Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci ta bayyana cewa, ta karbo bashin biliyan 12 na takardar Yen na Kasar Japan, wanda ya yi daidai da dala biliyan 12.
Ministan Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci, Abubakar Kyari ne ya bayyana haka.
- Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya
- NIMASA Za Ta Adana Wa Nijeriya Dala Biliyan 400 A Shekara Daga Cazar Kudaden Safarar Kaya
Ya ce, Ma’aikatarsa ta karbo bashin ne daga hukumar bayar da agajin gaggauwa ta kasa da kasa (JICA) da ke Kasar Japan.
Kazalika, ma’aikatar ta kuma yabawa hukumar kan goyon bayan da take bai wa Nijeriya.
Ya sanar da cewa, Nijeriya za ta yi amfani da bashin ne, wajen kara habakawa da kuma ciyar da shirin bunkasa aikin noma na kasar nan, wato NAGS-AP.
Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadaccen Abinci, Sanata Abubakar Kayri ne ya bayyana a haka, a cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar.
“Mun samar da tsarin samar da wadataccen abinci a kasar nan, wanda kowanne dan kasar zai amfana da shi”, in ji Kyari.
Daga cikin manyan abubuwan da suka hada da bashin sun hada da; samar da ingantaccen Irin Shinkafa da kuma habaka yadda ake samar da Irin na Shinkafar.
Sauran sun hada da mayar da hankali wajen yin girbin mai kyau, samar da nau’ikan Shinkafar da ke jurewa kowacce irin cutar da ke lalata Irin Shinkafar da aka shuka, aka ajiye a cibiyar gudanar da bincike kan amfanin gona (NCRI) da ke yankin Badeggi a Jihar Neja.
Kazalika, akwai kuma bukatar kara bunkasa kayan aikin gona, inganata aikin malaman gona, amfani da kayan aikin gona na kimiyya domin rika samar da bayanai a kan lokaci, musamman wanda ya shafi sauyin yanayi, samar da farashin kayan amfanin gona a kasuwa, dakile barkewar kwarin da ke lalata amfanin gona da sauransu.
A nasa jawabin, Karamin Minista a Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci, Dakta Abdullahi Sabi Abdullahi, ya bayyana gamsuwar da cewa, shuka ingantaccen Irin noma zai taimaka wajen ciyar da daukacin ‘yan Nijeriya gaba.
Dakta Abudullahi ya kara da cewa, ingantancen Iri shi ne, kashin bayan da zai kawo karshen kalubalen da bangeren samar da wadataccen abinci a kasar.
“Wannan hadaka za ta kara karfafawa, musamman kananan manoma na kasar nan guiwa, ta hanyar yin amfani da aikin karfafa wa kanannan manoma gwiwa, wato SHEP, wanda a yanzu aikin ya karade jihohi 14 na kasar nan”, a cewar Abdullahi.
Kazalika, wannan hadakar ta kasance tamkar cike wani gibi ne a tsakanin gudanar da bincike, yin aiki a aikace tare kuma da samar wa manoman kasar nan kayan aikin gona na zamani da kuma samar musu da ilimin kwarewar da ya kamata a fannin na aikin noma.
Shi kuwa, Darakta Janar na Hukumar, wanda kuma shi ne har ila yau, ya jagoranci tawagar kasar ta Japan, Takao Shimokawa ya bayyana cewa, Hukumar ta JICA da kuma Kasar Japan, sun mayar da hankali wajen ganin an bunkasa bangaren noman Shinkafa a Afirka, musamman ma a Nijeriya, duba da cewa, kasar ta kasance kan gaba wajen noman Shinkafa.
Wannan shirin ya nuna a zahiri irin mayar da hankalin da gwamnatin tarayya da Hukumar JICA suka yi, don kara habaka bangaren samar da wadataccen abinci a kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp