An tabbatar da mutuwar wani dan majalisar wakilai ta tarayya.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Isa-Sabon Birni a karkashin jam’iyyar APC, Abdulkadir Jelani Danbuga, ya rasu ranar Laraba.
- Jamaica Na Neman Greenwood Ya Koma Wakiltarta A Kwallon Kasa
- Muna Fatan Dawowa Kan Ganiyarmu – Eric Ten Hag
Dan majalisar mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta kudu a majalisar dokokin jihar Sakkwato, Aminu Almustapha (Boza) ya tabbatar da rasuwar.
A cewar Boza, dan majalisar tarayyar ya rasu ne da misalin karfe 12:30 na safiyar ranar Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya.
An ce an kwantar da shi a wani asibiti da yammacin ranar Talata.
“Za a kai gawarsa zuwa Masallacin kasa domin yi masa wanka, daga nan kuma za a kai gawarsa Sakkwato domin yi masa jana’iza da misalin karfe 11 na safe,” in ji Almustapha.
Danbuga ya bar mata biyu, ‘ya’ya da jikoki da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp