Kara inganta koyon yadda za ka bunkasa aikin ka da kuma kwarewar ka: Sai ka maida hanakli kan ci gaba da koyon yadda za,ka kara inganta iliminka da irin kwaraewa da kake da a matsayinka na Malamin makaranta,ta haka su ma daliban naka za su inganta har ma,su taimaka wajen yadda kai mai aikin naka na koyarwa zai bunkasa tare da kai.
Sai ka rika halattar tarurruka,da horarwa ,domin ka kasance a sanin irin halin da ake ciki na lamarin daya shafi ilimi,kayayyakin da za’ ayi amfani dasu,da kuma yin bincike domin ka kasance cikin sanin irinhalin da ake ciki.Idan kana ci gaba koyo, a matsayin ka,na Malamin makaranta,ta hakan kai, ma kana kara inganta amfanin da dabarar yadda zaka koyar a kuma koya cikin aji.
- Kwararru Sun Yi Musayar Ra’ayoyi Dangane Da Wayewar Kan Sin Da Afirka
- Fursunoni 62 Sun Rubuta Jarrabawar NECO da MBAIS A Kano
Yin mu’amala da dalibai Iyaye, Malamai, sauarn masu ruwa da tsaki ta bangaren ilimi: Idan Malaman makaranta suna mu’amala da masu fada aji da yawa a harkar ilimi kamar dalibai,Iyaye,da kuma wasu Malaman makarantar.Akwai bukatarsu ci gaba da yin mu’amala ba tare da wata rufa- rufa cikin gaskiya da adalci,tareda dalibai,da kuma rika bayyanawa su Iyayen nasu dangane da irin halin da ‘ya’yan su suke ciki kan ci gaban da suka samu kan karantun abubuwan da ake koya masu.
Lura da ba da shawara ga dalibai (Sabbi)
Malamai su kasance wadanda ke misala da su ne,sune kuma ke taimakawa wajen yadda ya dace su tafiyar da rayuwarsu ta karatu da kuma har yadda ya kamata su kasance bangaren rayuwa ta halayya gaba.
Bada shawara kan abinda ko abubuwan da su daliban suke bukatar zama da babban burin ko wane daga cikinsu,da yadda za su cimma burin abinda suke son zama a gaba.
Bada taimakon lokacin da ake fuskantar matsalolin rayuwa da kuma karatu.
Yin kwatance da Malamin makarnta wajen koyi da abubuwan da aka ga yana yi,irin hakan na karawa dalibai kwarin gwiwa, wajen daukar mataki kan irin abinda ya dace su yi,na taimaka masu daukar mataki daukar mataki na irin burin da suke bukatar cimmawa akan ilimi.
Samar da hanyar tafiya tare da kowa
Samar da hanyar da kowane dalibi zai gane tafiyar tare da shi ake yin ta,wannan ma wani abu ne da yake nuna babu wani bambanci kan yadda ake koyar da su daliban.
Sanya wadansu abubuwan da za su ja hankali cikin dabarun koyar da darussa.
Tabbatar da cewa kowane dalibi ya gane an dauke shi muhimmanci,ba tareda yin la’akari da yadda yake ba.
A yi maganin duk wata matsalar da ta taso hakan yana bada dama ganin darajar kowa da fahimtar juna.
Tafiya tare da kowae dalibi a aji hakan na taimaka masu wajen yadda za su fuskanci yin mu’amala da mutane daban- daban na sassan duniya.
Yin mu’amala kamar yadda ya dace tsaanin dalibai da Malamin makaranta hakan na tabbatar da cewa kowa ya san irin halin da ake ciki,da kuma irin taimako mai gamsarwa da dadadawar za a ba dalibi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp