Connect with us

RAHOTANNI

Dole Ne Mu Bi Umarnin Gwamnati Na yaki da Korona – Judo

Published

on

Alhaji Sule Musa Judo, shugaban kungiyar kasuwar sayar da kayan miya da nama da sauran kwalam da makulashe ta Kano, wato kasuwar Tarauni, ya ce, “ya zama dole gare mu da ma duk wani dan Kano mai kishin al`umma da kasarsa da jiharsa ya bi umarnin Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da umarnin masana da likitoci a kan yakar Korona a wannan lokaci.”

Alhaji Sule Musa Jido ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a kasuwar Tarauni da ke karamar hukumar Tarauni cikin birnin Kanon Dabo a ranar Larabar da ta gabata.
Har ila yau, ya bayyana cewa, “kasuwarmu kasuwa ce ta abinci da kowa da kowa ya ke amfani da shi a kowace rana, domin kasuwar Tarauni ita ce kan gaba wajen sayar da kayan miya lafiyayye da nama da kaji masu rai da yankakku kuma ga mu kusa da gidan gwamnati. To, idan ba mu bi dokokin tsafta da yaki da Korona, waye zai bi? Don haka mu na bin umarnin hukumomin gwamnati da na lafiya sau da kafa.”
Haka kuma ya ce, “wannan ce ma ta sa hukumomi irin su Ma’aikatar Muhalli ta Kano da sauran hukumomi su ka lura da tsaftarmu ta yau da kullum su ka karfafa ma na gwiwa ta hanyar nuna gamasuwarsu da kuma ba mu kyaututtukan lambar yabo ga wannan kasuwa Tarauni da ke birnin Kano.”
A karshe Alhaji Judo ya ce, a shekaru shida da ya yi ya na jan ragamar wannan kasuwa shi da mataimakansa sun samu gagarumar nasarar gyara kasuwar ta hanyar fitar da layi-layi da tsaftace layukan ta hanyar gina hanyoyin ruwa da yin malale siminti, sabanin da can a baya da kasuwar ta ke zaune kara-zube.
Ya ce, su na amfani da wannan dama wajen nuna gamsuwa da gwamnati karkashin jagoran ta Dr. Ganduje, wanda ya cika Kano da ayyukan alheri cikin shekaru biyu rak.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: