Yanzu haka ana shirin aike wani yaro dan shekara 10 gidan gyaran hali a Amurka kan zargin harbe mahaifiyarsa har lahira da bindiga kan kin saya masa abun sauraren kida.
Yaron yanzu da ke hannun ‘yansanda ya hallaka mahaifiyar tasa ne bayan da ta ki saya masa ‘headset’ a kamfanin sayar da kayayyaki na Amazon.
- Manoman Alkama Sun Koka A Kan Rashin Samun IriÂ
- 2023: Daga Karshe Dai Tawagar Su Dogara Sun Mara Wa Atiku Baya
An ruwaito cewar yaron ya harbe mahaifiyarsa da bindiga sannan ya yi amfani da asusunta wajen sayen abun sauraren kidan kwana daya da mutuwarta.
Dan yaron mai shekara 26 a duniya ne ya kai karar faruwar lamarin ga ‘yansanda wanda tuni suka damke shi, sannan ana shirin aike ahi gidan gyaran hali na yara da ke birnin New York.