Shugaban kungiyar direbobin tasi na ‘Tsaya Da Kafarka’ ta jihar Kano, Sani Hasan Jinjiri ya yaba wa gwamnatin Kano bisa kulawa da ta ba su, musamman na tallafin da ta yi wa ‘yan kungiyar don rage masu radadin matsi na cutar Kurona, wanda hakan ke nuna irin damuwa da aka yi da su.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da ‘yan jarida a taron kaddamar da tallafin gwamnatin tarayya ga kungoyoyin direbobi da makanikai da masu faci, wanda da aka yi a dakin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Ya ce a baya suna da mambobi sun doshi 6000, sai dai a yanzu da zamani ya sauya an sami yawan ‘Adaidaita sahu,’ amma ba motocinne suka bari ba,wasu sun koma suna fitowane suna aikinsu.
Sani Jinjiro ya ce, kalubalen da suke fuskanta shi ne na rashin aiki, duba da halin da aka shiga na rayuwa da ba kowane zai tsare tasi ya ce zai hau ya tafi india yake bukata ba, amma cikin ikon Allah ana aikin duk da dai ba dadi.