Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Garki da Babura a Jihar Jigawa, Musa Muhammad, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Hakan na kunshe ne cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar APC na yankin Kore a karamar hukumar Garki mai dauke da sa hannunsa.
- Canjin Kudi: Kotun Koli Za Ta Ci Gaba Da Sauraren Karar Da Gwamnoni Suka Shigar
- Sabon Kwanturolan NIS A Ribas Ya Gargadi Jami’ansa Kan Bin Dokokin Aiki A Zaben 2023
A cewar wasikar da jaridar Leadership Hausa ta samu, dan majalisar ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar ne saboda wasu rigingimu da abubuwan da suka faru.
“Na rubuta ne domin sanar da jam’iyyar cewa na yi murabus daga jam’iyyar APC daga ranar 21 ga watan Fabrairun 2023.
“Wannan ya samo asali ne sakamakon rigingimu da abubuwan da ke faruwa a dukkan matakai na jam’iyyar, don haka ina mika godiya ta ga jam’iyyar da ta ba ni damar tsayawa takara a cikinta,” in ji shi.
Musa, ya ce ya hada kai da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Mustapha Sule Lamido, domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ne, ya nada shi a madadin mahaifinsa marigayi Muhammad Adamu Fagen-Gawo wanda ya rasu a birnin Dubai bayan gajeruwar rashin lafiya.
Ya lashe zaben ne da kuri’u 48,318, inda ya doke dan takarar jam’iyyar PDP, Nasir Garba Dantiye wanda ya samu kuri’u 24,135.