Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya tabbatar da cewa dan wasan tsakiyar kulob din Kevin De Bruyne, zai yi jinyar makonni saboda raunin da ya samu a wasan da suka doke Burnley da ci 0-3 ranar Juma’a.
An tilastawa dan wasan na Belgium ficewa daga fili bayan mintuna 24 kacal a wasan farko na gasar Premier a gidan Burnley.
- Kane Ya Kammala Komawa Bayern Munich Bayan Shekaru 20 A Spurs
- Barcelona Ta Doke AC Milan A Wasan Sada Zumunta
Guardiola ya bayyana cewa tauraron dan wasan ya sake samun raunin da ya samu a karawar da suka yi da Inter a wasan karshe na gasar zakarun Turai a watan Yuni.
Babu tabbas tsawon lokacin da dan wasan na Belgium zai yi jinya a wannan karon.
Amma idan aka yi la’akari da yadda ya kwashe mintuna 24 kacal, Guardiola ba zai sake yi wa dan wasan mai shekaru 32 gaggawar dawowa karo na biyu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp