatin Alberta da kuma harkokin man fetir da gas a Kasar Kanada tun shekarar 1993.
An samu wannan nasara ce tare da taimakon wasu daga Kasar ta Kanada, Mista Earl Hickok, Shugaban Kamfanin ‘Energy Serbices Ltd of Calgary’, Alberta da kuma Kanada. Mista Earl Hickok da Dakta Soky Amachree suka jagoranci daukar wakilan Nijeriya sama da goma zuwa Kasar Kanada, a matsayin yawon bude ido a bangaren da ya shafi harkokin Ilmin Kimiyya da Fasaha, tun shekaru 20 kafin a samar da alakar kafa kamfanin harkokin man fetir da gas a Nijeriya.
Mista Earl Hickok, mutum ne jajirtacce wanda ya sha alwashin taimaka wa Nijeriya a wannan bangare. Ya kuma taimaka da aljihunsa, inda ya batar da sama daruruwan dubbannin dalar Amurka don ganin ya taimaka wa Nijeriya shekaru 20 da suka gabata. Hankalinsa ya kwanta tare da yarda wajen ganin an kulla harkar kasuwanci da Nijeriya tare da Dakta SOKY Amachree. Kazalika, yana da yakinin cewa Nijeriya kasa ce mai albarka, shi yasa ya dage wajen bayar da tasa gudunmawar don ganin ta ci gaba ta hanyar kimiyya da fasaha, musamman ma a bangaren da ya shafi harkokin man fetir da kuma gas.
Haka zalika, daya daga cikin nasarorin da aka samu na ziyarar da aka kai Kasar ta Kanada ya hada da, kafa Makarantun Gwamnatin Tarayya na man fetir guda biyu da kuma Makarantun Kimiyya da Fasaha a fannin Gas cikin Jihar Ribas (Bonny) da kuma Jihar Bayalsa (Ekowe), tare da hadin guiwar rukunin kamfanonin Kanada ‘Canadian Oil & Gas Polytechnic’ da kuma Kamfanin ‘Southern Alberta Institute of Technology (SAIT).’
Sannan, an sake samun hadin guiwa tsakanin Kamfanin DPR (Department of Petroleum Resources), ‘Alberta Energy and Utilities Board’ da kuma Jami’ar Calgary Energy da sauran makamantansu.
Har wa yau, akwai kuma hadin guiwa tsakanin manyan makarantun gaba da sakandire da suka hada da ‘Southern Alberta Institute of Technology’ da kuma Makarantun Kimiyya da Fasaha guda hudu daga Jihohin Nijeriya da ya hada da Jihar Bayelsa, Lafia a Jihar Neja, da kuma Jihar Gombe.
Haka nan, idan aka yi la’akari da irin gagarumar gudunmawar da Dakta Amachree ya bayar, musamman a yankunan Neja Delta a matsayinsa na Babban Manajan Daraktan Kamfanin ‘Sigma Technical Agencies Ltd’ a Fatakwal ta Jihar Ribas tare da taimakon Farfesa E. O. Okoro, Shugaban Tsangayar Koyon Karatun Likitanci a Jami’ar Ilorin, sun rubuta wa Ma’aikatar Neja Delta korafinsu tare da jan hankali, domin samar da hanyar warware rikicin da ke addabar su tare da samar kyakkyawar hanyar zaman lafiya a tsakaninsu.
A takardar da suka rubuta mai dauke da kwanan wata na 17 ga watan Yulin 2009, Amchree da Okoro sun ja hankalin mambobin al’ummar Neja Delta da kuma ‘yan kabilar Ijaw, wadanda aka ciro daga Jihar Ribas da Delta, kan cewa dukkanin banbance-banbance da rashin jituwar da ake samu, kai tsaye ya shafi matsalar tattalin arziki ne, wato rashin wadata.
Ya kara da cewa, “Babban abin da ke kawo rashin jituwar shi ne, rashin samun isasshen abin kashewa na yau da kullum, duk kuwa da cewa man fetir da gas daga wurinsu ake hakowa, amma sai a baiwa wasu bakin haure dama suna haka suna sayarwa wasu Kamfanoni na Kasashen Waje, cikin dan kankanin lokaci suna zama biloniyoyi, su kuma mazauna wajen wadanda ke ganin kasar tasu ce na ci gaba da zama cikin mummunan talauci da kuncin rayuwa.