Allah mai girma da daukaka (a farkon suratul Fat’hi) ya fara ne da sanar da Annabi (SAW) abin da ya hukunta a gare shi na daga hukunci mabayyani cewa Allah ya dora shi a kan makiyansa. Allah ya bayyana addinin Annabi (SAW) ya cika ko ina, yau ina su Abu Jahli? Allah ya rinjayar da Annabi a kan makiyansa da daukakar kalmar Manzon Allah (SAW) da Shari’arsa. Duk wadannan sun tatttaru ne a cikin fadin Allah (farkon surar) cewa shi Annabi (SAW) abin gafartawa ne a gare shi (duk abin da ya aikata na barin tarku aula), ba wanda za a rika ne da wani laifi ba, ba wani abu da zai yi nan gaba kuma a ce an rike shi da laifi.
Wani sashe na malamai ya ce, wannan yana nufin an gafarta masa ne (SAW) idan da ma akwai wani abu da ya kasance (na laifi) da abin da ma bai kasance ba da zai zo nan gaba, Allah ya gafarta masa. Sai mu lura a nan, duk da Allah ya ba Manzon Allah (SAW) garanti cewa an yafe masa (abin da ya yi a baya da wanda zai yi a gaba) amma Manzon Allah bai aikata wani abin assha ba. Shi ma Manzon Allah haka ya din ga yi wa wasu Sahabbansa garanti, yana fadin wane dan aljanna ne, wane da aljanna ne. Kuma su ma ba a ga suna aikata wani abin assha ba. Manzon Allah (SAW) ya ce duk ‘Yan Badar (wadanda suka halarci yakin Badar) Allah ya gafarta musu, duk abin da suka aikata ba za su shiga wuta ba, to kuma ba a ga wani Dan Badar ya yi shirka da Allah ko ya aikata wani laifi da za a iya cewa na assha ba ne.
- Gwamna Dauda Ya Ƙaddamar Da Rabon Tirelolin Taki 135 A Zamfara
- Girman Manzon Allah (SAW): Darasi Daga Suratul Fat’hi (I)
Malamai sun ci gaba da bayanin cewa abin da ayar (ta farkon surar) take nufi, shi ne (ya Rasulallahi SAW) kai abin gafartawa ne. Malam Makki ya ce Allah ya sanya baiwa sababi ce ta gafara, duka da baiwar da gafarar daga Allah ne wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi. Bayan baiwa, darajantawa ne Allah ya ba Annabinsa.
Sannan Allah ya ce zai cika ni’imarsa ga Annabi (SAW). Malamai suka ce meye cikar ni’ima ga Annabi (SAW) da Allah yake nufi? Suka ce ita ce kaskanta makiyansa (komai karfinsu na kudi da mulki) su dawo a karkashinsa. Kila kuma malamai suka ce cikar ni’imar tana nufin Allah zai bude masa Makka (Fatahu Makkata), ya so shiga sun hana shi sun ce sai dai ya dawo badi, to bari wata rana garin zai zama nasa, wand ya ga dama zai bar shi ya zauna a garin; wanda bai ga dama ba kuma ya kore shi kuma ya koru (SAW). Tana kuma nufin Allah zai bude wa Manzon Allah (SAW) Da’ifa. Kila kuma ma’anar cika ni’ima ga Manzon Allah (SAW) tana nufin Allah zai daga ambatonsa a nan duniya. Ba yanda za a yi ambaton Manzon Allah ya gushe, ba wanda yau a duniya zai ce bai san ambatonsa ba. Ga shi nan duk kiran sallah biyar sai an fadi sunansa kuma da karfi cikin daga murya, bayan sauran wuraren da ake ambatonsa kamar su tahiya da sauransu. In dai za a ambaci Ubangiji to sai an hada da Bawansa (Annabi SAW).
Allah zai taimake ka, Allah zai gafarta maka (ya Rasulallah SAW). Sai Allah ya sanar da shi (SAW) cikar ni’imarsa a gare shi ta hanyar kaskantar masa da girman makiyinsa, da bude masa mafi soyuwar garuruwa a gare shi (Makka), duk Allah ya bude masa. Haka nan Allah ya nuna masa zai bude masa Hira da Sham da Mada’in da Rum duk gabadaya ya fada wa Sahabbansa. Allah zai daukaka ambatonsa da shiryar da shi tafarki madaidaic, tafarkin da zai kai (mutum) zuwa Aljanna da arzikin lahira da taimakonsa, taimakon da ya zama mabuwayi da baiwar Allah ga al’ummarsa. Bayan ni’imar a kan Annabi (SAW), Allah Ta’ala ya kuma faranta wa Annabi rai a cikin al’ummarsa Muminai wanda ya natsar da zuciyarsu da natsuwa wanda Allah ya sanya a cikin zukatansu. Duk Mumini sai ka ga zuciyarsa a natse, za ka ga yana yin ayyukansa cikin hankali da natsuwa, amma duk wanda ba haka ba, sai ka gan shi a cikin tashin hankali, ko karatu zai yi sai ka ji yana yi a cikin tashin hankali kai ka ce sakon da yake isarwa da fada aka aiko, misalin irin wannan kamar kare ne, in ka bige shi ko ka bi shi da gudu zai yi haki; haka nan idan ka kyale shi yana hutawa duk dai za ka ga yana haki, Allah ya kiyaye mu. Mutum ya zamo yana cikin natsuwa.
Allah ya kuma yi wa (Muminan) bushara da abin da yake gare su a wurin Ubangiji. Duk Musulmi in dai ya yi imani (La’ila ha illallahu Muhammadur Rasulullah SAW), sauran abubuwa suna da sauki, zai samu Rahamar Allah. Komai laifin da Musulmi zai yi idan ya mutu ba za a ce yana wuta ba, sai dai a ce ya tafi Mashi’ar Allah, idan Allah ya ga dama ya azabtar da shi, idan kuma ya ga dama ya sa shi a rahama. Allah yana cewa mece ce ribar da zai ci idan ya yi muku azaba in dai kuka yi imani kuka yi godiya? Mutum ya yi imani da Allah iya kokarinsa, Allah Ta’ala zai gafarta masa, ya yarda da Allah; ya san Allah alheri ne ya yi nufi da shi, ya sa dadi a zuciyarsa; ba ya dinga yi wa Allah mummunan zato ba. Ai ka ga ma a karatunmu na baya, Allah ya ce yana mana bushara muna da wata ajiya a wurinsa, ajiyar shi ne Annabi Muhammadu (SAW). Kowane Musulmi ya yi bishara, ya san bayan imaninsa na Musulunci, bayan ibadarsa, yana da wata ajiya a Bankin Allah, shi ne Annabi Muhammadu (SAW), idan ka zama kana da Annabi (SAW) a lahira wannan babban alheri ne; ya ishe ka.
Allah ya ce wa Annabi (SAW) gaya musu, ku yi farin ciki da falalar Allah da rahamarsa (fiye da aikinmu, kar mutum ya ga aikinsa ne zai ba shi abu a wurin Allah, ba kuma wai kar mu ki yin aikin ba, a’a, mu yi aiki tukuru, amma mu san mun dogara ne da falalar Allah da rahamarsa domin duk abin da muka yi na ibada idan babu falalar Allah da rahamarsa banza ne.
Wani mutum ya zo wurin Shehu Tijjani Abul Abbasi (RTA) ya ce, “Shehu Allah ya jarrabe ni da wani laifi; na yi-na yi in bari na kasa, yi mun addu’a Allah ya raba ni da shi”. Shehu Tijjani ya ce masa “je ka Allah ya karbe ka a bisa kowane hali”, sai mutumin ya ce “a’a ni dai ka yi mun addu’a in bari”. Shehu Tijjani ya ce masa “to wai kai a zatonka in ka bari (aikata laifi)din, idan ba zai karbe ka; karbar ka zai yi? Ka je Allah ya karbe ka kawai”. Kila Allah ya haska wa Waliy (Shehu) ya ga mutumin nan ba zai iya barin aikata laifin ba, to ka ga gara ya roka masa Allah a cikin falalarsa ya yafe masa, Allah ya shigar da shi Aljanna. Mu dogara da falalar Allah, mu yi ta aiki, amma mu san falalar Allah da rahamarsa su ne babban abin da muke dogara da shi, wannan kuma shi ne Annabi (SAW).
Allah duk ya yi mana busharori na abin da muke da shi a wajensa. Da samun babban rabon al’ummarsa (SAW) mai girma, da yi mana rangwame, ba wai ba mu da laifi ba ne, a’a, muna da laifi zunkur, waye zai ce ba shi da laifi in dai ba Annabi ba? Waye wannan da bai taba laifi ba in ba Manzon Allah (SAW) da wanda Allah ya kiyaye ba? Amma da laifin da komai sai Allah ya gafarta ma, ka san kana da laifin kuma ka kankan da kai da kwadayin Rahamar Allah. Allah ya ce yana nan a wurin mutanen da zuciyarsu ta karye, sun san sun saba masa, amma zuciyarsu sai ta karye domin sun san suna da Ubangiji. Babban laifi dai shi ne Allah ya jarrabi mutum da kekashewar zuciya ya rika ganin laifin ma banza ne, amma wanda zai aikata laifi ya ji zuciyarsa tana kuka, to wannan Allah zai gafarta masa gabakidaya. Amma duk wanda zuciyarsa za ta kekashe ya ga laifin da ya yi ma ba laifi ba ne, to wannan ya shiga hadari.
Allah mai sitarta zunubin al’ummar Annabi (SAW) ne da halakar da makiyan Manzon Allah a duniya da lahira da la’antarsu da nesantar da su daga Rahamarsa. Duk wannan falala ce da Allah ya yi wa Annabi (SAW). Duk wanda yake kin Annabi zai gamu da mummunar makoma.
Bayan duk wannan, sannan Allah ya ce “Hakika mu muka aiko ka mai shaidawa (ga al’ummarka), mai bushara gare ta, mai gargadi gare ta… (har zuwa karshen ayar”. Allah ya kirga kyawawan abubuwa ga Annabi (SAW) da kebance-kebacen da ya yi masa na cewa Annabi zai yi shaida ga al’ummarsa da kuma kansa; da cewa ya isar musu (al’ummarsa) da aike. Kila kuwa aka ce mai shaidawa ne gare su da Tauhidi, Annabi zai yi shaida ga al’ummarsa da suka ce La ila ha illallahu Muhammadur Rasulullah (SAW) a matsayin Musulmi ne. Annabi mai bushara ne ga al’ummarsa da samun ladan Ubangiji, kila aka ce Manzon Allah mai bushara ne ga al’ummarsa da gafara. Mai gargadi ne kuma ga makiyansa da azaba, kila kuma aka ce mai gargadi ne a kan kar al’ummarsa ta bace. Wanda kyakkyawa ta rigaya da shi daga Allah sai ya yi imani da Allah tun da Manzon Allah ya yi masa gargadi. Sai kuma ya yi imani da Manzon Allah (SAW).